Chapter 38
Chapter 38
ma da Aunty Ma'u ta fara sai taji kukan da ta sha ɗazu ya sake dawo mata sabo. Fatima ta taho ta rungume ta daga tsaye tana gaya mata abinda kowa ke faɗa, cewa tayi haƙuri, kuma sai su Ummi ma suka karaso suna tayaa ta, tanajin yadda kukan bata ke jijijiga jikinsu kafin Aunty Safiyya tasa su suyi gaba. "Wannan shine dakin da muka kawo miki kaya, watakila zaki ga sauran biyun dake gefe sun fi shi kyau, amma kiyi zamanki a cikinsa Amina, don shine mutuncinki." Aunty Safiyya ta raɗa mata a kunne lokacin da kowa ke mata sallama, kuma tana ji tana gani dukkaninsu suka tafi, tayi niyyar tasowa suje ko wajen kofa ne amma mamansu Ummi ta hana, tace tayi zamanta kawai. Ta dade a zaune tana kallon hannyenta bayan tafiyar tasu, ji take yi kamar an saka ta a wani jikin ne da ba nata ba, an ce komai nisan jifa kasa zai faɗo, ta yarda da auren nan kamar wasa, zuciyarta na hango mata shi a can nesa sai gashi tun ba'a je koina ba har anyi an gama, kowa ya taka rawarsa ya matsa, an bar mata filin da tace zata iya yakin a cikinsa. Kamar wani yana kallonta da kyar ta ɗago idanunta tana karewa dakin kallo, kayan cikinsa dama ta riga ta sansu, har gadon a waya Aminu ta nuna mata don tare suka je shi da Baban wajen masu kayan katakon, labulen kuma duk a tsakar gidansu akayi ta dagawa ranar da su Aunty Safiyya suka siyo daga kasuwa, carpet din da aka shimfida a kasan gadon ma, a ɗakinsu aka jingine shi. Don haka ginin gidan da shine baƙo a wajenta take kallo, ɗakin kato ne yasha fenti da kuma tsarin fitulun da ba sai an gaya mata ba ta san masu tsada ne. Ta tuno yadda taji su Ummi nata yabon sauran bangaren gidan, ba shiri taji wani abu ya wuce ta makogwaronta, kowa ya sani cewar akwai dalilan da suka kawo ta wannan gidan, ba'a banza kamar ita zata sami irin wannan wajen ba, kowa ya sani cewa akwai wani abu daban a tare da auren nan, kawai kowa yayi shirun ne yana jiran ganin abinda zai biyo baya. Tafi minti goma tana tunane-tunanen abinda zai iya faruwa da kuma mafita kala-kala, amma duk abinda ta kamo sai ya suɓuce idan ta tuna cewar a yau zata yi ido biyu da mutumin da aka daura mata aure dashi, mutumin da ya riga yayi mata gargadin cewa kar ta yarda ta aure shi, zuciyarta ta sake matsewa kamar zata fashe zuwa wasu dubunnan ƙananan atoms. Da kyar ta cillar da komai a cikin kanta ta miƙe ta nufi toilet din dake manne a dakin, kuma sai da numfashinta ya tsaya sanda idonta ya kalli ciki, toilet ne da yasha adon wasu baƙaƙen marbles masu kyalli da santsi, anyi wasu hadaddun drawers a ciki da wani bakin katako da ya dace da kalar marbles din, ta ja numfashi a hankali sannan tayi addu'a ta taka kafarta ciki a hankali tana jin sanyinsa na ratsa ta. A gaban katon mudubin ciki ta tsaya tana kallon yadda idanunta suka yi ja dama yadda fuskarta ta dan kumbura, sai kawai ta bude fanfon kasan sa tayi alwalarta, ta haɗa da wanke wuyanta dama rabin bayanta, kuma dadin ruwan yasa wata zuciyar tace mata taje ta ɗauko sabulu a akwatin cosmetics ɗin nan tayi wanka gabaɗaya amma ta girgiza kanta. Ba yau ba, ba yanzu ba. A akwatin undies ɗin nan da Maryam tace ta dauko hijabinta guda daya, ta dawo kan carpet din dakin tayi sallah raka'a biyu, bayan ta idar ta dago da hannayenta da niyyar addu'a amma sai ta rasa ma me zata roƙa, saboda haka sai kawai ta dunƙule jikinta waje ɗaya ta ɗora kanta daga gefen gadon tayi shiru. Shirun da a cikinsa taji lokacin da aka buɗe kofar dakin. ** Karfe sha ɗaya daidai ta iso da Ma'aruf ƙofar gidan, ginin ya tsaya a gabansa kamar wani tsauni, babu wanda zai ce ma a cikin gidansu aka fitar dashi, don gate dinsa yayi gefe da yawa ta daya bangaren. Ya lashe lebbensa na kasa daya bushe yana gayawa zuciyarsa cewa sun zo matakin da suke jira, sakon ya isa kuma maimakon ya dawo cike da kwarin gwiwa sai ya dawo da wani raunin da kalaman da Ishaq ya gaya masa a dazu suka yi sanadiyarsa. "Ka sani cewa wannan ba labari bane Ma'aruf, ba labari ne da zaka rubuta a yadda kake so kuma har ka kai ƙarshe da son zuciyarka ba. Na fahimci dukkan abinda ka faɗa da kuma dalilin da yasa ka dawo ka yarda da auren, amma hakan baya yana nufin cewa ka tsallakewa abinda zai iya faruwa ne. Kar ka manta a baya ciwonka ko matakin HypoMania bai kai ba abubuwan da suka faru suka faru, yanzu kana stage na karshe Ma'aruf, kai da kanka kana tsoron wannan matakin, ba sai ka gaya min ba, a idanunka kawai nake gane cewar kaima kana tsoron faruwar wani abu kamar yadda kayi tunani a farko, tunda ni da kai mun sani cewa ba lallai ne mu iya binne komai ba a wannan karon..." Ya sake lashe leɓɓensa yana jin yadda har a yanzu tasirin kalaman ke yawo a cikin kansa, gargadi Ishaq ɗin yake yi masa ya sani, gargadin da shima ya riga yayi wa kansa duk da cewa bai tsara komai game da auren ba bayan cewar yana son samun bayanansa daga yarinyar, zai tafi da abinda lokaci ya bashi ne kawai yana kuma ƙoƙarin kiyayewa dukkan abinda gaban zata haifar, haka ya gayawa Ishaq, ya kara gaya masa cewar shi yanzu abubuwan dake gavansa ma Allah yayi yawa dasu, sai yaga komai ya lafa masa tukunna ma zai maida hankali kan yarinyar. Ta cikin glass ɗin motar ya hango ƙofar gate ɗin shiga wajen su Mami dake can gefe, babu kowa a wajen alamun da gaske dare yayi don ya sani cewar an sha hidimar mutane tunda yau ne rana ta karshe a bikin. Wayarsa ya jawo ya kira Mamin, bugu daya biyu, kuwa ta dauka tunda dama jiran isowar tasa take, har a hanya ta kira shi taji idan ya taho. "Ma'aruf..." Muryarta dake shaida dimbin gajiya ta kira shi da sunansa. "Mami na iso amma ba zan shigo ciki ba." Sai da ta ɗanyi shiru kafin muryarta tace. "Kai da mutane ne?" Ya girgiza kansa. "Ko Ishaq ma nace yayi zaman sa kawai. I'm alone." "Tohm shikenan da safe na ganka, dama bana son kayi dare sosai baka iso bane, don tun wajen Isha'i suka ƙawo ta, anyi muku addu'o'i masu tarin yawa, hatta ƴan uwan Hajiya Maimuna da basu so abin da farko ba sun yaba sosai da ita da kuma ƴanuwanta Ma'aruf, Ina fatan Allah ya sanya dukkan alkhairinsa a zaman da zaku yi, Allah ya baka ikon sauke sabon nauyin da ya hau kanka." Bai san lokacin da ya haɗiye wani abu a makogwaron sa ba kafin ya amsa a hankali, don ji yayi kamar itama tana tuna masa da abinda Ishaq ya faɗa ne. "Insha Allah Mami. Nagode." Yaji kamar ta gyada kanta kafin ta sake cewa.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73