Chapter 25
Chapter 25
ni idan kin gama abinda na gada miki." Da haka ta katse wayar tana mai taya kawar tata jin ɗacin dake faruwa a rayuwarta, da ace tana da ikon juya zuciyar Saratu yadda taga dama, tayi rantsuwa a ciki wata daya kacal zata gyara mata komai, ta samar mata fiye da ƴancin da take dashi a wajen mijin nata tun kafin sake aurensa. Amma zuciya ce kowa da irin tasa duk yadda ka kai ga iyawa, wani a baki kawai zaka bashi labarin dukkan nasararka amma tasa zuciyarsa ba zata taba iya ɗauka ba. Ƙawayenta biyu kenan a duniya Saratu da Salamatu, kuma bayan abotar tasu, tana zana su ne a cikin wasu mutane da suka taka muhimmiyar rawa a rayuwarta, suka yi mata amfanin da zata rantse ko uwar data kawo ta duniya bata yi mata ba a wajenta, don haka su biyun ne kawai duk duniya kawai take iya buɗewa cikinta su ga ainihin kalolin da take ɗauke dashi bayan farar fatar ta. Matsalar guda ɗaya ce a wajen kowannensu, zuciyar Saratu bata iya jajircewa abubuwa har tayi yaƙi da iyawarta kamar yadda ita kanta ta furta a yanzu, Salamatu kuma sun sha banban da abinda kowannensu ke wa kallon nasara, don ita yanzu ko aure bata dashi, tafi ganewa yawon kasuwanci ga manyan mutanen da zasu dinga bata kuɗin da suka fi ƙarfin kayan nata. Ta ja tsaki a hankali tana nufar ƙofar wardrobe ɗin ta, yau ita ke da turakar Baffa, ta gama shiryawa tuntuni wayar Saratun ce ma ta tsaida ita, a cikin wardrobe din ta dauko wata baƙar ledar magani da kuma muƙullin ɓangaren sannan ta nufi ƙofar ɗakin ta buɗe, ta buɗe ta sanda hayaniya ta cika kunnenta, hayaniyar da a yanzu kullum cikinta suke saboda ƙaratowar bikin. Mutane ne kawai ke zuwa musu Allah sanya alkhairi tun yanzu, musamman daga ɓangaren ƴanuwan su Baffan na can ƙauye, masu kwana ma babu adadinsu don wasu tun wancan satin suka taho ma da zugarsu wai sun zo taya aiki, aikin da kullum sai anyi musu bayanin babu shi. Don daga harkar jere har harkar abincin da za'aci lokacin bikin da duk wata hidima, kuɗi suka biya a dunƙule wa mutane daban-daban da zasu ɗauki nauyin hakan. Kamfanika biyu na interior decoration suka biya don su yi jeran gidajen amaren, kawai ƴanuwanta dana Hajiya Maimuna ne ke zuwa su sa ido akan aikin don a hada har da tunanin mata komai ya tafi daidai, don haka su ɗin da suka zo, ba abinda suke ma illa ƙara aikin, don in banda ci su da ƴaƴansu ba abinda suke yini suna yi, dadinta ɗaya kawai basu barwa ma'aikatan gidan komai ba dasu ake girkin da duk wani aikin da ya taso, shi yasa ba wanda ya kai Inna Danejo murna a gidan yanzu ganin duk inda ta juya kawai ƴanuwanta take gani. Surayya ta fara gani a falon tana danne-danne a wayarta kafin dandazon matan da ke ta fitar da kaya daga kitchen suna yin waje. Ta wuce Surayyan da bata ko dago ba zuwa tsakiyar falon inda suka fara ganinta. "Hajiya sannu da fitowa." Wajen mutum biyar dake rike da wasu manyan fanteku tun na aurenta suka fada. "Yawwa, waɗannan kayan fa? Ina za'a kai su?" "Sameera ce tace a fita dasu waje Hajiya, na aikin cincin ɗin da za'a fara ne." "Cincin kuma? Ina ita Samiran take?" Tana tambayar kuwa ta fito ita da wata sa'arta mai suna Khadija da take ƴar ƙanwar Hajiya Kilishin, suka fito suna jan ragowar wani buhun sukari da ya kusan kai kwata. "Cincin ɗin me ake yi shirin yi a gidan nan Samirah?" Ta tambaya tana katse dariyar da suke yi ta kasa ɗaukar buhun. "Mama yara ne ke jin yunwa kafin a sauke abinci musamman da safe, shine nace bari ayi cincin sai ya dinga rage musu hanya." Girgiza kanta kawai tayi tana kallonta, kowa da irin ƙaddararsa a rayuwa, ita tata ta abinci ce, don duk da science take yi a makaranta, amma course ɗin da take son yi a University shima ɓangaren girki ne, (Nutrition and dietetics.) "Allah ya baku sa'a, kafin ku fara ki kawowa Baffa abincinsa yanzu, can zan je." Ta faɗa sanda ta juya, a cikin zuciyarta tana lissafin layin da zata saka Samiran daya danganci ra'ayinta nan da shekara guda idan ƙwarya ta fashe! Sahla ta fito daga ɗakinta a lokacin riƙe da labtop ɗin Munaya tana sake gyara gilasan idonta. "Mami dan Allah ki bani 1000 muyi subscription, datar da muke streaming ta ƙare kuma Aunty Munaya tace mu kai mata labtop ɗin wallahi ba zata sake siya mana ba." "Kije ɗaki, na ajiye wasu canji akan mirror ku ɗauka." Ta san ita da Zahra ne don kullum suna manne da juna, shi yasa bata san me zai faru dasu ba nan da shekara ɗayan nan. Ta fita daga ɓangaren zuwa harabar gidan kamar wata sarauniya, don duk ɗaukacin mutane kowa tsugunnawa yake yana mata sannu da fitowa yayin take binsu da murmushin da zuciyarta ta wanke shi tsaf, ta tace shi kafin fitowarsa. Kuma ɓangaren Inna Danejo ta fara biyawa ta kai mata maganin cikin ledar nan, na ciwon ƙafa ne wanda Innan tace tana jin daɗinsa saboda haka take sawa ana kawo mata duk wata. Kuma bayan sun yi ƴar hira da sauran tsofaffin dake wajen da kuma tarin albarkar da Innar ke sanya mata, ta fito zuwa ɓangaren Baffa, kafin ta shiga ta hango Munaya daga gefen ɓangaren tana waya, sai gyara glasses ɗinta take alamun tana sauraren wani abu, kuma fuskarta kaɗai ta kalla ta san a rikice take tunda dama ita ko doguwar magana akayi yanzu zata rikice tace bata gane ba, duk kuwa irin mahaukacin ƙoƙarin da take dashi a ɓangaren karatu, don tun suna yara Jamal ke cewa Ma'aruf da Munaya sune Geniuses (masu kokarin) ɗin gidan. Zuciyarta ta cunkushe a lokaci guda da ambatar sunan, shekaru goma kenan da shafewarsa a doron ƙasa, amma har yanzu yaƙi barin zukata su huta, don ƙaryane a gidan nan ance an shafe sati guda na kowanne wata ba'a samu wani ya ambace shi ba, hatta ita kuwa tunaninsa na yawan wulga mata a zuciya, ta tabbata da ace Jamal na raye har yanzu to da itace a bayan ƙasa, don ta daɗe da lissafa cewa shi da ita mutane ne da baza su taba rayuwa a lokaci guda cikin duniyar nan ba. Ta zira muƙullin hannunta ta buɗe bangaren ta shiga. Komai yana nan kamar yadda ta sanshi, don dama ɓangaren a suna yake na Baffan amma ita ke da iko da komai na cikinsa, me ta gayawa Saratu ne ɗazu? Babu abinda ƙwaƙwalwar mace baza ta iya ba idan har ta saka kanta, ta tuno shekarun da ranta ke ɓaci idan ta ɗaga labulen ɗakinta ta hango kyakkyawar surar Hajiya Maimuna na shiga ɓangaren Baffan, idan taci kwalliyar nan tata za'a shafe tsawon dare ana musu da wani cewa bata ajiye kamar Ma'aruf balle ma wanda yafi shi a duniya ba, kuma da tayi tunanin cewa bata don ganinta a wajen lokaci yayi da zata bar mata bangaren ita kaɗai, me ya faru yanzu? Tayi wani guntun murmushi lokacin da take kunna turaren wuta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73