Chapter 4
Chapter 4
around, from that hospital...(Ina yawan zuwa, daga wancan asibitin..)" Ya juya ya nuna asibitin sannan ya dawo ga fuskar mutumin da bata canja ba, sai kawai ya daga hannayen sa sama alamun sallamawa sannan yace. "What I mean is my brother is coming to pick me from here... So do you mind If I just wait for him while I eat these? Because honestly I dont have anything with me right now but I assure you he's going to pay when he arrive...." (Abinda nake nufi shine ɗan uwana zai zo yanzu ya dauke ni anan... so ba zaka damu ba idan naci wadannan kafin yazo, don bani da komai a jiki na yanzu amma ina tabbatar maka shi zai biya ka idan yazo...) Mutumin ya saka hannunsa ya danne kayan da yake shirin ɗiba, sannan da sautin muryarsa da yafi kauri a yanzu ya sake maimaita masa adadin kudin. "24 dollors." (Dubu goma.) Har ya haƙura ya ɗauke hannunsa yana shirin juyawa sai kawai mutumin dake tsaye a bayansa yace. "You're holding up the line, man! If you can't pay just leave." (Malam kana riƙe mana layi, idan baza ka iya biya ba ba ka bar wajen mana.) A sakannin da mutumin ya rufe bakinsa, a sakannin wani irin naushi ya ziyarci fuskarsa, naushin da ya kusan kaishi har kasa, ya ɗago jini na fara zuba ta hancinsa lokacin da wata mata a gefensu ta ƙwalla ƙara shi kuma ya furta kalmar zagi yana share jinin, kuma baiyi wata-wata ba ya nufo kansa da nasa naushin shima dsya haddasa fada a tsakaninsu ba shiri, kuma kowannensu yaji lokacin da mai kantin ya kwalla ƙara yana faɗin. "Someone should call the police!" (Wani ya kira ƴan sanda!) **** British Transport Police Station No. 2 Melton St, London NW1 2BW, United Kingdom. "Kun tabbata dukkan waɗannan bayanan file ɗin gaskiya ne?" Ɗan sandan ya tambaya daga tsallaken teburin da Ishaq ke zaune tare da wani ma'aikacin asibiti a gefensa. "Da gaske muke ranka ya dade, mara lafiya ne ya fito ba tare da an sallame shi ba, kuma a yanzu haka ma ba'a hayyacinsa yake ba." Ɗan sandan ya kalli ma'akacin asibitin da yayi magana, ya kara kallon ID Card ɗinsa da ya mika masa sannan ya gyada kansa yana sake kallon cikin file ɗin. "Naga dukkan wasu bayanai na cewar yana da matsalar kwakwalwa, amma banga wani bayani ko sau daya na abinda ciwon ke saka shi ba..." "Ai da yake yallabai, mu a asibiti cutar kawai muke bayani ba abinda zata haifar ba." Jin haka yasa Ɗan sandan ya dawo da hankalinsa ga Ishaq dake zaune yana kallon can gefe inda aka ƙulle tarin mutane a cikin wani budadden cell da aka zagaye da karafa kawai. "Kai ɗanuwansa ne ko? Zaka iya gaya mana abubuwan da yake yi, don mu san cewa ba da gangan yayi abinda muka kama shi yanzu ba?" Ishaq ya gyara zamansa bayan ya dawo da hankalinsa nan, sannan cikin harshen turanci shima yace. "Yayi abubuwa da yawa yallaɓai, waɗanda suka fi wannan ma, ba tun yanzu ba..." "Misali..." Ɗan sandan ya katse shi. "Misali zaka bani ba wani bayani ba." Jin haka yasa Ishaq haɗiye yawu ba shiri, ya juya ya sake kallon idanun da suke kallonsa daga cikin cell ɗin sannan ya gyara zamansa kaɗan, muryarsa can kasa yace. "Yallabai, a karo na ƙarshe da ciwonsa ya tashi saura kaɗan yayi kisan kai." Idanun ɗan sandan basu canja ba, ya cigaba da kallonsa na wasu sakanni kawai kafin ya gyaɗa kai, sannan ya nuna file din dake hannunsa. "Zan baku belinsa ne yanzu saboda wannan kawai, amma ku tabbatar bai sake barin asibitin nan ba sai da cikakkiyar lafiyarsa. Idan ba haka ba idan muka sake kama shi, mu zamu riƙe shi har sai ya warke." Dukkaninsu suka gyada kai alamun sun fahimta kafin ya juya ya kira wani ɗan sanda dake ƙoƙarin wucewa. "Stone! bring the Black one out." (Stone! Fito da baƙin cikinsu.) Stone ɗin baya bukatar wani karin bayani don wanda aka nuna masa shi kaɗai ne baƙi a cikin tarin turawan cell din, don haka ya zaro muƙullai daga jikinsa ya nufi wajen. Ɗan sandan ya sake kallon file ɗin hannunsa a karo na ƙarshe, idanunsa suka sauka akan sunan dake rubuce a jiki. Ma'aruf Mansour Bakori! #Aysha Shafi'ee. #FikraWriters #FararWuta. BABI NA BIYU. ~~~~ "Kowanne ɗan adam yana da tarin ƙalubale a rayuwarsa, amma ga wanda suke da cutar 'Bipola disoder' nasu ƙalubalen daban ne. Bipola disoder cutar ƙwaƙwalwa ce dake canja yanayin mutum a lokaci guda, ta canja ƙarfinsa, yanayin tunaninsa har da ɗabi'arsa. Cuta ce dake iya taba rayuwar mutum ta bangaren aikinsa, karatu, zamantakewa har ma ta iya dakushewa mutum hanyar cigaba a rayuwarsa, don tana yawan tashi ne akai-akai. Cutar tana farawa ne daga lokacin ƙuruciya, kuma duk da cewar babu takamaimai maganinta ana samun saukinta ko kuma ƙaruwarta idan har ba'a bin ƙaidojin magani daidai. Tana da matakai huɗu kuma na ƙarshen da ake kira da "Mania" shi yafi kowanne hatsari. A matakin 'Mania' mara lafiya yana jin tsananin ƙarfi da jin cewa zai iya komai, da kuma tsananin fushi da yawan tunanin abubuwa barkatai, wanda ke jawo mutum ya harzuƙa ta yadda babu mai iyawa dashi, mara lafiyar yana samun ƙarancin bacci da kuma rashin nutsuwa sannan wasu ƙwaƙwalwar su tana buɗewa ta yadda za su yi abinda idan a lafiyarsu ne baza su iya ba. Matakin dake bi wa wannan kuma shine 'HypoMania'...." Duk wannan bayanin yana fitowa ne daga wata Tv dake kafe a saman harabar wajen, ƙaton wajen jira ne na asibiti inda tarin ma'aikata ke wucewa wajen wasu gadaje daga can baya da aka kwantar da marasa lafiya, labulayen da aka sassaka a tsakanin kowanne gado sune kadai abinda ya raba gadajen. Bayanin dake fitowa daga Tvn, na irin rashin lafiyar ƙwaƙwalwar da ake dubawa a wannan ɓangaren asibitin ne, masu jiran kuma na zaune suna saurarar bayanan da ake yi mai dauke da hotuna don sauƙin fahimta ga marasa lafiyar da kuma masu jinyar, Ishaq yana ɗaya daga cikin masu jiran, yana zaune daga karshen kujerar kamar mai jiran ƙiris! Ya mike, kafarsa ta bangaren dama yake faman bubbugawa yayin da gefen bakinsa yake a cije. A bayyane yake ga duk wanda ya kalle shi cewa jira kawai yake likitocin dake tsaye a wajen gadon ɗan'uwansa su fito daga bayan labulen da aka zagaye gadon dashi. Sun taru kusan su bakwai a ciki har da Nurses don hankalinsu ya tashi jin cewar daga police station aka taho dashi bayan an neme shi an rasa. Ya sani cewar dukkaninsu tsoro suke yi game da ciwonsa, don Ma'aruf ya riga ya kai mataki na karshe a ciwon ƙwaƙwalwar tasa, ya riga ya kƙure komai a Bipolar Disoder, don idan har akwai wani mutum a duniya da baya taimakon kansa to Ma'aruf ne. A shekaru goma da cutar nan ta same shi babu irin fadi tashin da ba'ayi ba daga kowanne ɓangare na iyaye da kuma ƴanuwansa amma rashin tasa tallafawar ya haɓɓaka ciwon har sai da ya ƙaraso matakin ƙarshe, 'Mania Stage'. A baya bai fi ƴan awanni ko kwana ɗaya zuwa biyu ba yake yi idan ciwon ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73