Skip to content

Chapter 52

Chapter 52

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

wannan tunanin ta kammala haɗa abincin breakfast ɗin lokacin da ta tsinci bugun ƙofar nan. Kayan jikinta riga da skirt ne na wata atamfa ash da tun ganinta da ita da farko tayi mata kyau wa ido, kuma sai akayi sa'a mai dinkin ya zabi wani ɗinki mai kyau da ya dace da ita don haka suka karbeta sosai, kuma yau bata saka mayafin data saba ba sai ta yiwa ɗankwalin V kawai ta yafa shi a haka. Ta buɗe ƙofar lokacin da hoton wata budurwa ya shiga idonta, doguwa ce, fara, kamaninta na yare ne amma kuma kyakkyawa ce, ta bazo gashin data ɗora a saman kanta mai kyau sannan matsatstsiyar rigar data saka ma mai kyau ce, don ta fito da kowanne lungu da saƙo na jikinta yayin da hannunta ke rike da wata ƙatuwar jaka irin ta aiki. "Good Morning my name is Martha, I'm..." ( Barka da safiya, sunana Martha, nice...) "She's my sectary." (Sakatariyata ce.) A lokaci guda muryar Ma'aruf ta faɗa daga bayanta, kuma ba tare da jiran komai ba taji hanayensa masu dumi dun sauka a bayanta, daidai wajen da zip din rigarta ya fara, sannan ƙamshin turarensa ya cika hancinta. Bata san lokacin da ta juyo da kanta ta kalle shi ba, idanunta na nuna mamakin da dukkan wani abu mai hankali a jikinta ke yi na yadda ya tsaya kusa da ita amma shi ba ita yake kallo ba, wadda ta kira kanta da Martha din yake kallo da wani dan guntun murmushi a leɓɓensa. Kuma bata sake shiryawa ba sanda taji ya jawo ta baya kaɗan yana haɗa ta da jikinsa, kanta ya tsaya daidai kafaɗunsa. "You're welcome Martha, meet my wife Amina Sulaiman." Sai da numfashin Amina ya katse a ƙirjinta jin yadda ya ambaci cikakken sunanta amma hakan baiyi nisa ba saboda Martha da ta miƙo mata hannu tana jiran su gaisa, sai tayi saurin mika mata nata itama tana murmushin da bata san a yaya ya fito ba. "You came with everything right?" (Kinzo da komai ko?) Taji muryarsa daga saman kanta tana sake tambayar Martha ɗin wadda ta ɗaga kai. "Yes sir, everything is intact, I just need to explain some things to you about Document A." (Eh yallaɓai, komai ya cika bayanin wasu abubuwan kawai zan yi maka.) Har yanzu da murmushi a fuskarta ta amsa, kuma sai kawai yasa hannunsa ya sake matso da Amina gefensa, suka bawa Marthan hanyar shiga ciki, ta wuce su kuwa tana ƙoƙarin fito da takardu da kuma labtop daga jakar hannunta. "Kin tashi lafiya?" Muryarsa ta tambaye ta tun kafin ta dawo da hankalinta kansa, sai tayi baya da ƙafafunta da sauri wanda hakan yasa ya saki hannun nata, kuma maimakon ta amsa sai tace. "Barka da safiya." Ya shafo gashinsa ta baya. "Barkanmu dai, hope kin dawo daidai?" Ta san me yake nufi don haka ta ɗaga kanta sau biyu idanunta akan yatsunta, ya cigaba da cewa. "Wannan sakatariyata ce sunanta Martha zamu yi meeting anjima ne and I left my things a office shine tazo ta kawo min." Bata san me yasa yake mata bayanin mutanen dake rayuwarsa ba, Farko da Faruk ya fara, sannan wani Ishaq da har yanzu bata gabshi ba bands yawan wayar da take jin suna yi, sai kawai ta ɗaga kanta a hankali alamun ta fahimta. "Zamu ɗan yi briefing a ciki, ba zaki damu ba?" Da sauri ta sake girgiza kanta, a wane dalilin zata damu, gidanta ne? ya gyada kansa shima sannan ya juya ya shiga ciki, hannayensa duka biyu sanye a cikin aljihunsa duka biyu, don rigar shaddar dake jikinsa bata kai gwiwa ba, kayan kamar ma sababbi ne, light brown, suna ta kyalli a cikin hasken safiyar. Wajen da ya dora hannunsa a bayanta ya sake ɗauka da irin abinda take ji a hannunta, sai kawai ta shaƙi wani numfashi mai nauyi a ƙirjinta sannan ta rufe ƙofar falon a hankali. *** "Me? Me kika ce Amina? Ya kawo wata arniya cikin gidan da sassafen nan?" Muryar Fatima ta faɗa cikin wayar dake kare a kunnen Amina, a hankali ta rufe idanunta sannan ta kai kofin shayin dake hannunta baki ta kurɓa. "Ba yadda kike tunanin bane Fatee, yace min sakatariyarsa ce, kuma zancen aiki ma suke tayi wai meeting suke dashi anjima." "Duk da haka ni dai banga wannan ya dace ba, ko ba komai gidan aurenki ne ya kamata a mutunta ki a cikinsa ko ba komai." Saura kaɗan murmushin da take yi ya suɓuce a cikin wayar saboda yadda Fatiman ke yawan fadar 'Gidan aurenta' ita kanta da take ciki bata ganin hakan kamar gaske tunda har yanzu babu wanda ya san abinda gobe zata haifar. "Ni sai naji muryarki ma kamar akwai wata damuwar daban bayan wannan, me ya same ki?" Fatiman ta sake tambaya, sai tayi ajiyar zuciya kawai, Fatima ta santa ciki da bai kwatankwacin yadda Amma ta santa, don sau da yawa ma abubuwan da zata iya ɓoyewa Amma da Fatiman zata yi shawara su haƙa su binne, ko Maryam da take ƴaruwarta ba komai nata ta sani kamar yadda Fatin ta sani ba, Don haka a yanzu ma dalilin kiran da tayi mata kenan, sai gashi ta gane tun kafin ta kai ga gaya mata. "Wani mafarki nayi da ya tashi hankalina jiya, ban taba irinsa ba Fatee, wallahi na tsorata sosai don har na farka ina jin kamar gaske ne." "Ya salam! Allah ya kyauta, kinyi addu'a dai ko?" Tambayar ta dawo mata da muryarsa sanda ya tambaya jiya 'Kinyi addu'a?' "Nayi, har asuba ma ina ta nafila, amma da na sake tunowa hankalina yake kara tashi, gashi na kasa fahimtar komai a cikinsa." "Babu abinda yake nufi insha Allah, ki cigaba da addu'a kawai kina kokarin yin taka-tsan tsan da komai insha Allah ba abinda zai faru Amina. Zanje wajen Malam mai almajirai anjima insha Allah in saka ayi miki rubutu, wataƙila wani satin zamu zo da Maryam sai in taho miki dashi." "Ba watakila ba, ku zo dan Allah Fatee..." "Kin san Amma ce tace sai an kwana biyu tukunna." Ta katse ta, sai ta girgiza kanta kamar tana kallonta. "Wallahi ko kullum zaku zo na gaya miki mutanen nan basu da matsala Fatee, yanzu kwana biyu ma kusan kullum ni kadai nake yini saboda duk sun koma makaranta, babu mai shigo min." Fatima ta girgiza kanta itama. "A abinda muka sani yanzun kenan Amina, gwara mu jira mu ga abinda lokaci zai haifar kafin komai ya daidaita, kar a sake ɓallo wani abu daban." Ta haɗiye wani abu a makogwaronta kafin ta amsa. "Toh shikenan. Ki gaishe min dasu Mamah da Ahmad idan yazo." Sai Fatiman tayi dariya tace. "Na gaya masa waccar gaisuwar taki ma sai cewa yayi wai kina matar auren yanzu kike cewa a gaishe shi? Wai in gaya miki kiyi azumi guda uku." Suka yi dariya a tare kuma da haka suka yi sallama fuskar Amina ɗauke da murmushin dake cike fal da kewar gida kamar kodayaushe. Ta ajiye wayar a gefenta tana kallon lokacin daya nuna akan ɗan screen ɗinta kafin hasken ya ɗauke. *** "Eh, yanzu zan fito... I will be there in 10 minutes insha Allah. " Ma'aruf

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73