Skip to content

Chapter 46

Chapter 46

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

kawo wata gudunmawa kayan kitchen ɗin ne, don haka har wasu abubuwa ta ware a cikin ranta cewar zata ajiyewa Maryam idan lokacin nata auren yazo. Sauran ɗakunan nan biyu ashe ɗaya carpet ne kawai da labulaye da kuma su tintin a jere, sai ɗayan ne aka tsara shi da wani irin nau'in furnitures masu tsananin kyau da ɗaukar ido, komai kalar grey, milk da kuma ash ne, wani silk bedsheet din da aka shimfide gadon dashi yana ta daukar ido a cikin hasken fitulum ɗakin, Aunty Safiyya bata sani bane da take cewa tayi zamanta a dakinta, dama ba'a tsara wannan don ita ba, shi suka yiwa abinsu, don har wasu fitulu aka saka a tsakiyar ceiling ɗin dogwaye masu haske, ga kalar fentin shima grey ne, labulayen kuma milk gabaɗayansu. Kasa rufe bakinta tayi a lokacin da su Ummi ke cigaba da santin ɗakin daga inda suka tsaya a bakin kuma ƙaton akwatin dake ajiye akan gadon, shi ya hana kowannensu shiga don ba sai ta gaya musu ba sun riga sun gama sanin dakin na waye. Ta fita ɗakin ta rufe kofar a hankali kamar mai tsoron kar a jita sannan ta nufi hanyar kitchen, daga tsakiya akan work table ɗin nan tray din dake dauke da flask din abincin da ta gama ne, a yau zata danne zuciyartaa tayi abinda ta kasa jiya, shekaranjiya ya aiko aka kawo kayan abinci kamar ya san dana ta matsu ta fara girki da kanta, don haka kai tsaye ta gayawa Samirah cewa ta huta tunda dama ita ke kawo mata abinci kullum, abincin da ita kadai take ci don ko yana sanin an kawo ɗin ma bai taɓa tambaya ba, ta fahimci idan ya dawo yayi wanka wajen Mami yake tafiya yaci abincinsa sannan ya dawo. Don haka ko jiya da tayi girkin, har dashi tayi amma tana ɗaki tana biya abinda zata ce masa taji ya buɗe kofar falon ya fita, haka ta debi abincinta ta rufe a fridge, amma yau ta gama shirya cewar ba zata bari ya fita ba, ba don komai ba sai don tarin nasihohin nan da aka yi mata suna ta yawo a cikin kanta, gani take kamar laifi take idan zata yi girkin babu shi, don akwai nasa hakkokin akanta kamar yadda shi ya sauke nasa wajen kawo abincin. Bayan haka ma, ta karanci kalolin kayautata zamantakewa fiye da adadi a wajen Ammarta, abinda ke cikin zuciyarta kenan fal kuma dashi tayi tunanin zata iya cin galabar komai dama, har yanzu bai nuna wata alama ta cutar da ita ba don haka don me yasa ita zata fara da abinda bai dace ba? A cikin addu'o'in da Gwaggo Balkisa tayi mata tace '... Allah yasa masa tausayinki a zuciyarsa..' To idan bata kyautata masa ba ta yaya zai ji tausayin nata, Me ƴan uwansa ma zasu yi tunani idan hakan ta cigaba? Idanunta suka hasko mata Hajiya Kilishin da yake zuwa wajenta yaci abincin, bata san me yasa ba ita har yanzu zuciyarta bata kwanta da ita ba, ranar da su Samirah suka fara kaita wajenta, hannayenta duka biyu ta kamo tace. "Barkanki da zuwa cikinmu Amina, zuciyata cike take da murna idan na tuna cewa ƴa ta na kawo gidan nan ba kowa ba, ki saki jikinki ki saba da kowa, don a gidan nan bama taba banbanta kanmu, kowa ɗaya ne kuma kowa yana samun tallafawar ɗan uwansa saboda ƙaunar dake cikin zuciyoyin mu, kuma kema kin shigo kenan cikin wannan lissafin namu, rayuwarki zata canja da dukkan alkhairin da dake tare damu, kuma ina fatan kema zaki bamu damar amfana da irin naki alkhairin." Haka kurum a lokacin sai taji maganganun basu tafi har cikin zuciyarta ba, sai taji kamar sun tsaru da yawa ace kai tsaye take faɗarsu daga zuciyarta a wannan lokacin, amma ko da ta daga ido ta kalli fuskarta, sai zuciyarta ta ture wannan kokwanton a gefe, tana tuna mata cewa itace wannan Hajiya Kilishin da ta tallafi rayuwarsu ta ɓangarori da yawa. Hajiya Kilishin da kullum Baba yake ambato da kyawawan kalamai sannan kuma kamar yadda ta gani ta itace jagorar wannan gidan, don a yinin yau kawai ta fahimci abubuwa da yawa sai da izininta ake yi, don haka saboda tana ganin itace umul'abasin faruwar wannan auren bai kamata zuciyarta tayi wannan tunanin ba. Amma Allah ya sani da suka shiga wajen Hajiya Maimunan wadda aka gaya mata itace asalin mahaifiyar Ma'aruf, zuciyarta kusan narkewa tayi tun kafin ta kai ga zama, mace ce har mace, irin manyan matan nan masu tsananin kamala da nutsuwa, fukarta fuska ce da za'a iya amfani da ita a koina a fadin duniya ta wakilci kalmar 'Uwa a rayuwar bahaushe' sai dai babu ƙafafu, tana zaune kan Wheelchair ɗinta da Hisnul Muslim a hannunta. Kuma abinda ya bata mamaki shine itama da fara'arta da komai itama ta karɓeta, tana ta zuba tarin addu'oin fatan alkhairi da kuma fatan zaman lafiya a tsakaninta da Ma'aruf, wani abu data lissafa cewa yayi ƙaranci a kalaman Hajiya Kilishi. Sai kawai ta ture wannan tunanin ta dauki tray din ta taho falon, sai da ta tsaya tana ta tunani inda zata ajiye kafin ta tsugunna a hankali daga gaban Three-sitter dake gabanta, kuma tsugunnawar tata tayi daidai da fitowar Ma'aruf daga falon, ta dago da kanta lokacin da kafafunsa suka tsaya cak yana kallonta daga hanyar kofar da ya nufa. Yayi wankan, ya canja yansa zuwa wani bakin wando da dark navy blue riga data dace da kalar daren, kallonta yake yi da mamakin dake nunawa karara a fuskarsa, sai kawai tayi saurin ƙarasa ajiye tray din sannan ta mike tsaye itama. Kanta a sunkuye hannayenta cakude da juna tace. "Barka da dare." A cikin shirun dakin muryarta ta fito kamar wani fukafikin dake tahowa kasa a hankali, Ma'aruf ya gyada kansa yana kallonta har yanzu da mamakin a fuskarsa kafin ya amsa da. "Kin yini lafiya?" Haka yake tambayarta kullum, don haka ta gyada kanta ba tare da ta dago ko ta daina cakuɗa yatsunta cikin juna ba, kuma sai tayi shiru bata ƙara cewa komai ba. Amina ta san ya kamata tace wani abun game da abincin da yake kallo a gabanta amma bata san me zata fara cewa ba, kuma ga mamakinta sai kawai taji yace. "Wannan abincin..." "Naka ne..." Ta ƙarasa da sauri tana ɗago da kanta, idanunsu suka haɗu waje guda sai tayi saurin sake maida kanta kasa ta cigaba da murza yatsunta, amma zata iya karanta mamakin daya karu cikin muryarsa sanda yace. "Masha Allah, kamar kin sani dama yunwa nake ji." Wani abu a cikin zuciyarta yayi tsalle da jin hakan, yayi kokarin subucewa daga zuciyarta zuwa kan fuskarta amma ta tare shi da karfi tana cigaba da motsa hannunta, ƙarar takunsa taji yana tahowa don haka tayi saurin tsugunnawa ta ɗauki plate din tana bude murfin flask ɗin farko. Ƙamshin abincin ya shiga hancin Ma'aruf sanda ya karaso kan carpet din, idanunsa na kallonta tana zubawa yayin da ƙaramin mayafin data yafa kalar kayanta ya zame yana reto a gefen fuskarsta, wani abu yake ji na daban yana shiga zuciyarsa bayan mamaki, sai kawai ya zube wayoyin hannunsa akan kujerar sannan ya ƙarasa

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73