Chapter 9
Chapter 9
na dare Yana kallonta,tashi yayi ya fice zuwa gidan Abokinsa a can yaci ya koshi,tsakanin Aisha da Farooq an rasa waye me gaskiya tsakaninsu idan wannan yayi rashin mutunci gobe wannan ne zaiyi kullum basa shiri abinda ya damu Farooq irin gorin haihuwar da Aisha take Masa kullum,kwana biyu Babar Aisha tazo gidan suna dakin Aisha Babarta tace ke dai anyi shashasha mene amfanin aurenki da Farooq mutumin da baya haihuwa kunje asibiti yafi a irga ance a shine ai ya kamata kisa ya sakeki,ribar aure ai haihuwa ce tun wuri kisan me kike ciki,Babar Aisha haka ta gama zuga yarta daga ranar Aisha ta daina girki Farooq Yana Mata magana sai masifa tace juya Wanda baya haihuwa ka sakeni tun baya damuwa har abin ya dameshi ya sanar da Babarsa tace yayi hakuri Kawai kowa haka yake hakuri,da a baya suna yin Dan fadansu su shirya haka Yar karyar su dai sukeyi yanzu duk Aisha ta canja ba mutunci Kawai a sake ta taje ta samu me haihuwa. Affan ne ya fito yasha wata shadda fara yayi mugun kyau Yana kamshi Raudat itama ta fito cikin farin lace zata tafi wajen aiki Kawai taga Affan da fararen kaya Ido suka hada tace Allah ya kiyaye na saka Kaya kala daya da Kai God for bid ta juya cikin fushi ta canja wata blue atamfa ta fito Yana tsaye da mamaki Tsaki yaja ya juya zai fita tace masu appointment kullum Ina da appointment kullum meeting ba uwar komai a kasa ba Sisi,kallon baki Isa ba ya Mata yace Banda lokacinki ya Bude karamar kofar gate ya fice,ita Kuma ta bude gate ta fita da motarta yace arga akwarabas da na Shiga wannan motar gwara na tafi a kafa,Tsaki ta ja tare da Shiga motarta tazo ta gabansa Malam bani hanya gurgu kawai masu mota suke da kafa ta daga glass din motarta sama tayi gaba. Yau kwanan su Charity goma Sha biyu da bacewa Mama ta rame ta lalace ga bakin cikin Shehu ga bacin rai yarta ta bace Addua kullum suke ba dare ba rana,Bangaren Charity Kuwa Matar kanin Babanta wacce take Kira da Anty cewa tayi ban yarda ba Dauda yarka karuwanci ta tafi Siyama duniya Kawai ta shiga,nima Ina zargin haka cewar Dauda, Su Nusaiba kuwa sunfi sati daya basu ga ko alamar Oga ba sunci kukan har sun gaji,me aikin ma da suke gani yau ta tafi ganin gida sai nan da kwana biyu zata dawo sai ranar Suka ga Oga ya fito daga dakinsa ya musu murmushinsa me kayatarwa yace Hey,suka kalle shi Kawai yace me aiki yau ta tafi kuyi hakuri sai jibi sai ku tafi idan Kun tafi babu me gyara min gida ni Kuma bana son kazanta Dan Allah ku gyara gidan nan ya juya tare da komawa sama,ba yanda Suka iya Haka suka hau gyara ko Ina na gidan Bayansu ciwo suna gyara garden Nusaiba ta rike bayanta tana Nishi tace gwara tallan kosai na sau dubu da irin wannan aikin, Charity tace hmm ai nayi missing tallan Alala ashe haka talla yake da sauki kana zaune za a Zo a siya,tun ba ma an soya ba kafin ka tafi tallan sai kaci ka koshi cewar Nusaiba itama Ai sai ma Ina zubawa mutane Ina daga zaune abina da yajina a gefe,daina tuna min cewar Charity suka ci gaba da uban aikin gidan Ku dinga sharhi please novel zai Fara wuta nan gaba AsmaBaffa [4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️ 21-25 Official By AsmaBaffa Page naki ne MRS CHIEF Biki Saura kwana uku Charity taga ba a sata a harkar itama bata Shiga ba uzurinta take yi,ana gobe daurin aure Nusaiba tazo gidan su Charity tace kinki zuwa ana ta shagali ba ke,Charity tace kice ana ta soya kwankwason rago,wa yake ta wani rago ana fada Miki kwankwason bijimin sa,dariya tayi ta shirya tare da yiwa Aunty sallama suka tafi,leshin da Nusaiba ta sa aka dinkama Charity ta Bata tace gashi shi Zaki sa da safe ni na Kai Miki dinki me tsada aka Miki, Charity ta ajiye Kaya a gefe Nusaiba tace an fa goge su ki Adana Kaya masu tsada ne fa sai ana kula,Charity tace hmm kawai,Nusaiba tace Ni tsoro ma nake ji Kar ki fini kyau ranar bikin yanda kike farar nan kyakyawa Ni Kuwa wankan tarwada da ma nice ke Charity,Siyama tayi dariya Nusaiba ta sake cewa ji dimple dinki sis gaskiya ki godewa Allah ya Miki baiwa,Siyama tace kema ai kyakyawa ce Nusaiba hancinki ai yafi nawa tsayi,Ni ba Fara ba Yaushe ma na Kama kafarki,sai gashi a hakan me kudin ke yace Yana so ba farar ba ko ta nan ai Kya godewa Allah ni da kin sani ma dinkin Riga da wando Kika min ban iya sa Riga da skert ko da zani ba kin sani,Baki Isa ba bikina guda ki sa Riga da wando bazai yuwu ba shegen duwawunki su ja hankalin mijina,Siyama tace da Zan ja hankalinsa ai da tuni ya gani ki daina kishi dani wlh sister bazan taba cutarki ba,Nan ta kalli Lefe akwati kusan ashirin aka kawowa Nusaiba. A gidan charity ta kwana duk wani aiki da ita akeyi tana gaba gaba ranar daurin aure 11am za a daura su Charity an Sha kyau tafi amaryar kyau duk da cewa Amarya me makeup tazo ta Mata nan take Nusaiba ta bata rai ganin Charity tayi kyau cikin Riga da skert din less kawayensu duk sunci kwalliya sun Zo Basu sa anko ba Basu da kudin siya,Ango da best friend dinsa Sabeer sun gayyaci abokai Nan da nan masallacin kusa da gidan ya cika da mutane ko Ina Yan gayu ne da manyan masu kudi lokaci na Yi aka daura auren Aslam Mu'az da Amarya Nusaiba Usman,kowa yayi mamakin Wai Aslam ne zai auro mace Yar talakawa haka Basu shigo gidan ba Suka wuce reception kowa a can yaci ya sha daga nan abokai suka wuce gidan da suke angwanci. Nusaiba haka aka yini ana hada hada sai 5pm duk Suka yi wanka aka Fara Shirin Kai Amarya,Shehu yasa yarsa a daki ya dinga Mata Nasiha yace ki zauna lafiya da mijinki Nusaiba Allah ya Miki zabi,ki rike mijinki da Yan Uwansa babu batun Maganar son kudi a cikin aure idan ka auri mace ko mace tayi aureka baka fata ku rabu sannan zaka tsaya ka jure samunsa da rashinsa ki Zama mace me tunani ke ba yarinya bace kin girma kin wuce shekara ashirin ki San me kike, Mahaifiyarki Aminatu kin San mu Yan asalin Rogo ne dake nan Kano,sanda na ganta Ina sonta Ina da kudi lokacin kasuwanci Yana gara min na aureta Bayan na aureta na hadu da karayar arziki daga lokacin Mamanku ta dinga wulakantani tana ci min mutunci sabo da bani da kwandala,bayan wasu shekaru Allah yasa kudina ya dawo daga nan Kuma kauna ta dawo ta dinga nuna min so Sabo da kudina shi yasa Kika ga na fita safgarta gaba Daya ba karamin wulakantani tayi ba lokacin da Banda shi to karki haka Nusaiba ki zauna lafiya a nan dai yayi ta Mata fada ita Kuwa Mama ance ga Amarya ko Zaki Mata fada,Mama tace mu yaranmu ai tun suna
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71