Chapter 11
Chapter 11
ta bar Aslam a tsaye kikam yace karfa abinda nake tunani ya Zama gaskiya karfa Yarinyar nan dan kudina ta aureni,Zama yayi ransa a bace babu wani so ko kulawa babu tunda ya aureta bakin ciki take cusa Masa tun Yana sharewa har ya gaji. Zuwa dare zuwa tayi cikin kayan baccinta tana zuba kamshi ta kwanta a gefensa,Aslam ya hadu ne ta ko Ina bata iya share shi jikinsa Kawai abin kallo ne,rungume shi tayi ta baya hakura yayi ya juyo Suka kwashi love,Watan Nusaiba daya ta shirya driver ya kaita gidan su Charity, Charity tana zuba kullin Alala taga Nusaiba da murna da ihu ta mike ta tafi da gudu zata rungumeta cikin azama Nusaiba ta ja baya tana Danna Wayarta me tsada tace karki bata min jiki baki ga a gindin murhu kike ba so kike na Fara warin hayaki, Charity ta saki baki tana mamakin Nusaiba ganin haka Kawai Charity itama ta shareta taci gaba zuba da alalarta ta bar Nusaiba a tsaye sai da Aunty ta fito jiki na rawa tace Nusaiba kece Nusaiba ta ja kujera ta zauna,bayan sun gaisa da Aunty tace dama wata samuwa ce ta taso da abin Alkhairi shi yasa nazo na Fara sanar muku,me aikina guda Daya ce ta min kadan to Zan dauki wata Yar aikin Kuma dubu talatin mijina ke biyan ma'aikatansa me zai hana ku bar Charity ta koma can da aiki ai yafi talla ta Zama kamar ma'aikaciyar gomnati dubu talatin a rayuwar nan ai ba Wasa bace,shine nace ai da bare gwara na gida Bari naji ko Charity zata yarda,Aunty dake ba yarta bace tace an gode wlh Zama ta yarda ko Dauda idan yaji ai zai yarda dubu talatin fa ai tsab zamu rage radadin talauci,Charity tace bazan je ba ni babu gidan wacce zanje bauta,Nusaiba me yasa Kika Zama marar Imani mun taso tare kina kawata Amma burinki ki ganni a kaskance a wulakance me na tare miki,ke ba abin kunya bane ace babbar kawarki da ya kamata ki taimaka yau Nusaiba kawarki Zaki dauka a matsayin Yar aiki sabo da bani da gata Charity ta karasa da hawaye,Dauda ne ya shugo Yana tambaya lafiya? Aunty ta bashi labari babu bata lokaci yace Siyama hada kayanki Alhmdllh kudi sun samu aiki har gida ke ai abin ma ki godewa Nusaiba ne Kuma gata kawarki ai baza ki Sha wahala ba tashi maza bar Alalar masu siya in sun matsu suzo gida,Charity ta mike tace Inshaallah abinda Kika min Nusaiba Watarana sai kinyi Dana sani kayanta ta ebo a Leda viva Suka fita da Nusaiba,Nusaiba ta Shiga bayan mota ita Daya tace Charity ta zauna a gaba,Siyama Bata sake magana ba har Suka Isa gidan Aslam Aslam Yana compound Yana hutawa ya zaci Charity ziyara ta kawowa kawarta ma yace sai yau Zaki zo munyi Fushi,Charity ta kalle shi Suka hada Ido gabanta ya Fadi ya hadu karshe,gaida shi tayi ya amsa da fara'a suka shiga ciki Nusaiba ta fada Saman kujera tana huce gajiya tace wash Kinga Charity zo ki min tausa Charity kamar gaske ta tsuguna ta Kama kafar Nusaiba maimakon Tausa sai ta lankwasa kafar iya karfinta zata balla ta,Nusaiba ta kwala ihu tare da kwace kafarta tana zagi ke wacce Dabba ce,Charity ta samu ta gallawa Nusaiba Mari ta dungure Nusaiba tace shegiya ke din banza na Miki bauta wlh kinyi kadan ta juya ta sake tallafewa Nusaiba keya ta baya ta wuce ta Shige bedroom din da Suka taba zama a gidan tare,Nusaiba ta taso a fusace tace fito ai ba gidan ubanki bane,Charity tace ai ke shi yasa Naga Shehu ne ya Gina gidan har kinyi clean Yarinyar da ni nake koya Miki daurin dankwali,Nusaiba sai dura ashar take Yi. Washe gari da yamma Aslam yasha suit farare ya dawo daga Office ya iske Charity zaune cikin riga Yar kanti doguwa red,Nusaiba an cakare cikin Super green,Yana shigowa Nusaiba tace karbi jakarsa ki Kai masa bedroom,Charity ta duka tare da cewa barka da zuwa Sir ta karbi brief case din ta wuce sama ta Kai har cikin dakinsa,mamaki ne ya hanashi magana ya kalli Nusaiba yace Wai meke faruwa ne?Nusaiba tace Yar aiki na Karo guda Daya ta min kadan,Kuma best friend dinki? Rokata Suka Yi dan Allah a dauki Yar su aiki kullum Charity sai ta bugo min waya,ya zanyi dole nace tazo ta Fara Kuma kawarki Baby,haba Nusaiba bai Dace ba me yasa baki da tunani ne,ba ruwanka tunda na fada maka gaskiya kaki ji,Charity ce ta fito Aslam ya Kira sunanta Siyama tace naam,Dan Allah ki koma gidanku hakan bai Dace ba ni bana ma bukatar Yan aiki, Charity tace ko na koma Babana bazai kyaleni ba dole sai nayi aikin nan Kawai idan akace yau baka da iyaye to ka shiga Uku karka damu zanyi aikin,Aslam ya buga ya buga Charity tace Zama daram,Nusaiba tace ka kyaleta na fada maka tana so Washe gari da wuri Charity ta tashi ta shirya musu lafiyayyen Kari waccen Yar aikin Kuma tana ta gyara gida me gadi Yana aikin compound ko Ina na gidan ya dauki kamshi... Affan ne a zaune Yana waya ya mike ya fito daga part dinsa Yana cewa Yaya kayi hakuri na rigada na karba kudin,Wanda ya Kira da Yaya masifa Kawai yake ma Affan tunda Kai ka kashe zuciyarka baza kayi aiki ba ka daina kassara Ni kana zuwa ka karbi kudi yanda kaga dama,an baka aiki da komai kaki Yi,na samo maka har Offer a gomnati kaki yi na baka babban matsayi a company na kaki yi,na saka a Kan business kaki uban me kake so ayi maka Kai a duniya baza ka motsa jikinka ba mace ma ta fika kokari sai dai kaci me kyau ka sha me kyau ka saka sutura ka zaga gari,Affan ka kiyayeni karka sake zuwa ka karbi kudi a wajen ma'aikatana kaje kayi rayuwarka,Affan da shagwaba Kamar dan yaye yace ni bazan iya aikin nan naku ba na wahala idan kudinka ne bazan sake karba ba ya kashe waya,Raudat tana wajen tana ji sai dariyarta yaji tace anji kunya kayi asara Kuma Namiji da Kai ka kashe zuciyarka ka zauna zaman banza zaman kashe wando, Affan yace a gidan ubanwa na kashe wandon? Wandunana fes suke kije ki gani Designers ne,Allah ma ya kiyaye ranar da za ace na kashe wando na ban canja sabo ba Idiot ya juya ya wuce dan shi Affan bai gane hausar me take nufi ba AsmaBaffa [4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️ 26-30 Official By AsmaBaffa Page naku ne MARYAM T BALIYA UMMU ISMAIL Ranar Affan ya Kira Landlady dinsu yace window nake so a Kara min a part Dina daya windown ya fito ta gidan wannan Raudat din Sabo da Algungumai dayan ma ya fito ta cikin gidanta Sabo da munafukai,Landlady tace palon Raudat ne fa Daya Kuma bedroom dinta ta Nan za a maka windunan?Affan yace ae ko ki min ko a bani kudin haya dana biya, Landlady tace Banda kudin da Zan biyaka yanzu na yarda Kawai Zan maka windunan amma sai ka biya kudin da za a kashe kwandalata baza tayi ciwon Kai ba,Ba matsala ya furta,Landlady sai da ta bari Raudat zata
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71