Skip to content

Chapter 47

Chapter 47

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

kan kapet ɗin gaban abincin ya zauna, ƙamshint turarenta mai sanyi ya shiga hancinsa tare da na abincin don a yadda ya zauna tray ɗin shi kaɗai ya raba tsakaninsu. Kuma bai ce mata komai ba, yana kallonta ta zuba iya adadin da take so na komai sannan ta ture tray din gefe a hankali ya tafi cikin laushin carpet din kafin ta ajiye plate din a gabansa. Shinkafa ce fara da vegetables a ciki sai kuma miyar dake tashin ƙamshin daya baɗe falon a lokaci guda, akwai wani abu a dan bowl data zuba na cabbage da kuma Irish potato mai hade da nama duk da wanda yake cikin miyar. Wani abu ya motsa a cikin zuciyarsa cike da yabawa kokarinta dama abincin tun kafin ya kai bakinsa, yana tuna masa da wani al'amari daya shuɗe a labarin aurensa na farko, ba kai tsaye ya samu irin wannan gatan ba. "Thank you so much." Muryarsa ta furta a hankali da wani sauti da yasa numfashin Amina katsewa a kirjinta, ba shiri ta gyada kanta sannan ta mike da sauri. "Ina zaki je?" Shima yayi tambayar kamar kai tsaye bai shirya mata ba. "Zanje in kawo ruwa ne." Muryarta ta fito tana fallasa bugun da zuciyarta ke yi, kuma kafafunta basu motsa ba sai da ya ɗaga mata kansa. Ta isa kitchen din ta ɗauko robar ruwa guda ɗaya da ba'a fridge ba, don ta kula duk sanda zata ganshi da ruwa a hannunsa to ba mai sanyi bane, shi yasa lemon data haɗa ma ta kaishi can kasan fridge din baiyi sanyi sosai ba, Samirah ce ta koya mata hada lemon, kuma ta tabbatar tayi komai daidai, sai dai bata san dadinsa ko akasin sa ba tunda bata taba sha a wani waje ba. Ta isa falon lokacin da idonta ya sauka akansa ta baya ya kai lomar da bata san ta nawa bace cikin bakinsa, zuciyarta ta kara nutsewa cikin kirjinta da tsarin nata ya tafi daidai, a hankali kafafunta suka ƙarasa kan carpet din, tana jin yadda kafar tata ke shigewa cikinsa saboda laushin sabunta. Wannan karon nesa kaɗan dashi ta zauna sannan ta fara ƙoƙarin zuba lemon a kofi. Ma'aruf ya dago ya kalle ta, har yanzu mamakinta bai bar kan fuskarsa ba, kuma a lokaci guda yaji kalaman da Mamin ta taɓa gaya masa suna dawowa cikin kansa. ... Wannan ba irin ba irin Ruƙayya bace Ma'aruf, don nayi Imani yarinyar nan zata baka kulawar da kake buƙata. Abinda Mamin bata sani bane, ita kanta Rukayyan tayi iya kokarinta a zamansu, don ta canja abubuwa da yawa a rayuwarta zuwa bukatarsa, matsalar kawai shine don son zuciyarta tayi komai, babu abinda tayi saboda shi ko don ta kyautata masa, don haka itama zai iya yiwuwa ta fara hakan ne don an saka ta, don bin umarnin da ya tabbatar shi tayi har auren nasu ya kasance, yaji zuciyarsa ta matse da wannan tunanin amma kuma sai ya samu sauƙi da hasashen cewa haka ba zai iya zama gaskiya ba. Ta gama zuba lemon a wannan lokacin, ƙarar awarwaron dake hannunta ya janyo hankalinsa sanda take ajiyewa a gabansa daidai lokacin da wayarsa tayi kara daga kan kujerar nan, don haka tayi amfani da damar don miƙewa ta bashi waje amma sai muryarta ta tsaida ta. "Ki zauna." Fuskarsa fayau yana kallonta kafin ya juya ya dauki wayar. Ta haɗiye wani abu a makogwaronta a hankali sannan ta dawo da baya ta zauna ɗin, nesa kaɗan dashi kamar ɗazu. Ya ɗauki wayar yana magana ta ciki, ta fahimci da wani yake magana kuma akan harkar aikinsu ne bayan hakan bata gane komai ba, amma kuma yanayin yadda yake maganar ya saka taji zuciyarta na sakewa da amon muryar tasa. Ya gama wayar ya ajiye ta a gefensa sannan ga mamakinta taji yace. "Faruq ne, abokina ne a wajen aiki." Sai ta daga kanta lokacin da ya sake kai wata lomar bakinsa sannan yace. "Abincin nan yayi daɗi sosai Amina. Kinyi kokari." Wani abu ya matse a zuciyarta daga yadda muryarsa ta ambaci sunanta, kamar zata yi magana amma kuma sai ta sake gyada kanta kawai tana wasa da karshen mayafinta. Kuma Yanayinta yasa Ma'aruf yaji a lokaci guda yana son suyi hira, aƙalla yau maganar tasu ta tsallake babin gaisuwa saboda haka yana kallonta yace. "Munaya ta gaya min kina son karatu, tace ta samu wasu novels a wajenki. kina da litattafai da yawa." Sai da sakanni biyu suka wuce sannan Amina ta yarda da maganar da ya furta saboda ɗan mamakin da ya kamata, ranar da take kokarin samawa litattafanta waje ne Munayan ta shigo ta ganta, a ciki har da wasu English novels dama na Hausa wanda take tarawa tun tana makaranta, shikenan sai suka shafe kusan rabin yinin suna hirar labarai kala-kala har ta ara mata wasu ma ta tafi dasu, don haka ta tabbata a yanzun ma ganinta yayi tana karatun ɗaya daga cikin wanda ta ɗauka. "Wanne da wanne kika karanta?" Muryarsa tana fitowa ne kamar yadda take jinta a kullum idan yana waya ko kuma da wani, amma a yanzu da ta san cewa ita yake wa magana sai take ji ta daban, tana saka ta ƴar rikicewar da bata shirya ba. A hankali ta daurewa hakan muryarta ta shiga jero masa sunayen littattafan da ta san sunyi suna amma da yawansu yace bai san su ba saboda yawanci akan Romance ne shi kuma yace ma yafi karanta Non-fiction, yana yi yana cin abincin cike da wani abu da zata iya kira da nishadi. "Akwai wani 'The Life we had' na san zaki san shi.'" Ta ɗaga kanta da sauri don ji tayi kamar hakan na kaɗe tasirin da muryarsa ke yi a zuciyarta, kuma a lokaci guda bakinta ya ɓalle da wani murmushin da bata shirya masa ba tana tuno yadda akayi ta karanta littafin a wani shagon bakin titin unguwarsu inda ake sayar da shi, zuwanta shagon nan bakwai kafin ta kai karshen littafin saboda yayi mata tsadar da ba zata iya siya ba, kuma wata ƙawarta da suka yi makaranta ɗaya da yawanci litattafan wajenta ma ita ta bata, itace ta dame ta zancensa, bayan sun bar makaranta ne a lokacin ita tana can Bauchi babu ta yadda zasu iya haɗuwa sai dai ta kira ta a waya tayi bata labarinsa. Tana tuna ranar da ta kai ƙarshen labarin da wani a cikin masu tsaron shagon ya gane ya tada ballin sai ta biya, da taimakon Aminu aka rufe case ɗin. Bata sani ba ko shima murmushi yayi don kanta yana sunkuye amma taji muryarsa ta ɗan canja lokacin da yace. "Ke ma kamar su Munaya ce ashe, ban san me marubucin littafin yayi da ya siye zuciyarku da yawa ba, babu wani abu da yake gaskiya a labarin nan." Amina bata san sanda ta ɗago ta kalle shi ba tana girgiza kai, tace. "Ai dama Fiction ya gaji ƙirƙire-ƙirƙire da yawa, shi yasa ya kirkiro komai ɗin don ya fito da ma'anar labarin sosai." Ya girgiza kansa shima. "Saboda kawai ya karya zuciyar mutane ne, shi yasa ma ya kashe su daga karshe, daga lokacin da na fahimci itama yarinyar mutuwa zata yi, na tsayar dashi

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73