Skip to content

Chapter 60

Chapter 60

AURENMU Book One Complete Hausa Novel 1,256 words 0 views Progress saved
Download Book

kalli kitso Kamar Kan mace,Aslam yace Surukarki ce tayi min tace tafi son kitso nafi Mata kyau,Mum duka ta durma Masa a gadon baya ya saki kara Yana shafa wajen yace da zafifa Mum,lallai a tsefe kitson nan yau yau,dama dazu tayi shi da safe idan Zan fita pcap nake sawa,Mum tace ya muku kyau,yaushe zaku tafi ne ku? Yace sai next week akwai abinda Zan karasa,tace to shike nan Allah ya nuna mana,tace Ina Siyaman ne? Yace Wai kunya take ji,kirata Mana mene abin kunya yarinya taki sakewa dani,a waya ya kira Siyama tana dagawa yace kizo inji Mum,Fitowa tayi Aslam Yana kokarin jawo hannunta tayi maza ta matsa bangaren Mum tare da Zama a kasa Mum tana sama,Mum tace ki zauna a kujerar Mana Siyama ai an Zama daya ki daina wani kunya Nima na Zama mamanki ai tashi ki zauna kema,Siyama sai lokacin ta samu kujerarta daban ta zauna,Aslam sai kashe Mata Ido daya yake ta dauke kallonta daga garesa,Suna ta hira da Mum kadan kadan take saka musu baki,Mum bata dade ba tace tafiya zata yi driver da ya kawota shine ya maida Mum,Yana dawowa daga rakiyar Mum ya Mika hannu zai Kama Siyama sabo da ta Harare shi dazu,zillewa tayi tana dariya,wayo ya Mata kamar ya fasa kamata yace kawo min lemo,taje ta kawo Yana kwance a 3seater tana Miko Masa ya hada da hannunta ya rike,Lemon ya ajiye a gefe ya jawota jikinsa,tana shagwaba tace dan Allah ban dade da yin wanka ba yau tunda ka yini a gida sai wanka kake sani wankana sau uku kenan,tana zamewa zata gudu ya Mata rikon tsauri ya Kama bakinta Yana tsotsa sosai tare da murzata bata Sanda ma ta biye Masa ba ta shiga tayashi daga nan Suka lula duniyar ma'aurata cike da so da kauna. Nusaiba ce zaune a gida ta zuba tagumi gabanta tuwon masara ne miyar kuka da rana tsaka domin kudin abincin da Shehu ya bawa Mama na cefane ta kwashe ta kashe wasu Kuma tayi zubin adashi sai wahala yaransa suke sha,Mama ce ta kalli Nusaiba ta tabe baki tace idan Zaki ci ma kici wa ya hanaki duk inda Kika Yi aure ki bari ki haihu ai da yanzu kina da yaro da Aslam ko Sufyan a ciki dole Wanda Kika Haihu da shi ya dinga kawo Miki kudi na ciyar da dansa amma Kika ki yarda da shawarata ke baza ki haihu ba sabo da idan wannan ya talauce ki kashe aure ki auri wani ke baza ki tsufa ba Kika dinga Shan kwayoyin hana daukan ciki babu Wanda kika samu ciki da shi gashi nan ai kin koma marar amfani baki da wani amfani. Nusaiba ta kalli Mama tace yanzu Mama nice na koma marar amfani sabo da bani da kudi bana samo Miki kudi yanzu nice marar amfani sabo da kin gama cinye kudin Mazajen Dana aura? Mama tace ae baki da wani amfani an fada dan ubanki kuma idan ke Kika haifeni naji labari,amma wlh Mama Zaki gani Inshaallah Abba sai ya Miki kishiya Kuma Inshaallah sai an sake ki kema kiji in da dadi, ruwan mari Nusaiba taji ta ko Ina a fuskarta Mama tace dan ubanki sa'arki ce ni oh sabo da Ina Zama inyi zance dake shine Kika rainani,Nusaiba tace ae din na fada tana kuka tace wallahi Kuma ko Zaki kashe ni sai na fada Inshaallah sai an sakeki kema Kamar inda Kika kashe min aure Kika dorani a hanyar banza,Baki min tarbiyya ba baki ma cancanta ki Zama uwa ba ma,Mama ta mike ta rufe Nusaiba da duka ta ko Ina amma Nusaiba bata fasa fadar abinda taga dama ba. Affan kuwa Yana Office ya fara tunanen matarsa irin farin cikin da yake kwasa a wajenta tun kafin 5pm ya tattara sai gida,shi da yace sai 5pm Raudah tana kitchen sai ganinsa tayi ya shigo bayan ya Mata sallama ta amsa ya Rungume abarsa a jikinsa,Allah yasa ta gama kwai Kawai take dafawa shima ya dahu tana jira ne ta sauke ya shigo,Gas din ya kashe tare da Daukanta cak Kamar jaririya sai bedroom dinsa,burin Raudah ya cika ya dawo da wuri tace kasan me na tuna? Yace sai kin fada Yana ajiyeta saman gadonsa tana dariya kasa kasa tace fadan mu da kullum bamu da aiki sai fada Murmushi yayi yace sabo da yawan appointment dina ne,dariya Suka yi yace ai kin rainani da yawa ne,tace ai kuwa Watarana da na maka Tsaki ka mareni gaskiya na maru sai da na kwana kumatuna suna zafi tun daga ranar ban Kuma ba,me yasa Kika sa min Ido ne a lokacin? Maybe so ne,a'a ba wani so yanda Kika tsaneni,dariya suke yana shafa cikinta Yana Kare Mata kallo tayi kyau sosai sanye take cikin kana nan kaya wani dan short wando da Yar rigarsa yace halina da ke iya wanka kina birgeni ga tsafta ko Ina kamshi duk wani lungu da sako kamshi yake zubawa har can head of Service clean Yana kamshi tv dinsu dake kunne a bedroom din tana ta wakoki iri iri na Nija,Raudah tace Baby ka iya rawa? Yace rawa ban taba gwadawa ba a rayuwata ba wannan ba girma rawa sai Mata ai amma Namiji me class baya rawa bata cikin swag dina, Murmushi tayi tana shafa sajensa da gemunsa tace Yan gayu, Ido ya zuba Mata itama shi take kallo cike da shauki yace Allah sarki Hussain yayi asara,dariya tayi tace ba ruwana ni da ni na fada sai ka Fara Jin haushi kace Ina zancen tsohon mijina,yace ki daina cewa Hussain mutanen kirki su ake kira da Hussain amma shi Usaini yake su Usaini anyi asara,Raudah ta Masa Shuru sabo da tana magana zai ce tana Masa maganar wani,tashi ki kawo min milk before na fara servicing dinki,tace alright ta mike tana cewa kayi timbidi da yawa,dariya yayi yace dan Allah karki sa na tuno timbidin Yara me karni na kasa Shan madarar,Ni timbidin mazan aure nake nufi,lips dinsa ya lashe tace Allah ya shiryeka suna dariya yace ameen taje ta kawo Masa madarar tare suka shanye tace ka Dade kayi karko duk nasan ba rago bane,kissing dinta ya Fara Yana sarrafata Kamar zai cinye ta danya itama haka har Suka lula duniyar su ta Dadi. Aslam tunda Siyama ta samu ciki kullum Kansa Yana saman cikin tun cikin ma bai fito ba,ya dinga Tambayarta me take son ci,in Banda gyada me gishiri ba abinda take ci kullum sai abinci Wanda ya Zama dole tana ci ta koshi ga gyadarta a kusa,bayan Mum ta tafi da sati daya Aslam da Siyama Suka tattara Suka tafi yawon shakatawarsu kasashen duniya,Nusaiba sai labari ta ji,ta zauna tana ta faman bala'i ita Daya a tsakar gida tace Siyama baza ta taba ganin dai dai a rayuwarta ba,tsawa kwarantsa sai ta fado Mata a kai ta mutu kowa ya huta,shima Aslam sai ya talauce ya tsiyace da izinin Allah sai yayi bara a gefen kwalta sai yazo wajena ya nemi taimakon Naira hamsim,Mama tace Ameen Inshaallah basu babu ganin dai dai Siyama sai ta dawo tallan goro,Siyama tace Kuma baza ta taba haihuwa ba, Inshaallah cewar Mama bari zata dinga yi jini ya barkewa shegiya sai ta shekara tana

Table of Contents

Chapters

71 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71