Skip to content

Chapter 5

Chapter 5

AURENMU Book One Complete Hausa Novel 1,249 words 0 views Progress saved
Download Book

farko ma fa da tuni Yar kwallon kafa ce Ni,lokacin da Kanu yayi tashen cin ball ba shi ya kamata yaci wannan ball din ba lokacin Atalanta cup nice ya kamata,ana wani zancen Ronaldo wani Messi dan ba a Sanni bane na iya ball amma makiya sun hana naci gaba,Ina da makiya da yawa shi yasa,Aslam Yana ta dariya a ransa,yace to me Kika iya dafawa a ciki? Na iya Alala,tuwo,danwake ga sarkin Dadi shinkafa da Miya duk na iya,Yace hmm duk ni bana cinsu me yasa kike sa kananan Kaya kina Yar musulma bahaushiya? Sabo da na nuna musu Ni ba sa'ar Mata bace mace ce ni me kamar maza kwari ne Babu,Ni Yar jam'iyar what man can do Woman can do better ce,to Kuma kina da saurayi? Charity tsaiwarta ta gyara ta Fara zuba Murmushi tace haba Ina da shi har da Ridwan a cikinsu yaudararsu Kawai nakeyi Ina cin kudinsu,Rannan Ridwan din ma yazo daga karbar kudin ankonsa shike nan ya rungumeni zo kaga kiss hmm kamar maye ni kuwa na ci masa mutunci nace babarsa me tsatsar hakora,Aslam dai Jin labari Kawai yake ratata tun a nan yace Charity bata kirki bace, Nusaiba ce ta fito ta dakawa Charity tsawa tace Charity kiji tsoron Allah Ridwan din baki taba sauraronsa ba yaushe ma a masifarki Zaki Bari ya Miki kiss Naga rannan Abdulhadi daga yace ki rungume shi Kika fasa Masa Kai da dutse, Enough kuje kuyi girki cewar Aslam,komai na Kitchen din kasa amfani sukayi da shi sai siyo musu abinci yayi,washe Gari suka dinga kuka tafiya zasu Yi yace to ba damuwa yasa Driver yace ya kaisu Tasha Kuma ya tabbatar sun Shiga mota,ya mikawa driver kudin motarsu sannan ya Basu dubu ashirin ashirin kowacce,da sauri Nusaiba suka Shiga motar,suna tafiya aka zo saitin layinsu Nusaiba tace nan zamu sauka,a sauke mu a nan,driver yace ai oga yace dolene a saku a motar Taraba Kar a samu matsala su Charity suna ji suna gani aka wuce layinsu har zuwa tasha aka sasu a mota tare da biyan kudin,sai da suka tabbatar driver ya tafi suka fito daga mota suka ce sunyi mantuwa ko tsayawa karbar kudin motar Basu Yi ba Suka Shiga Napep zuwa wani gidan amarya kawarsu ce Suka bata ajiyar kudinsu sannan Suka tafi layinsu Kafin su karasa gida lungun da ba mutane suka tsaya Suka sallami me Napep suka shafawa jikinsu toka har gashinsu hular Charity ta cire ta wullata cikin wani gida itama Nusaiba ta jefa dankwalinta gashi sun samo toka wajen masu girki a tasha sun shafe jikinsu tare da shafa bakin gawayi a hannayensu da kafafun su cikin katuwar bolar dake layinsu suka Shiga tare da tsugunawa a ciki kamar birarrika,kowa ya wuce ana cewa Allah sarki ga wasu can mahaukata kalli Yan Mata dasu Allah ya Basu lafiya,ana ta musu addua har Yamma likis sai ga Ameer kanin Nusaiba zai wuce suka ki magana har ya wuce sai da ya wuce Charity a hankali ta daga hannu Ameer gamu nan karya muke,Nusaiba ce ta bige Mata baki suka Yi Shuru,har Yan unguwa suka gaji aka nemo Yan sanda da me unguwar layin aka je inda su Charity suke dukun dukun suna soshe soshen karya,me unguwa yace a fara bincike ko a Nan akwai Wanda ya sansu,Shehu yazo wajen Yaga yarsa Nusaiba da kawarta Siyama,Shehu yace Wannan ai Yata ce data bace da kawarta Yar gidan Dauda,mutane aka dauki Salati Shehu yace Wanda Suka sace su ko me ya faru oho Nusaiba da Charity sunki magana ba uhmm Babu Uhmmm Uhmm Dan Kar ma a musu fada a gida,Yan Sanda Suka ce sai dai Wanda Suka sace su ne Suka musu tsafin da baza suyi magana da wuri ba,Shehu yace tunda Sun fito Alhmdllh kaga aikin Addua ko sun sace su amma Addua tayi tasiri sun kasa yanka su ko tsafi da su Addua kenan ai ba karamin kudi na kashe ba Sadaka masallatai Masallatai cewar Shehu yaja Hannun Nusaiba suka tafi gida Charity ta faki idon Shehu ta radawa Nusaiba Kar muyi magana sai gobe,Mama harda ihu sabo da murnar ganin yarta karshe ta fashe da kukan farinciki tana oh ashe Zan sake ganinki Nusaibata,Shehu yace basa magana yanzu amma kafin mutane su Fara shigowa suyi wanka Bari naje na Kira Dauda ya fita cikin Sauri,Su Ihsan Suka dinga ihu suna fada a unguwar anga su Nusaiba a bola aka tsince su. Mama ruwan wanka ta hadawa ko wacce Suka shiga kowacce ta wanke toka da bakin gawayin da Suka shafawa kansu sai gasu fes ba alamar wahala a jikinsu duk sunyi wani kiba ma fatarsu ta murje amma sunki magana juyin duniya sunki magana a Haka Shehu ya siyo musu shinkafa da wake da Miya Wai sun Sha wahala hannun Yan mafiya bari a basu me dadi,suna Fara ci Anty tazo tare da Dauda Suka zauna a tsakar gida Nusaiba da Charity suna ciki suna cin abinci,ganin ba kowa kasa kasa Charity tace ba dadi abincin na Saba dana gidan Oga,Nusaiba tace ji kazar da aka sa Mana jiya a cikin shinkafa,Charity tace habawa ai sai lemon shekaran jiya ga sanyi ga dadi yanzu shike nan mun dawo cin gafza Kuma ga wanka da ruwan botiki can a shower Muka saba,ta kalli gidan su Nusaiba tace Kai Kan uba kalli gidanku dama haka yake duk dirty painti ma ba a Gane wanne kala ne,dariya sukayi yanda baza aji ba Nusaiba tace Nima sai yanzu na kula gashi mun dawo kwanciyar Kai da kafa gobe da sassafe sai tallan kosai,Charity tace idan Muna so mu huta da talla gobe zuwa jibi Kar mu sake muyi magana hauka muke cewar Nusaiba Suka sake Yin Shuru abinsu. Juyin duniya sunki magana haka bayan sunci abinci Dauda da Aunty Suka tafi gida da Charity,washe gari ma basuyi magana ba a Rana ta uku Charity sai ta Fara magana tace Aunty daga nan bata sake magana ba,Aunty tace Dauda yarka ta Fara magana Alhmdllh wlh yanzu tace Aunty ta Kira sunana,Dauda yazo kusa da Charity yace Siyama me Kika ce kinyi magana dazu Nima Kira sunana ba sai kince Baba ba ko Dauda Kika Kira ba matsala ai duk cikin lalura ne, Charity a ranta tace dama haka nake so wlh sai na more sunanka tace Dauda,Dauda ya kyalkyale da dariya Alhmdllh Nima ta Fadi sunana asiri ya fara sakinta, Charity ta sake cewa Dauda Iliyasu,Dauda ya sake shekewa da dariya yace haka ake kirana da a makaranta, Charity Kuwa a ranta dadi take ji dama ta gaji da kiransa Baba,yace Fadi sunan Auntynki Fadi muji, Charity tace Hajara Musa Aunty tace to hankalinta ya fara dawowa jikinta,daga Nan Charity ta Fara magana sai me ma'ana wacce ta Zama dole sai tayi magana a Haka a haka ta dawo normal itama Nusaiba haka ba Wanda ya Musu fada ko Daya da aka tambaye su ma Suka ce wani ne ya fesa musu wani Abu a Fuska Basu sake sanin inda suke ba sai a daji Suka tsinci kansu,Nusaiba tace yan Yankan Kai Suka ce a dawo da wannan matan sunfi karfin mu matan manya ne shike nan daga nan basu sake ganinsu ba sai a bolar unguwarsu,Mama tace Addua ce tayi

Table of Contents

Chapters

71 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71