Chapter 48
Chapter 48
maybe arowa ma yayi karya ne talakane har yanzu wai ni za a yiwa burga ta ja tsaki ta zauna tare da gallawa Siyama Harara,Siyama ko kallon Nusaiba bata Yi ba,ganin Nusaiba tana ta kallon Aslma tace please Ni ka canja mana joint muje Cenema kallon film yace alright ya riko hannunta yace sai abinda Kika ce ai shi za ayi Baby yaja hannunta Suka fita,Nusaiba tace karyar banza bibiyata sukeyi shi yasa Suka zo za a min burga ni Ina mamaki ma da har yanzu yake kamshi me dadi haka sutura me tsada ya kamata na Fara ganin wuyan rigarsa ya kode ya yage Yana wari amma kullum mutum kamshi Kamar namijin karuwa,harda aro mota azo za a rude ni Yan Iska Yan karya Yan Yan yan...ita Kuma Wai sa car key din a jakata sabo da naji suna da mota fake....ta ja tsaki,tashi tayi ta leka bata ga kowa ba motar da take tunani a ita Suka Zo bata ganta ba tace sun shiga taxi matsiyata Yan karya me motar ya dauki abarsa ta juya ciki. Siyama kuwa zasu shiga Cenema Kawai Aslam yaji sha'awa shi bazai iya jira ba,matarsa yake so ya murza,order ya musu na take away kaji da su ice cream da sauransu tana rike a hannunsa yace muje gida an fasa kallon Watarana sai mu zo bazan iya barin sabuwar Amaryata ta huta na hours ba ace bana taba komai ke muje bazan iya ba na fasa yaja hannunta Suka Shiga mota,Siyama tace mun fasa? Yace ae Nima ai ganganci nayi da na fito da Amaryata bazan yarda ba gaskiya wayo zaki min muje gida haka Kawai kowa idan yayi aure Yana hutawa ni shike nan na zauna a kallon film zaki min wayo,dariya ya bawa Siyama yace haka Kawai sai kalle min matata akeyi a banza... Masu sharhi Ina godiya AsmaBaffa [4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️ AUREN MU🛢️ 76-80 Official By AsmaBaffa Page naki ne AUTARESS Kofar gidan da Mum take yayi parking sai gasu ita da Hajiya Zainab sun dawo daga unguwa,Aslam Suka gani ya fito daga cikin hadaddiyar motar ya dakko Leda da flask,Mum tace daga Ina haka? ciki Suka shiga gaba Daya Yana cewa daga gida Mana,sai da Suka zauna a Palo ya gaishe su,ya ajiyewa Mum flask din da ledar a gabanta tare da cewa gashi inji Siyama,Mum tace me Muka samu Kuma ta bude flask din taga farfesun kaji ledar ta Bude ta washe baki tace an gode Mata Allah ya Mata albarka,yanzu nasan Ina da suruka,Aslam yayi murmushi ganin Mum ta Kira Zainab ta kawo plate ta ebi nata ta bawa Zainab nasu,Mum ta Fara yagar kaza tana cewa wannan yarinya Allah ya mata Albarka,Zainab ma tana ci tace haka ake son suruka wasu Kuwa Kai da kayan danka ya gagareka,Aslam yace ni baza ku sa min albarka? Mum tace Kai Dan Allah rufe mana baki muna Jin dadin mu wannan motar ma ta waye ne nasan baka aro kayan wasu,Aslam yace tawa ce Mana ya Fara bawa su Mum labarin komai har ya gama,Mum tana tsotse Kashi tace amma ka wahalar damu har hawan jini sai da yakamani,kiyi Hakuri Mum kin San dalilin da yasa nayi haka yanzu,ae hakan ma kayi dai dai gashi Yanzu mun samu Yar arziki irin albarka,amma cuta sai da ta kamani,Ki zabi kasar da kike so Mum na kaiki ki huta,tace ba yanzu ba aure zanyi na tafi da mijina,Dariya ta bawa Aslam yace kina son aure Mum?wa yaki ibada da ace Ina da mijina ai bazan dinga yawo kasa kasa ba da sauran kuriciyata fa,Aslam yace Mum na Miki miji, Waye? Ki auri Shehu Baban Nusaiba,Mum tace Kai nifa bana son kazami Indai tsoho ba me tsafta bane karka kawo min shi bare wannan Yarinyar tasa marar kunya bada ni ba,dariya Suka yi,Baffa Shehu ai Dan gayu ne kin girme shi fa sosai sai dai yayi manage dake cewar Aslam,Mum tace tashi ka tafi ka San inda dare yayi maka tunda magana zaka fada min,Yace Flask dinmu fa? Hajiya Zainab tace ai ba bata zaiyi ba in ka dawo sai a baka,yace idan tana son amfani da abinta fa matar gidan,Mum tayi dariya tace duk cikin zumudin Amarya ne rabu da shi Aslam kuwa kitchen ya shiga da Kansa ya dakko wani flask din da Kansa ya juye ragowar a ciki ya dauke flask dinsu ya rufe ya musu sallama ya tafi Wajen Sabeer yaje shima Sabeer tunda yaji ya dinga masifa yace ka wahalar damu wallahi sai ka biyani dubu dari biyar dina dana taimakeka da ita ai ka fini karfi,Aslam Yana dariya yace dama badan Allah ka bani ba,yace na fasa taimakon ka dawo min da abata nima na kusa aure,yace Zan maka transfer din tsiyarka yace da yafi maka Suka Yi dariya tare da tafawa,a ranar Aslam duk Wanda yasan ya talauce sai da yaje ya tabbatar Masa ba Haka bane,karshe gidan su Siyama yaje,Kawu da yaji yace banyi mamaki ba tunda dama Sam lokacin baka Yi kala da Wanda ke cikin wani Hali ba,Aunty tace uhm lallai Aslam kayi kokari da kayi haka,Siyama tace a gaishe ku,Aunty tace ai munyi waya dazu dazu ta kirani,Kawu kam cewa yayi fatan yanzu ta kusa haihuwa? Murmushi Aslam yayi cike da kunya bai ce komai ba, Kawu yace ei kaji kunya Mana yanzu ai da a baya baka ji ba so ya rufe maka ido,Aunty tace Kai Kuma ga mita tunda an riga anyi ai sai ka hakura, Aslam ya zaro kudade ya ajiyewa Aunty, Kawu ya raka shi Yana cewa wallahi idan baka kula da 'yata ba sai ka gane kurenka,Indai tayi wata uku banga tayi kiba ba zaka fadawa mutan garinku,Aslam Yana dariya a ransa yace Zama tayi Inshaallah,Yana Fitowa har zai je waje Shehu sai ya fasa yace sai nan gaba tukun ba yanzu ba ya koma gida abinsa. Aslam Yana komawa gida suna hutawa a Palo Siyama tana jikinsa a kwance me aiki ta shigo tace yayi bako,Yace Siyama ta koma sama baza a kallar Masa Mata ba,mikewa tayi ta haura sama,sannan yace a shigo da bakon Jin ance ma'aikacinsa ne,Yana shigowa sai yaga Sufyan ne ya shigo a firgice ya tsuguna a gaban Aslam yace dan Allah Sir kayi hakuri ka yafe min,Aslam yace tashi tashi ba matsala ai ba laifinka bane Sufyan na fahimci komai Kai ai baka da laifi,Sufyan Yana zufa yace ban San matarka bace ka yafe min,Aslam yace please get up ba damuwa aikinka Yana nan,Sufyan yace ba wannan ba Sir cikin Ina Ina yace ...Ni...Ni...nine na zuga Nusaiba akan sai ka saketa na aureta,tun tana gidanka nake zuwa Muna fita yawo,ni nake kaita restaurant munyi soyayya tana da aurenka,a nan ran Aslam yayi mugun baci ya tuna Sanda ko girki baza tayi ba sai dai ta shirya ta fice ashe tare suke fita,yace dama tare kuke fita Kaine kake Neman matar aure me yasa mutane wasu baku da Imani ne,Sufyan yace na tuba dan Allah karka koreni Sir,yace oh yanzu da badan ni bane da shike nan kaci banza ka cuci mutum,ka daina batawa kanka lokaci da nayi Niyyar kyaleka ashe Kai azzalumi ne ba mutumin kirki bane me bin matan wasu na sallameka daga aiki,Sufyan hawaye ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71