Skip to content

Chapter 20

Chapter 20

AURENMU Book One Complete Hausa Novel 1,241 words 0 views Progress saved
Download Book

siya Mata,shi yasa tazo kano ta Kama gidan haya har Suka hadu da Affan suke fada Kuma kusan a tare Suka zo Kama gidan ta Sha Matukar wahala a hannun Hussain kafin Allah ya yanke mata. Affan Affan Kuwa asalin Fulanin Zamfara state ne, sunansa Aliyu A. Aliyu,mahaifinsu su biyu Maza ya Haifa Yusuf shine Babba an haife shi da shekaru hudu aka samu cikin Affan,da cikin Affan Allah yayiwa babansu Aliyu rasuwa,Babar su tana haihuwa aka sakawa Affan sunan Mahaifinsa wato Aliyu shine aka boye sunan ake kiransa da Affan, su biyu Suka taso a hannun mamansu a Zamfara duk da cewar babansu bai mutu ya bar wata kadara ba face wata gona layi biyu,bayan Yusuf da Affan sun gama secondary School babu kudin ci gaba da karatu,sai Mamansu ta siyar da gonakin nasu ta hada kudin kaf ta Kira Yusuf da Affan tace kunga kudin nan nasan bazai isheku kuyi karatu ba ku biyu Kuma ina so a cikinku wani yaje yayi degree a rayuwa ya kuke gani Kai Yusuf gadon ku ne idan Kuma kowa bazai iya barwa kowa ba to sai dai mu Kama sana'a da kudin,Yusuf ya kalli Affan yace gaskiya ni bazan iya barwa Affan kudina ba,Affan Kuwa Nan take yace Yaya Yusuf ni na hakura da karatun dama kaga nine karami na bar maka kudin gado na halak malak kaje kayi karatu idan ka samu aiki daga baya ka biya min ni nayi karatun daga baya ai ba'a girma da karatu,Yusuf yayi farin ciki sosai karshe aka Nemo admission lokacin baya wahala a ABU Zaria Yusuf ya shiga ya gama degree dinsa gashi Allah ya hadashi da Abokinsa Dan gidan me kudi ya ja shi cikin Harkar kasuwancinsu na siyar da gwala gwalai har aka zo ma ana tura Yusuf kasar waje yana siyo kayan, a hankali a hankali Yusuf ya Zama me kudin gaske ya kera katafaren gida a Kaduna gida na gani na fada,ko aikin gomnati ma bai nema ba,ya manta da halaccin da Affan ya Masa ya kasa tunawa ya sashi a university,karshe da yazo zamfara da galleliyar motarsa Wai yazo daukan Mamansu zai maida ta can Kaduna kusa da shi,Mama tace Yusuf Saura Affan Yana ta Zama ba karatu burina ka biyawa Affan shima yayi karatu ya shiga University yace to zaiyi cikin ikon Allah watan mamansu Uku kacal a gidan danta ta kamu da ciwon sugar farar daya ta rasu dake Affan shima Yana gidan Yusuf din tun asali Allah yayo shi da son Gayu da tsafta ga iya daukan wanka dama Kuma gasu kyawawan gaske. Bayan mamansu ta rasu da watanni Yusuf ya fara wulakanta Affan kamar ba gidan dan Uwansa ba,karshe Affan har ya gaji ya fara sana'a haka Kawai sai ya saro irin Guava ya dinga siyarwa Yana samun kudinsa baya kula kayan Yayansa,ya koma sarar irin su safa da handkerchief yana bin titin kwalta a hannu Yana siyarwa,ya dawo ya koma koma siyar da su charger a gefen titi da Haka ya samu ya shiga University amma shi BUK ya samu a Kano ya dawo Kano Hostel a school ranar da ba school ya tafi siyar da kayansa a gefen hanya,har ya hadu da wani babban mutum yace yazo ya dinga zauna Masa a shago a kasuwar kofar wanbai Harkar Yan robobi,ya koma can Yana fama a Haka ya kammala degree ga Yayansa can kullum arzikinsa Kara gaba yake amma sisi baya bawa Affan bai ma San Ina yake rayuwa ba,Affan wata yarinya ya samu Yar talakawa Suka Fara soyayya Nabeela,Yana mugun kaunarta Kamar ransa a Kaduna take Mamanta tana da ciwon zuciya kullum Affan akan taimaka musu yake duk abinda ya samo a wajen Maman budurwarsa yake karewa wajen nema Mata lafiya,Neman kudi yake Yana samu amma Maman budurwa kullum a asibiti can yake Kai kudin,magunguna shine ke siya, Basu da abincin ci shi zai siya musu a Haka jarinsa ya tarwatse babu ko sisi,Watarana Affan yaje zance Sabo da Nabeela ya koma Kaduna,ta rako shi gefen titi kenan Suka hadu da Yayansa Yusuf zai wuce a mota ya tsaya,Affan yace Yaya Suka gaisa ya nuna Masa Nabeela yace itace budurwata yace Nabeela ga yayana uwarmu Daya uban mu daya tace oh suka gaisa Yusuf sai kallonta yake gaba Daya Nabeela ta tafi da imaninsa,bayan Affan ya shiga Napep ya tafi sai ya dawo da motarsa ya Sha Gaban Nabeela yace ta shigo ya rage Mata hanya,Bata kawo komai ba ta shiga motarsa Suka tafi har gidansu har take fada Masa rashin lafiyar mamanta ya shiga gidan Suka gaisa tashi Daya ya basu dubu dari biyu,zuwa sati Yusuf ya koma gidan su Nabeela yace ta shirya zai fitar da mamanta kasar waje India nemo Mata lafiya Suka dinga murna Affan ma tuni Suka daina ta tasa idan yazo ma bata taba fada Masa Yayansa Yana zuwa ba ko dan kudi ya bata sai Taki karba tace Alhmdllh karka damu yanzu Allah ya hore mana, bata fada Masa zasu je India ba Kawai Yusuf ya musu visa da komai Suka je can ai Kuwa Maman ta warke ta samu lafiya Suka dawo garau da ita,Sabo da irin kudin da Yusuf ke kashe musu Yana cewa zai turo manya Suka ce ba matsala,ya turo da danginsa na zamfara Kuwa aka tsaida ranar aure, Affan Yana ta zuwa zance bai taba sani ba yaji dai Yayansa zaiyi aure,ranar data Kama daurin auren Nabeela da Yusuf sai Allah ya kawo Affan yazo zance da safe Dan lokacin ma a gidan wani Abokinsa yake zaune ai Kuwa ya iske abin mamaki Yayansa ya aure Masa budurwa har an daura aure ma ana ta hotuna,Nabeela ta fito Suka hada Ido da Affan ta fashe da kukan munafunci,Affan mutuwar tsaye yayi Kawai hawaye na tsiyaya a idanunsa tunda ya tabbatar Kawai ya juya ya bar gidan. Yusuf Yana ta Neman Affan yasan yayi laifi, Affan Kuwa yafi sati biyu Yana cutar so,Abokinsa sayyeed shine ke ta tausarsa har ya dan Fara hakuri ya Sha wahala ya rame sosai ya fita hayyacinsa Yana mugun kaunar Nabeela,lokacin Nabeela ma tuna abinda tayi na cin Amana ya hanata sukuni a gidan miji,Yusuf ya kasa Gane kanta dole ya Nemo Affan yazo har dakin Abokinsa ya samu Affan yace Affan sai dai fa kayi hakuri,na kashe kudi...Affan yace dakata Mallam ni kasan me na musu jarina kaf na karar bani da shi na iya taimakon su Kai Kuma kana da arziki idan kayi ma baka birge ba domin nasan da Kaine a halin da nake ciki na talauci baza ka iya sadaukar da arzikinka garesu ba,Indai akan macece kaje na hakura na bar maka har abada Kai jinina ne amma idan kayi da kyau ma ka sani idan ma baka Yi da kyau ba ka sani kanka Kuma Allah Yana kallonka,Suna haka Nabeela Katsam sai gata itama ta fito daga gidan auren nata tana cewa Dan Allah Affan ka yafe min,Affan ya kalleta yace bazan taba yafe Miki ba Nabeela kinfi Yusuf Laifi tunda da baki bashi kofa ba keda mamanki da Haka bata faru ba na tsaneki a rayuwata nayi nadamar saninki a rayuwata mayaudariya makaryaciya suna kallo ya hada kayansa ya dakko kudinsa da ya Dade Yana tarawa a asusu ya fice

Table of Contents

Chapters

71 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71