Skip to content

Chapter 34

Chapter 34

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

akwai abinda zai saka Baffa ya canja maganarsa? Na gaya maka na yarda da auren ne saboda naga ba zan iya karewa ba, naga babu abinda zanyi wanda zai canja ra'ayinsa, yanzu ka gaya min da ban je ba ya fasa ɗaurawa?" Ishaq yayi shiru kawai yana kallonsa, sautin numfashinsa na fita da yawan da ya zarce daidai, don akan fuskar Ma'aruf din yake gane cewa abinda ya fada ba haka bane, dole akwai wani dalili daban da yake dashi game da auren nan, saboda abinda ya faɗa da farko gaskiya ne. Su biyun sun sani cewar wannan auren ba ƙaramin haɗari bane, abu ne da bai kamata ya faru ba, don haka ba saboda Baffa ya ture hakan ba ya sani, shi yasa babban tsoronsa shine abinda zai iya yi, don shi shaida ne akan tarin abubuwan da suka faru a baya, abubuwan da basa furtawa har yanzu balle na ukunsu ya sani, abubuwan da ba wai sunyi shawarar ɓoyewa bane kawai akwai su ne amma kamar babu su ɗin. Ya haɗiye wani abu a ƙirjinsa yana jin yadda shakka da kuma tsoron abinda Ma'aruf din zai iya ke bin koina a jikinsa, bai san yarinyar nan ba, bai taɓa ganinta ba amma yana tausayinta tun yanzu, don ya san wani rauninta a rayuwa aka kalla aka haɗa wannan auren, tunda a bayyane yake ga kowa cewar ba kowanne uba ne zai iya ɗaukan ƴarsa ya bawa mutum irin Ma'aruf ba, kamar babu banbanci ne da ka tura ƴar taka cikin dokar dajin da babu ranar fitowa. Sai kawai ya zaro wallet ɗinsa daga aljihu, kuma har a lokacin Ma'aruf ɗin na kallonsa da nasa idanun dake danne tarin abubuwan da yake dannewa, a cikin wallet din Ishaq ya zaro ID Card ɗinsa ya nuno masa shi, kuma da ganin haka Ma'aruf ya san me yake nufi, ya san cewa da gaske ransa ya ɓaci, don rana ta ƙarshe da ya fito da ID card ɗinsa yana tuna masa cewa shi lawyer ne zai iya ɗora aikinsa sama da alaƙarsu shine ranar da aka kai Baffa asibiti saboda ciwon zuciyarsa da ya tashi ta dalilinsa. "Ban san me kake shiryawa ba Ma'aruf, amma na yarda cewa ba ka yarda da auren nan saboda Baffa ba, akwai wani abu da kake ɓoye min..." "Jamal ya san yarinyar." A lokaci guda muryar Ma'aruf ɗin ta katse shi yana kallonsa. "Me kace?" Ya tambaya idanunsa na shaida rashin ganewar. Ma'aruf ya gyara zamansa, ya ƙifta idanunsa yana kallon Ishaq ɗin sannan ya sake maimaitawa. "Jamal ya san yarinyar Ishaq, so nake na san yadda akayi Jamal ya san yarinyar, wataƙila hakan zai iya bani damar da zan iya gano mutanen da suka sa na kashe shi!" Ya rufe bakinsa daidai lokacin da Faruk ya shigo Office ɗin yasha adon wasu fararen kaya har da babar rigar, bakinsa a buɗe yace. "Wai da gaske baka je ɗaurin auren ba?" **** Kayan jikin Amina wani farin Lace ne wanda aka ɗinka daga cikin kayan lefen, ta yafa farin mayafin da shima a cikin kayan yake, hannayenta sun sha ƙunshin da suka je har zoo road tare dasu Ummi suka yini ana yi, ɗaurin ɗankwalin da Momi tayi mata yayi baya da yawa ta yadda hakan ya fito da gashinta ta gaba, akwai fararen awarwaro a hannyenta har da wani zobe mai kyalli ma. Babu ko kwalli a idanunta amma ita kanta ta sani cewa kamanninta ba ɗaya suke da sauran ranaku ba, watakila suna da kuma matsayin aure yana zuwa ne da tasirin dake banbanta kowacce amarya da sauran fuskoki, don ita kanta ta sani cewar fuskarta tayi wani irin fresh da kuma kyan da kowa ke gani tare da fararen idanunta, fatar fuskarta har maiƙo take saboda yadda take tas babu ko ɗigon ƙananun ƙurajen da ta saba fama dasu. "Fatee, ina gurasar? Jiranki fa muke yi!" Wata Shukra ɗaya daga cikin kawayenta a islamiyya ta kwallawa Fatiman dake can cikin hayaniyar tsakar gida kira, a cikin ɗakin nasu ƴanmata me fal da suka haɗa da kusan duka ƙawayen su na islamiyya da kuma na makarantar boko wanda duk a ƙoƙarin Fatima ne ta tattaro su, sannan ga su Ummi ma da tasu tawagar ƙawayen, don haka ɗakin ya cika taf sai faman hayaniya suke wadda ke sajewa cikin tarin ta gidan gaba ɗaya. Don ko'ina a cike yake taf da mutane sai faman rabon abinci kawai ake, babu wanda yayi tunanin za'ayi wannan taron, Amma bata taba lissafa cewa yawan waɗannan mutanen zasu taru ba, amma ance wai biki dama ba'a masa gayya da kansa yake fallasa kansa, musamman ga su ɗin da kusan duk wanda suka mu'amalanta yana jin daɗin zama dasu. A lokacin Maryam ta shigo ɗakin riƙe da wani faranti da aka cika da ƙullin zobo. Ummi da tasha kwalliya cikin ankon atamfar nan tace. "Yawwa Mary, matso ta nan, tun dazu dama Aunty Safiyya ke cewa mu jira a kawo." "Taɓ! Wallahi na wannan ƙawaye na ne suna can a dakin Aminu, plate nazo nema idan kun gama zan zuba gurasa." "Au ba zaki bamu ba?" "Waashi can fa ana ta ɗiba a ɗakin Amma, kuje ku ɗebo naku kafin ya ƙare don wallahi har yaje rabi." Ummi ta miƙe da sauri tace. "Mu nawa ne a dakin?" "Ai kawai je ki ɗebo ashirin, in ma da saura ma kara." Cewar wata a cikin ƙawayen Aminan suna ƙyalƙyalewa da dariya gabaɗayansu. Ummi ta fita daidai lokacin da Fatima ta shigo rike da plate guda biyu na banɗashen gurasar, Maryam kuma ta juya ganin ba zata samu abinda tazo nema ba. "Wallahi kowa ya ɗauke hannunsa kafin in ajiye." Cewar Fatiman ganin yadda kowannensu yayi shiri da hannunsa. "Dalla malama ki ajiye kawai meye haka wai?" Cewar Shukra. "Wallahi sai kowa ya ɗauke hannunsa, salon ina ajiyewa in rasa." Ta faɗa tana dariya, yayin da hayaniyarsu ta ƙaru kowa na fadin ta ajiye, ai kuwa tana dire farantin kafin ta mika nata hannun ta nemi gurasar ta rasa, sun wawushe ta tsaf suna ƙyalƙyala dariya, kuma yanayin fuskar Fatiman yasa Amina dake daga gefensu yin dariyar itama, lebbenta yayi talewar da har haƙoranta suka fito, don abu ne da ba yau suka saba ba, tun a makaranta sun saba irin wannan abin da an kawo abinci kawai wanda ya samu ya samu. Kuma dariyar taji tana tafiya har ciki ƙirjinta, tana taɓo wani abu da ya kamata dama ace yana nan, wannan farin cikin da mace ke ji a lokacin aurenta. A cikin hayaniyar da ɗakin ya ƙara ruɗewa dashi Aunty Ma'u tazo ta kira ta, tana fita taga Aminu ne yazo da mai hoto, aka shiga ɗaukar hoton kowa da ƙungiyarsa, Aminu na tsaye shine mai bada umarnin dake sa kowa yin dariya, don haka kusan duk a hotunan an ɗauka ne Amina na dariya, tayi kyau a cikin kayan da suka zauna a jikinta sosai ga kuma skirt ɗin kayan daya buɗe ta ƙasa, ita kanta ta yarda cewa telan nasu Ummi ya iya ɗinki ba'a banza suke ta yabonsa ba, kuma a kowanne hoto ita idonka zai fara gani saboda shigar kayan nata farare tas da kuma baƙin gashinta daya fito ya haɗu da baƙin ƙunshin

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73