Chapter 50
Chapter 50
rediyon tana neman lokaci, karfe ɗaya da rabi na dare, wani salatin ya sake suɓucewa a bakinta cike da mamakin yadda akayi tayi bacci mai nisan haka, sai kawai ta wullar da ita gefe ta janyo dankwalinta daya zame akan filon data kwanta tayi saurin ɗaure kanta, koina a jikinta rawa yake har yanzu yayin da mafarkin ke ƙara dawowa cikin kanta, bata fahimci komai a cikinsa ba amma Allah ya sani ta tsorata sosai da yadda abubuwa suka faru don bata iya tunawa idan ta taɓa irin wannan mafarkin a rayuwarta. Taji maƙogwaronta ya bushe yayin da amon muryar nan dake dariya a cikin mafarkinta ke dawo mata, bata san me hakan ke nufi ba, bata san waye zaiyi dariya alhali tashin hankali irin wannan yana faruwa ba, kuma har a yanzu tana jin cewa kamar ta san muryar amma ta kasa tabbatar da inda ta santa. Makogwaronta ya ƙara bushewa yayin da take kokarin saita zuciyarta da har yanzu ke bugawa, ta sauko daga kan gadon, wata doguwar riga ce a jikinta ta bacci da bata kai ƙasa ba ta gaba, don haka kusan tun daga saman gwiwoyinta a waje suke, kuma ba tare da tunanin komai ba tayi hanyar fita daga ɗakin. Kitchen zata je ta ɗauko ruwa, wataƙila zai iya wanke bugawar da zuciyarta ke yi bayan ƙishirwar, idan ta dawo tayi sallah raka'a biyu kuma, watakila tunaninta zai iya komawa daidai. Jikinta na rawa har a lokacin da ta isa kitchen ɗin, ta buɗe ƙofar a lokaci guda da hasken fitilar da aka kunna ya shiga idonta kafin shi, yana zaune daga kan worktable ɗin tsakiya na kitchen din, fitilar dake saman wajen ita ce a kunne da labtop a gabansa yana danne-danne, a gefe kuma foodflask ɗin abincin data dafa ne. Kuma duk da rikicewar da take ciki, ta gane cewar babu riga a jikinsa, wata bakar singlet ce kawai da ta fito da faɗin kafaɗunsa ta kowanne gefe, shima ya dago daga kan labtop din yana kallonta daidai lokacin da ta bude ƙofar. "Me ya faru? Me ya same ki?" Ya tambaya kai tsaye yana kallonta, kuma ba shiri wani abu ya zarce maƙogwaronta jin yadda muryarsa ta fito a cikin shirun daren tana gaya mata kamar har yanzu a cikin mafarkin take, sai ta ɗaga girgiza kanta kawai da sauri sannan ta sake haɗiye abinda ke bakinta kafin tace. "Ba komai, ruwa zan ɗauka." Da haka ta saki hannun kofar ta nufi wajen fridge, Ma'aruf ya bita da kallo zuwa wajen fridge ɗin, yanayin fuskarta a firgice yake sosai duk da kokarin da tayi wajen ɓoye hakan, kuma ko daga yadda muryarta ta fito ya san akwai wani abun, da wuri tayi bacci ya sani don bayan ya dawo yaga alamun hakan duk da yau cikin gida kawai ya wuce wajen Mami, acan yaci abincin darensa ma bayan sun tattauna maganganun da yasa ta kira shi, zancen Hamida. Kuma bayan ya shigo ya tarad da nata abincin jere a falo, haka kurum sai yaji wani iri, sai yaji kamar bai kyauta ba, ya sani ba zata ji dadi ba idan har ta farka ta ganshi a yadda ta ajiye tunda jiya ta bashi kuma yaci. Bai tsara komai tare da ita ba, abinda ya sani kawai shine aurensu zai zame masa garkuwa ne har lokacin da zai gama da case ɗin dake gabansa na kamfanin nan kafin ya fara binciken da zai shafe ta. Amma tun jiya da yaci abincin nata, sai yaji wani gefe a zuciyarsa ya kara nutsuwa da ita, har yana gaya masa gwara nata ma akan na Mami, tunda aƙalla ya san ita tayi da kanta, na Mamin kuma idan Samirah bata nan masu aikinta ne kawai. Don haka dole a yanzu da ya ɗebo aikin daya shirya zai kwana akansa, ya ɗauko abincin daga falo ya taho kitchen tunda babu Dining area a gidan, kuma ba yunwar yake ji ba amma da ya zuba ya fara ci sai yaji kamar dama bai ci komai ba, yaji hankalinsa ya sake nutsuwa sannan aikin da yake yi na tafiya akai-akai yayin da dukkan maganganun da suka yi da Mamin akan Hamida ke dawowa kansa kafin ta shigo a yanzu da yanayinta a hargitse. Sai kawai ya tura kujerar da yake kai baya ya mike tsaye. "Wani abu ne ya same ki?" Ya sake tambaya yana tahowa inda take shirin buɗe fridge ɗin, kayan jikinta yake kallo a yanzu, kamar na bacci ne... wata riga mai tsawo daga baya amma daga gaba kamar an guntule ta har wajen gwiwarta, don haka kafafunta na tsaye a waje, kuma bai san me yasa ba sai yaji wani abu a zuciyarsa na yabawa da yadda ɗankwalin kanta yayi kala ɗaya da rigar, Pink. Kallonsa take yi itama, idanunta farare na nuna dukkan wani alamun tsoron da ba sai ta furta ba, don haka kai tsaye cikin hasashensa ya sake tambaya. "Mafarki kika yi?" Amina bata san lokacin da ta ɗaga kanta ba don kayan jikinsa a yanzu sun karawa rikicewarta tasiri, bayan baƙar singlet din nan, three-quarter din wando ne kuma a jikinsa wanda da kadan ya wuce gwiwa, sannan ga muryarsa mai zurfi da taji tana tayar da wasu abubuwa akan fatar ta bayan rawar da jikinta ke yi. Kuma bata yi aune ba sai jin hannunsa kawai tayi ya riƙo nata ɗaya, ya jawo ta zuwa wajen kujerar daya taso ya zaunar da ita a ta gefen inda yake zaune kafin shima ya zauna. "Kinyi addu'a?" Tambayar ta tuna mata da abu na farko da ta kamata a e tayi, amma tsabar rikicewar da tayi, zuciyarta bata kawo mata wannsn lissafin ba, sai ta girgiza ksnta a hankali don ko tayi ƙokarin yin ƙaryar ma bata san me zata ce ba, ba zata iya wani tunani mai kyau ba slhali har yanzu yana riƙe da hannunta sannan ga kafafuwanta tun daga kan gwiwarta a waje daga ƙasan rigar nan, bama za'a lissafa da kayan jikinsa ba... "Suratul Ikhlas sau uku, Suratul Falak sau uku, Suratul Nas sau uku..." Muryarsa mai zurfi ta sake faɗa yana kallonta, bata da wani zabi sai ta rufe idanunta, ta haɗiye yawu a maƙogwaronta kafin a hankali bakinta ya shiga karanto su, bata jin sautin muryarta yana fitowa amma tana kaiwa karshe, ya sake cewa. "Ayatul Kursiyu..." Ta kai ƙarshe lokacin da taji kamar almara, ƴar rikicewar tata na bin iska, kuma shirun da yayi riƙe da hannunta bai saki ba wani abu ne daya saita numfashinta daga hawa da saukar da yake faman yi, taji kamar hannayen nasa sunyi wa nata wata rumfa ne ko kuma sun zama wani bango da ba abinda ya isa ya ratsa ta cikinsu ya cutar da ita, don haka a hankali nutsuwarta ta fara dawowa jikinta. "Mafarki ba gaskiya bane, daga shaidan yake zuwa ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru insha Allah." Sai kawai ta gyada kanta a hankali yayin da take ture dukkan wani tunani daga cikin kanta tana yarda da kalaman nasa don ta samu zuciyarta ta dawo daidai, Mafarki ba gaskiya bane, ta shiga biyawa zuciyar tata layi bayan layi. Abinda bata sani ba a wannan lokacin shine, wani lokacin mafarki na juyewa tamkar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73