Skip to content

Chapter 18

Chapter 18

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

da nasa murmushin shima. Wajen karfe biyun dare bayan kowa ya kwanta, ta hango shi ta ƙofar ɗakinsu a wajen banɗaki yana miƙe bayansa, kukan da tayi a cikin filonta a wannan daren Allah kaɗai ya san yawansa, abu ɗaya kawai ta sani shine tayi wa kanta alƙawari a wannan ranar cewa ko abinda yafi rayuwarta ne zata sadaukar a duniya don farantawa mahaifinta. * "Wallahi gani nake yi kamar zaki ƙyalƙyale da dariya ki gaya min wasa kike yi." Fatima ta faɗa tana kallon Amina data idar da sallah a gabanta. "Ke ma kin san ai ban taɓa miki irin wannan wasan ba, da gaske nake Fatee, don yanzu haka ma Baba ya tafi gidan Kawu Mallam ya faɗa masa." "Ya fada masa cewa kin yarda zaki auri wanda yake da matsalar ƙwaƙwalwa Amina...? inalillahi wa'inna ilaihir raji'un Amina kin san Allah ko da nake cewa ki rabu da Abdallah ki samu wanda yafi shi ba irin haka nake nufi ba, ya za'ayi kiyi irin auren da ake bada labarin ire-iren sa a sigogi mara sa daɗi?" Fatiman ta ƙarashe muryarta na karyewa. Amina ta cire hijabin sallar tana kallonta, "Ban gane me kike nufi ba?" Ta tambaya tana kallonta. Fatima ta girgiza kai kafin ta gyara zamanta. "Amina duk wanda yaji batun auren wallahi shaidar da zaiyi miki daban, kowa cewa zaiyi auren kuɗi zaki yi, musamman ƴan unguwar nan da kin san daman ƙiris suke jira akanki." Amina ta haɗiye wani abu a maƙogwaronta, abinda Fatiman ta faɗa gaskiya ne ta sani, kuma maganar iri ɗaya ce da maganganun Amma na jiya, duka su biyun ƴancinta suke nemar mata, amma a wajenta darajar mahaifinta itace a gaba da ita kanta don haka ta riga ta gama yankewa kanta hukunci, ta gayawa zuciyarta cewa zata tsaya tare da mahaifinta koda zata mutu sau biyu idan ana yi. "Fatee na tabbata ba fa ba wai matsala ce sosai ba, kawai sun faɗa ne saboda kinga a aure ba'a ɓoye komai, kuma ma Baba yace baza'a bari maganar ta fita ba, kema kin san ba zan iya ɓoye miki bane." Ta faɗi hakan yayin da idanunta ke hango takardar data cusa cikin kayanta a jiya, babu wanda ya san da ita, babu wanda ta gayawa hatta Amma kuwa duk yadda kowanne abu mai hankali a cikin kanta ya tsorata da maganar dake rubuce, amma ta sani cewar in har iyayenta suka ji hakan dole zai iya sake zama wani ƙalubale musamman ma a wajen Amma don haka ta yanke hukuncin ɓoyewa tunda ba zata taba fatan abinda zai hadassa mahaifinta yaji kunya ta dalilinta ba. Kuma kafin Fatiman ta sake cewa wani abu suka tsinci sallamar Ummi daga tsakar gida, ƴar Kawu mallam wadda suke kusan sa'anni da Aminan. "Ina amaryar take?" Muryarta ta fito da fara'a bayan ta gaisa da Amma da kuma Maryam wadanda suke kitchen, ta karaso ya ɗage labulen ɗakin tana kallon Amina bakinta a washe. "Yarinyar nan da tsinannen wayo, sai dai muji kawai wai zaki yi aure?" Sai dai Amina tayi wani guntun murmushi kafin tayi mata sannu da zuwa. "Ni ba zan amsa ba wallahi, tunda sai da muka ga meeting ɗin su Kawu yayi tsawo sannan da kyar muka san me ake ciki, da ake ɓoye mana naga wanda zai raka ki siyayyar kayan bikin ai." A cikin maganar ta Amina ta tsinci wani abu, cewa da gaske Baba yake a ɗazu daya shaida mata cewar kowa zai ji maganar auren ne ta fuskar alkhairi, babu wanda zai san me ake ciki, gashi kuwa ko iyalan Kawu Mallam ɗin da ake taruwa a gidansa basu san komai ba, zurfin maganar ya tsaya a iyakar Baba da yayyensa ne sai kuma Amma, Fatima, Maryam da Aminu da suka sani a yau. Ance zancen duniya baya ɓuya, amma har cikin ranta tana fatan zancen ya tsaya a iya wadannan mutanen kawai. "Ai ni ban yi zaton har ɗan bokon naki ya gama makaranta ya shirya ba, shi yasa wallahi abun ya bamu mamaki sosai, har su Umma ma cewa suka yi koda wasa Amma bata yi musu zancen a kurkusa ba." Amina ta girgiza kanta. "Ai ba shi bane Ummi, wani ne daban." Sai da Ummin tayi shewa kafin tace. "Gaskiya ne yarinyar nan, kice da karfinki kika taso, Fatima bani labari don na san zanfi ji a wajenki, wane ne sabon kamun?" Fatima tana take tace. "Wallahi kin san al'amarin Allah ai, kawai komai a lokaci guda yazo." "Eh, amma dai da maiƙon sa ko? Yadda komai ya taso a lokaci gudan ai na san a shirye yazo ko?" Kawu malam mutum ne malami mai sauƙin sha'ani, amman sai Allah ya bashi matansu duka ukun masu azabar son kuɗi, kuma suka taso da ƴaƴansu ma gabaɗaya akan hakan, gashi mata sunfi yawa a ciki don haka a zaune yake cewa basa auren kowa sai mai abin hannunsa ire-iren ƴan kasuwa, gasu da surutu da kuma kauɗi, hakan yasa duk kusancinsu dasu Amina basu fiye shiga cikinsu sosai ba don halayensu sun banbanta duk kuwa da cewa suna da mutukar kirki. "Ai kuwa dai yana da kuɗi gidansu ma haka." Fatima ta bawa Ummin amsa har a lokacin tana murmushin yaƙe. "Kice dole ne mu raƙashe a bikin nan, wallahi azo a saka mana rana ma nan kusa Momi tazo mu fara shirye-shirye, zaki yi anko?" Amina taji wani abu ya tokare mata a maƙoshi, don ita har ta yanke hukunci bai taɓa zuwa kanta cewar ma biki za'ayi ba, gani take kamar jana'iza kawai za'ayi akaita, kuma sai Allah ya taimake ta kiran Amma yazo a daidai lokacin don bata san amsar da zata bawa Ummin ba. Amma ta kalle ta bayan ta isa kitchen din, fuskarta fayau tace. "Kizo ki zuba muku abinci gashi nan an sauke." Ta haɗiye yawu a hankali tana ƙarasawa ciki, lokacin da flask ɗin ruwan zafin nan ya faɗi daga hannun Amma, sai ya zama kar ya fashe da dukkan irin hukuncin da take tunanin Amman zata dauka akan ƙin bin maganarta da tayi, don a lokacin bata ce komai ba, juyawa tayi kawai ta bar wajen yayin da Baba ke saka mata albarka, kuma bayan taje ta same ta a ɗaki, abu daya kawai tace. "Rayuwarki ce dama Amina, na nuna miki kuskuren dake ciki ne kamar yadda yake alhaki na a matsayin uwa, kuma tunda har kinga zaki iya dauka, ga fili ga maidoki nan, zuciyata ba zata riƙe ki da komai ba, Allah ya baki sa'a." Daga haka bata ƙara cewa komai ba, kuma bata yi fushin da Amina tayi zato ba, harkokinta ta cigaba da yi a gidan kamar dama maganar bata taso ba, kamar dai shekaranjiya da Baba bai ko ziyarci gidan Hajiya Kilishi ba, balle su san da komai. Ta zuba abincin ta kai musu, suna ci Ummi na daɗa bada bayanin yadda abubuwa zasu kasance wanda daga ita har Fatiman yaƙe kawai suke suna amsa mata, wajen la'asar ta tafi, lokacin ma Fatima ta daɗe da tafiya asibiti inda tace yau za'a sallamo kakarta. Wajen ƙarfe biyar, Aminu ya shigo gidan riƙe da wani flask lokacin da take wanke-wanke ita kaɗai a gidan, don Amma ma ta shirya ta tafi

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73