Skip to content

Chapter 73

Chapter 73

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 868 words 0 views Progress saved
Download Book

haka a baya na tsaya da ƙafata sosai wajen takura masa a duk lokacin da ya kamata yasha maganin, kafin daga bisani na fahimci cewa hanyar nasarata tana tattare da ikon da nake dashi ne akan magungunan sa. Ina son Ma'aruf Amina, amma son da nake yiwa cikar burina yafi karfin nasa, shi yasa nake rufe idona a duk lokacin da buƙatar in kwantar dashi ta taso min ina yin hakan." Tayi shiru na tsawon wasu sakanni tana kallon yadda tasirin maganganun ke aiki a fuskar Amina kamar yadda ta zata kafin ta cigaba. "Magungunan dake cikin jakar nan har America naje na nemo su Amina, magunguna ne dake birkita ƙwaƙwalwar mutum a lokaci guda ya fita daga hayyacinsa, kuma dama ciwon Ma'aruf abinda yake bukata kenan ya tashi, don haka duk sanda nake shirin yin wani abu da na san zai iya zame min ƙalubale, sai in kwantar dashi in gama duk abinda zan yi kafin ya dawo hayyacinsa." Ta kai karshen maganar kamar bata karasa ba, don dukkansu shiru suka yi yayin da nauyin kalaman ke zagaye iskar dakin, ba irin ga Amina da taji hannayenta har rawa suke yi ɗauke da sabuwar rikicewar da maganganun suka sata, don yau ne karo na farko da ta ji ciwon Ma'aruf daga makusantansa, ko shi bai gaya mata ba, cewa kawai yayi 'I'm a mess Amina...' Zuciyarta ta ajiye komai a gefe ta shiga gaya mata cewa har ta gama rayuwarta a duniya ba zata taba iya haɗuwa da wata muguwar halittar irin Hajiya Kilishi ba. "Na san idan Ma'aruf yayi aure dole ne zargi zai shiga zuciyar wasu idan har na cigaba da rike magungunan sa, don haka wannan yana daya daga cikin dalilan da suka sa na kawo ki gidan nan, daga yau magungunan nan sun koma hannunki. Ki ɗauka ki tafi dasu, guda uku ne a ciki, ki ɓalli kowanne guda ɗaya ki bashi a gobe, don jibi zan fara aiwatar da abinda ke gabana kuma a sannan bana buƙatar ganinsa a kamfanin. Wannan shine aikin ki na farko Amina, kuma idan komai ya tafi daidai, zaki fara ganin daidai bari nayi miki alkawarin farko tun a yanzu, idan na samu abinda nake so Amina zan sa a fitar da ɗanuwanki Aminu ƙasar waje a gyara masa kafafunsa su kamar yadda duke a da." Shirun da ya sake ratsa ɗakin mai tsawo ne da babu abinda zaka tsinta a ciki kafin Hajiya Kilishi ta kai ƙarshen zancenta da magana ta karshe kuma mafi girman da daki zuciyar Amina babu zato, maganar da daga ita har Amma basu taba hango ta ba balle tasa ta a jerin tunanin Hajiya Kilishin, kuma duk da dauriyar da take da ita a lokacin sai da kalaman suka tasa allon kirjinta girgizawa da karfin da ta san har Mamin ta lura. "Maganin dake gefe kuma naki ne Amina, ki dauka ki dinga shansa kullum, na san ba zan iya hana Ma'aruf kula ki ba idan har yayi niyya, amma kuma ba zan lazimci wani abu ciki ba don babu shi ko kadan a cikin lissafina!" *** Yaya kuka ga sharaɗan farko na Kilishi?? Ta yaya kuke ganin Amina zata bullo musu??😅😅 Ta yaya zata sa komai ya faru ba tare da Hajiya Kilishi ta ɗorar da zargin da take mata ba?? Mu dai jira hukuncin Amma ko?? And the Uban gaiyar is over there going crazy akan ƙafafun Amina ba tare da ya san me ke shirin tunkaro shi ba!😅 Wani ya gaya masa cewa su Rukayya ma na can nayi masa nasu shirin suma... Jawad ma kuma yana nasa! A tsakiyar komai kuma dai, zamu samawa Ma'aruf wannan nutsuwar da yake nema insha Allah.😍😍 #Aysha shafi'ee. #fikrawriters #FararWuta. SANARWA. ~~~~~~ Assalamu alaikum. Fatan alkhairi ga tarin Masoyan FARAR WUTA da ma duk wani littafi da ya kasance nawa. A lokaci irin wannan nakan nemi kalamai in rasa, nagode da dukkan support ɗin ku tun daga shafin farko na farar wuta zuwa in da na tsaya. Ina kuma ganin tarin saƙonni da ƙorafin ku akan rashin samun update akan lokaci, ina jin kalmar HAKURI kamar tayi kaɗan, amman ita kaɗai nake da ita. Na fara littafin nan ne ba tare da na hango tarin uzururrukan da suka dinga taso mun ba, suka kuma zama dalilin rashin samun update ɗin da ba kwayi. Na sani... Na kuma fahimta tun kafin ku furta. Kuyi HAƘURI, don saboda dalilai da yawa littafi na biyu (Farar Wuta 2) zai koma Paid Story cikin tsarin da nake fatan dukan mu zamu ji daɗin shi. Wanda na ɓatawa a farkon tafiyar nan zuwa yanzun, banda kalamai masu yawa sai neman afuwa da kuma bada hakuri. Allah ya tabbatar mana da alkhairi ya kuma bamu aron lokacin sake haduwa dan karasa tafiyar FARAR WUTA. Kar ku manta yanzu tafiyar ta fara... Zan baku labarin yadda nasara ke samuwa babu boka ba Malam! Zan baku labarin soyayyar Ma'aruf da wataƙila zata narkar da zuciyarku kamar ruwa. Zan kuma baku labarin yadda mata ke samawa kansu mafita ta hanyar wayo da dabarar da Allah ubangiji ya halitta a ƙwaƙwalwar kowacce mace. Ku tuntube ni ta wannan lambar. 08067794315. Nagode muku fiye da yadda baki zai iya furtawa. #AyshaShafi'ee #fikrawriters #FararWuta.

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73