Skip to content

Chapter 12

Chapter 12

AURENMU Book One Complete Hausa Novel 1,255 words 0 views Progress saved
Download Book

fita tace dan Allah bar min key dinki a hannuna Zanyi girki a gidanki gas Dina ya Kare,Raudat mutuniyar Landlady ce shi yasa Kai tsaye ta bar Mata key ta fice,masu aiki ta Kira Affan ya biya kudi aka huda katon Palo ya fito ta palon Raudat aka sa glass da komai cikin kankanin lokaci,aka sake huda wani window ta bedroom dinsa ya bullo ta cikin bedroom din Raudat shima an sa glass anyi komai,Raudat tana dawowa taga palonta ya koma wani iri ta duba taga windo ga palon Affan, bedroom ta shiga nan ma mamaki ya kuleta ta tafi wurin Landlady da sauri,Me gidan tasan zance shi yasa ta kulle bangarenta gaba daya ta fece ganin gida sai tayi sati zata dawo,Raudat ciki ta koma . Affan ne yake ta faman shara da kalkale kalkalen gida sai kace mace haka part dinsa yake da tsafta komai a shirye a gyare Raudat tana ganinsa ta window Yana ta faman goge goge ya gama ya Shiga kitchen ya dora abinci harda fasa kwai ya dawo jikin window Yana karkadawa Dan Kawai ya tsokani Raudat, tana kwance a saman 3seater window din ya bude ya leka ta ciki yace ke Balagaggiyar akuya,kaine balagaggen dan akuya kwarto dan taure ka isheni Malam ka kyaleni da wulakancin da aka min aka hada min window da Kai wanne irin masifa ce wannan har windown bedroom,ae ai gwara naji munsharinki ba a ja damu idan na kulla da mutum ya Shiga uku sai na hanaki Shan ruwa,Raudat ta kalleshi tace wlh baka Isa ba Kai din banza ka hanani Shan ruwa,Kitchen ya koma yaci gaba da girke girkensa tana ji kamshi na tashi bata kulashi ba,Bata ko kalli window dinsa ba ya gama ya zubo egg source dinsa da shinkafa Fara harda Naman kaza plate daya ya Mika Mata yace ungo badan halinki ba,ba kunya ta mike taje zata karba ya janye plate dinsa Yana dariya yace yanzu sai ki karba?Dan Allah ka bani na gaji dama bazan iya girki ba yanzu,ai Kuwa Zaki mutu da yunwa ya bar jikin window ya koma palonsa tare da kunna tangamemiyar plasma tv dinsa Yana kallo yana cin abinci. Aslam ne ya fito sanye cikin farar Jallabiya ya zuba wanka Yana shining da kamshi ya zauna a dining inda Charity ke zaune tana cin nata abincin,Ina kwana tace Masa ya amsa da fara'a sanye take cikin wata barmemiyar t-shirt yellow da wando me Fadi baki duk da haka tayi kyau Dake me kyau ce harda saka hula,dariya take bawa Aslam,Nusaiba ce ta fito sanye cikin kayan baccinta tana Mika kusan tsirara haka take amma ta fito harda yin Mika,Charity ta kalleta ta kalli Aslam tace a rike Mata,Aslam yace me? So take tace ya tallafe ta iskancin ya motsa sai taji kunya tace ba komai,Nusaiba ce ta kalli Charity ko a jikinta ta zauna Wai zuba min tea, Charity tace kinyi kadan wlh ke dai baki Isa kin sani aiki ba,a gidan aure na kike fa,Tattabara ma taci ubanta cewar Charity ,Nusaiba Tsaki ta ja tare da zuba abinda take so ta ja gefe tana ci ko a jikinta ba ruwanta da mijinta Kawai ita kudi,tana gamawa ta mike ta shiga bedroom,Aslam ya kalli Siyama wacce ta mike itama zata tafi yace Charity zo muyi gulma,Dariya ya bawa Siyama ta dawo ta zauna tace to muyi ta furta kasa kasa da muryar rada,yace bai kamata na fada Miki ba Sirrina nane sirrin iyalina amma ba yanda zanyi so nake ki Mata fada ki dinga fada Mata gaskiya ko zata yarda ni Ina son matata Ina so mu zauna lafiya amma na kasa gane kanta ba wani kulawa ba soyayya komai kudi,komai a bata kudi Aslam ya fadawa Charity duk abinda Nusaiba ke Masa yace kuma bata ganin girmana,Bata iya magana ba abinda duk taga dama yazo bakinta haka zata Yaba min,gaskiya bazan boye Miki ba idan nasan haka Aure yake da banyi ba da na hakura nayi zamana a single, Charity ta tausayawa Aslam amma tace kayi hakuri mu Mata da yawa haka muke auren kenan shi yasa ake cewa sai hakuri, Inshaallah Zan dinga fada Mata gaskiya ka Kara hakuri haka ta dinga kwantar Masa da hankali suna haka sai ga Nusaiba ta cakare ta fito tace shopping nake son zuwa,yace baza ki je ba wlh sai naje Kuma nasan Dan Kar ka bani kudi ne Kuma na eba,ta juya zata fita Siyama tace Nusaiba dama haka Kika koma wacce irin hauka ce wannan? Ke a naki haukan ma harda jahilci wlh kin bani mamaki Ashe ke jahila ce haba Nusaiba yanzu idan wani yace me zai ci da Yar talla sai kiji haushi bayan wasu ne ke bata wasu,mijinki yace Bai yarda ki fita ba amma kice sai kin fita bai baki kudi ba kin ebar Masa kudi mene hakan ke nufi,wlh kiji tsoron Allah ki gyara halinki,wani wawan Tsaki Nusaiba ta ja tace to munafuka Sannu uwata ke kin Isa ki min fada karfa ki manta Yar aikina ce ke ta sake Jan tsaki ta fice,cike da bacin rai Aslam ya mike Kawai ya haura sama Yana mugun mamaki ko a film bai taba ganin haka ba da labari aka bashi bazai yarda ba. Ya dade a sama Charity tana zaune a Palo itama tana Takaici da mamakin Nusaiba,Fitowa yayi yasha wata shadda da alama fita zaiyi Charity tana zaune tace dan Allah kayi hakuri Sir,ka kwantar da hankalinka karka sa damuwa a ranka Inshaallah zata gyara komai zai wuce,Murmushi yayi Kawai yace ba komai na gode ya fita,lunch ta Dora musu tasan bai fiye Zama a Office ba. Bayan sati biyu Charity tana gidan kullum tana kallon haukar da Nusaiba take zubawa Iskanci kala kala Aslam bai Isa da ita ba duk da haka Siyama sai ta fada mata gaskiya tana ta kokarin ganar da ita tana kwantarwa da Aslam hankali Abu yaci tura kullum ma abin na Nusaiba karuwa yake Yi,Mota me kyau ta million uku ya siyowa Nusaiba ya shigo da Fara'a yace yau zaki surprise Zo muje ki gani,Charity tana goge dining yace taho kema ki taya kawarki murna,Nusaiba tana zumudi tace ka daina cewa kawata Yar aiki na ce fa suna Fitowa ya nuna Mata dalleliyar mota sabuwa ya Mika Mata key yace gashi Taki ce,Maimakon fara'a da murna sai aka ga Nusaiba ta bata rai tace yanzu Baby ka rasa motar da zaka siyo min sai Toyota Carina matan masu kudi irinka suna Hawa manyan motoci su Marcedes benz su perari,bugati amma kamarka me kudi haka ka siya min Toyota ordinary Toyota,Da karfi charity tace Nusaiba...oh my God wannan wacce irin rayuwa ce,ke Kika nema Masa kudin,Nusaiba ki tuna fa gidanku da inda Kika fito,Tsaki Nusaiba ta ja ta koma ciki abinta tace bana so Indai Toyota ce wallahi bana so,zuciyar Aslam ji yake kamar ta fito sabo da bakin ciki da bacin rai,Charity har kwalla tayi sabo da takaicin Nusaiba da tausayin Aslam,tace kayi hakuri dan Allah,kaddara ce Allah ne ya jarabceka kayi hakuri ka cinye jarabawarka,kowanne Dan Adam da tasa Jarabawar kayi hakuri ka kwantar da hankalinka please,Aslam kasa magana ma yayi ya wuce ciki Kawai. Bayan wasu Yan kwanaki Aslam kullum cikin damuwa yake ko abinci bai

Table of Contents

Chapters

71 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71