Skip to content

Chapter 10

Chapter 10

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

na mutuwar auren, don Maamah bata taɓa sani bane, amma MA'ARUF shine sanadiyar mutuwar aurenta da Alhaji Ahmad. Kuma ko a yanzu da kowa ke kwaɗaita mata auren Jawad, ita ta sani cewar abinda ya faru shi zai sake faruwa, babu wanda zai taɓa iya cike gurbin Ma'aruf a ranta, ta so shi tun bata ma san kanta a duniya ba balle ta san menene son, ta so shi da dukkan kowanne bangare na ruhinta, don rayuwarta ma gabadaya tare dashi ta gina ta. Iyayensu maza abokan juna ne tun da dadewa, saboda haka ba zata taba iya cewa ga ranar data san Ma'aruf ba, tayi wayo ne kawai a duniya tana iya lissafo shi a cikin abubuwan da ta sani na rayuwa, don haka kowa ya sani cewar tsananin kulawar da take yi masa shi ya janyo hankalinsa akanta shima har ya kai ga soyayyar su. Sai dai a lokacin da ta aure shi, ta auri wani Ma'aruf din ne daban saɓanin wanda ta sani, ta san hakan don yasha gaya mata cewa Ma'aruf din data sani ya mutu babu ko da digonsa a cikin zuciyarsa, amma ta rufe idonta daga komai tace taji ta gani har aurensu ya tabbata. Auren da tun a darenta na farko a gidan abubuwa suka yi juyin waina daga yadda take hasko su. Ta rufe idanunta a hankali tana tuna dukkan abubuwan da suka faru a waɗannan shekarun, irin wahala da barazanar da rayuwarta ta fuskanta, sai dai ashe bata san gwara su sau dubu akan abinda zata je ta tarar a gaba ba, don a yanzu ta gane abinda taso ta manta a baya, cewar duk duniya Ma'aruf ne kadai namijin daya tattara duk wasu halayen da take so a wajen namiji. Shi yasa bata son sake maimaita kuskure na uku a yanzu, bayan guda biyun da tayi a baya na fitowa daga gidansa har kuma da auren Alhaji Ahmad. Ta riga yankewa kanta shawarar cewa ba zata sake biyewa kowa ba, ra'ayin zuciyarta kawai zata bi, zata samo yadda zata koma cikin rayuwar Ma'aruf kotawacce hanya kuwa, kuma bata ma tunanin cewa hakan zaiyi mata wuya tunda tana da abinda daga shi har iyayensa zai kassara su. Hameeda... Tayi murmushi tana sake kallon yarinyar, lokaci yayi da a yanzu zata san waye mahaifinta! *** A wannan daren.... Na baki amanar rai na, daiman Yau zaki ceton raina, abadan Kin ƙulle mini kwaɗon raina, da'iman Ki taho, raina yana sururi numfashina kece abadan dai'man! "Maryam dan Allah ki kashe waƙar nan, dan Allah." Amina ta faɗa tana hararar rediyon da Maryam din ta kunna, ta jingina ta da langa-langar langar kitchen ɗinsu yayin da ita take ciki tana girki. "Haba mana Yaya, kin san yadda nake son irin waƙoƙin nan fa, kuma yanzu zasu cire ma don wani shirin zasu fara." Maryam ɗin ta faɗa daga cikin kitchen ɗin, kuma jin tayi shiru yasa ta kara da... "Idan ana yi wallahi ji nake kamar in tashi sama don dadi, da wayarki android ce ai da har sai kin gaji da jin su ma." Amina ta girgiza kanta daga kan tabarmar da take zaune Hafsa a kwance akan cinyar ta tana tsefe mata kalbar da ta baɗe ta tsaf da wani sabon yashi da aka zube a layin nasu inda yara kamarta ke tururuwar wasa. "Ni basu dame ni ba sam, kawai a yanzu ne ban ga amfanin jin waƙar ba tunda kin san abinda yake faruwa." Jin haka yasa Maryam ɗin tayi shiru tana cigaba da yanka cabbage ɗin dake hannunta, kuma a daidai lokacin ma suka cire waƙar, muryar wani ma'aikaci daga gidan rediyon ta fara gabatar da shiri na gaba a jerin shirye-shiryen su, amma tuno abinda ke faruwar kamar yadda Amina tace, yasa Maryam ta ajiye wuƙar hannunta ta taso ta kashe rediyon gabaɗaya. A jiya da Baba ya fita zuwa kiran Hajiya Kilishin da yace, bai dawo ba sai wajen sha ɗaya saura na dare har su Hafsa da Adam sunyi bacci a sannan, wanda hakan wani abu ne sabo a wajensu, wani abu daban, saboda ba don sun kira shi a waya har ya ɗauka ba ma, Amina ta san tsaf Amma zata iya saka hijabinta a daren ita da Aminu su fara tafiya nemansa. Shi ba mutum ne mai dadewa a waje ba musamman idan dare yayi, abubuwa da yawa komai muhimmancin su in har dare ya raba to zai ajiye su ne sai zuwa gobe, ko hirar maza irin ta daren nan Baba baya taɓa zaman yinta, tun suna yara sun taso da sanin cewa lokacinsa da daddare nasu ne, a cikin iyalansa zai zauna ayi wasa da dariyar da a cikinta zai fahimci dukkan matsalolinsu. Don haka a jiyan da ya kai goma sha ɗayan dare dole zuciyoyinsu suka kasa nutsuwa sai lokacin da suka ji ƙarar shigowarsa da kuma rufe kofar gidan da yayi, babu wuta a lokacin, sannan Aminu ya fara tararwa jingine da bango yana danna wayarsa. Kuma ta cikin ɗan hasken fitilar tsakar gidan da batiranta suka gama yin sanyi, Amina ta hangi fuskarsa tattare da dukkan wani nau'i na damuwar dake fitowa har a cikin sautin muryarsa sanda yake amsa gaisuwarsu, gaisuwar da daga ita bai sake cewa komai ba, ya nufi hanyar ɗakin sa kawai ya shige. Amma ta ɗebi kwanukan abincinsa ta bishi dasu yayin da suma kowa ya kama hanyar makwancinsa, Aminu yayi hanyar soro inda ƙofar ɗakinsu shi da Adam take, su kuma suka dauki Hafsa suka shige nasu dakin, kuma ba sai ta tambaya ba, Amina ta sani daga ita har Maryam da Aminun babu wanda yayi baccin kirki a ranar. Kuma babban abinda ya ƙara tsurar dasu shine na yadda har a yau basu ji komai ba, ko daga bakin Amman kuwa. Baban bai ko je aiki ba a yau, tun safe ya fita zuwa gidan wansa da suke kira da Kawu mallam kuma bai dawo ba har yanzu, Amman ma kusan a daki ta yini tun bayan fitarsa, ita kadai tayi ta kai kawo a gidan bayan sun tafi makaranta, tace mata wai gyaran durowarta take yi, amma tsaf Amina ta sani cewa kayan nata data barbaza akan katifar ɗakinta ba don ninki ta fito da su ba saboda yanayin dake fuskarta kusan iri daya ne da wanda ke kan fuskar Baba tun a jiya da daddare, kuma wajen la'asar sai ga kiran Baba a wayar Aminan cewa Amman taje ta same shi a gidan Kawu mallam ɗin, wanda hakan shine abinda ya ƙara ɗaga hankalinta, da ƙyar Aminu ya shawo kanta bayan sun dawo daga makaranta kafin ya tafi wajen aikinsa shima. Sai dai kafin ta bawa Maryam amsa, Adam yayi sallama yana shigowa. "Salamu alaikum, wallahi Yaya yarinyar nan ƙarya take, babu wanda ya ture ta, wasan banzan su kawai suke yi, ga sauran ƙawayen nata can ma har yanzu a kusa da yashin." Ya zayyano dukkan wannan bayanin daga tsaye kasancewar shi yaje ya zaƙulo ta tsakiyar masu wasan yashin. Da jin haka kuwa Hafsa tayi narai-narai da muryarta ta shiga rantsuwa tana faɗin da gaske ture ta akayi ta faɗa kan yashin, wanda kowa ya san ƙarya ne wasanta tayi daga yadda baƙin gashin kan nata ya burɗine

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73