Skip to content

Chapter 67

Chapter 67

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

Ma'aruf, a cikin mutanen gidan na san baza a rasa wanda zai tsaya maka a matsayin shaida ba, na gaya maka kuɗi kawai zaka basu har sai kayi limiting iya wadanda kake so, don wannan ita kadai ce hanyar da nake ganin zamu bi." Muryar Ishaq ta faɗa a cikin wayar dake kare a kunnen Ma'aruf wanda ke tsaya a barandar wani ƙayataccen Guest inn dake cikin garin na Jigawa. Hannunsa ɗaya ya zura a cikin gashin kansa kasancewar ya cire hular kansa ya baro ta a cikin mota. "Na gaya maka babu shaidar da zan gabatar Ishaq, ka barsu suyi dukkan abinda zasu yi, I have my ways akanta ita Ruƙayyan ita ta sani." "Ka shirya faɗuwa kenan tunda ka san kotu ita da shaidu take dogaro ko?" Ya cije leɓɓensa kaɗan. "Ko hakan ne zai faru let them Ishaq, na san abinda zanyi. Kar ka tanadi komai kawai ka cigaba da harkokin ka, Allah ya kaimu ranar." Da haka suka yi sallama a wayar da wataƙila itace ta huɗu tsakaninsu a yau kaɗai, ya kashe wayar daidai lokacin da wani ma'aikacin Guest inn ɗin ya ƙaraso inda yake. "Yawwa yallaɓai, gashi an kammala komai." Cewar matashin yana miƙo masa wani muƙulli. "Nagode sosai." Ya faɗa da murmushi yana karbar muƙullin ya zura a aljihunsa, kuma a cikin wayar tasa ya sake nemo nambar Hajiya Kilishi. A wanna lokacin Hajiya Kilishi na ɗakin Baffa wanda dawowarsa kenan daga tafiyar da yayi zuwa Kaduna, shayinsa take ƙoƙarin hada masa yayin dashi kuma yake daga can kan kujera yana shafa man robb akan kafarsa don fitowarsa daga wanka kenan a lokacin. Fuskarta ɗauke da faffaɗan murmushi ta ɗaga wayar tana fadin. "Mai gaskiya na, kun taho ne?" Ma'aruf ya girgiza kansa lokacin da yake tafiya wajen motarsa. "A'ah Mami, yamma tayi sosai, so zamu kwana ne sai gobe, yanzu ma zanje in dauko ta daga can." A lokaci guda irin wannan shirun dake biyo bayan walƙiya bayan haskawarta kuma kafin zuwan tsawa ya ratsa ƙwaƙwalwar Hajiya Kilishi da ta tsaya daga kokarin ɗebo madarar da take yi tana jinsa. Biyu kenan! Sau biyu kenan a jere Ma'aruf ya yanke irin wannan hukuncin ba tare da tuntubarta ba, na farko tafiyar tasu zuwa Jigawan da kai tsaye yazo yake gaya mata tare da kowa, a yanzu kuma kwanansu a garin? Me yake shirin faruwa ne? Ta girgiza kanta a fili lokacin da shi yake cigaba da gaya mata wani sabon labari na cewar baya son tuƙin dare ne, ba sai wani satin ba kamar yadda ta tsarawa Awwalu, a gobe ko jibin nan Ma'aruf zai sake komawa cikin ciwonsa. Ba ta yin saken da abubuwa ke cakuɗe mata, dole ne ta kwantar dashi don ta fahimci duk abubuwan data gano cewa suna ɗagewa daga cikin tsarinta. Wani abu da bata sani ba shine, abubuwa ma basu fara ɗagewa ba ko kaɗan! *** Kun fahimci cewa kowa ya shirya a wannan Babin??😅😅 To su waye zasu yi nasara? su waye zasu fara su kasa? Su waye kuma zasu faɗi kasa wanwar?? Me kuke tunani game da Amma da kuma ƙudirinta?😀 Kar ku manta kuma, zamu yi kwanan Jigawa....😍😆😆 #Aysha shafi'ee. #fikrawriters #FararWuta. BABI NA SHA BIYAR. ~~~~~~~ This could be the start of something new. -High School Musical "Ina zamu je?" Aminah ta tambaya lokacin da Ma'aruf yayi wata kwana data dauke su daga titin da ta kula cewa tun da suka shigo cikin garin Jifaywan a dazu shi suka yi ta miƙewa, muryarta a hankali ta fito yayin da take kallon hanyar. "Wani waje." Amsar tasa ta fito a gajarce ba tare da ya kalle ta ba. Sai ta juyo a hankali ga barin kallon titin da suke kai ta kalle shi ita, idanunta na shaida rashin fahimtar zancen, a can ciki kuma ruɗanin da take ciki, kamar ba zata ce komai ba amma sai muryarta ta sake fitowa. "Nayi zaton gida zamu tafi." Kalaman suka fito tare da nauyin yadda a yau bakinta ya furta wani waje daban da sunan Gida, saɓanin wajen da ta taso da rayuwarta a ciki. Ya girgiza kansa sannan ya juyo ya kalle ta, nauyin idanunsa suka sa taji kamar ta sunkuyar da kanta amma ta daure. "Dare yayi kuna bana son tuƙin dare a babbar hanya, so anan garin zamu kwana sai gobe tukunna." Yadda sautin muryarsa ya fito a cikin motar da kuma yadda yake kallonta yasa ta haɗiye wani abu a makogwaronta da bata san meye ba kafin ta gyada kanta alamun ta fahimta sannan kuma ta sunkuyar dashi ƙasa ta shiga wasa da karshen mayafinta, tattaunawarsu da Amma bata kare ba sam zuwansa ne ya katse su, wanda ta san haka ne, da tun a can ta roƙe shi fa ya barta ta kwana tare dasu idan yazo da safen sai ya koma ya ɗauke ta, wani abun ya sake zarcewa makogwaronta tuna cewa a yanzu bata san ina zai kaita su kwana ba ma. Amma duk da haka sai taji wani ɓangare a cikin zuciyarta na washewa, zuciyarta na rage nauyin da take ɗauke dashi a ɗazu mai cike da taraddadin rashin sanin abinda zata yarda dashi a al'amarin Hajiya Kilishi, ko ba komai yanzu ta san tana da babbar hanyar da take da yakinin zata samawa kanta mafita kamar yadda Amma ta fara gaya mata, Har a yanzu tana jin tasirin kalamanta da ya cika kanta taf! Yana ƙara buɗe wasu sababbin shafuka da a iya zagayen tunaninta gabaɗaya ita bata hango su ba. Tana jin yadda amon kalaman nata ke zagaye cikin kanta, ma'anarsu na bi ta cikin jijiyoyinta suna taso da ƙarfin gwiwar da ta nemi ta rasa, kuma duk da taraddadin da take ji, koina a cikin kanta dama jikinta yana gaya mata cewar yanzu ne komai zai fara, don kamar yadda Amma ta fada ne babban kuskuren da Hajiya Kilishi tayi, ya riga ya bude musu ƙofar nasarar su. "Mafitar ta riga tazo hannunki Amina, buɗe idonki kawai zaki yi ki kalle ta, kina da rabin maganin wannan matsalar yanzu a hannunki, wanda babban abun shine sanin halinta da kikayi, ita kanta bata sani bane amma tayi babban kuskure wajen bayyana miki sirrinta duk kuwa da na san cewa iya abinda take so ki sani kawai ta faɗa akwai sauran ƙurar da dole na san ta lulluɓe. Amma tun ana na fara raina lissafinta Amina, don da ace tayi bunƙasar da zan sara mata, da zata sami tarin hanyoyin da kema zata juya ki ba tare da kin san sirrinta ba..." Wasu daga cikin kalaman Amman kenan da suka ƙara saka ta yarda cewa mahaifiyarta na cikin irin daidaikun matan da ake misali dasu a duniya, masu halayen da dimbin jama'a zasu gani tamkar a mafarki, da kowacce kalma da ta gaya mata a yau, zuciyarta ta ƙara yarda cewa mahaifiyarta itace babban makamin da zata iya tunkarar komai dashi a duniyar nan bayan addu'a. Sai dai akwai wani abu guda daya a cikin kalaman nata dake fassara abinda zuciyarta bata taɓa lissafawa ba, abinda har yanzu da ta tuno yake rikita lissafinta yana sa hannayenta rawa, har yanzu bata gama sanin tunanin Ma'aruf game da ita ba, don haka ba zata taɓa iya ɗorar da

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73