Chapter 54
Chapter 54
fito Yana kallon Siyama yace fatan dai Jin dadi ne ya sa Kika canja haka ba Sha ka fashe kike Sha ba da Kuma wannan kwayoyin na Karin hasken fata,Siyama tace ni da nake Fara Kawu Jin dadi mana,yace to madalla Allah yayi albarka ya Kara muku zaman lafiya yaro ka iya kiwo gata nan ta canja haka ake so to ke Kuma Kar naji Kar na gani na fada Miki karki sake a kawo min kararki na fada Miki,Aunty tace to ai taji dan Allah,a gida ya barta ta yini ranar sai magriba ya dawo Suka tafi gida ya kaita wajen Mum ta kwashi gaisuwa a nan taji Mum zata tafi Qatar ta koma can ta huta Wai ta fasa auren Indai Shehu ne bata sonsa,daga Nan ya kaita gidan su Sabeer Wanda shima gaf yake da aure. Raudah biki ya matso ta koma gidansu can tana Shan gyaran jiki iri iri iri,Affan ma bangarensa ya gama gina gidansa me kyan gaske dama tunda ya samu aiki fili ya Fara siya ya Fara gininsa a hankali gidane flat me shegen kyau,Raudah Kuwa Babanta me kudin gaske ne Furniture dinta da duk wani kayan da za a zuba Mata a gidan daga kasar waje aka kawo su na musamman,ana Saura kwana uku daurin aure duk wani gyara an gama anzo an shirya Mata kayan gidanta a Kano unguwa ce me kyau ta masu hali dama shi Affan sarkin gayu da son wanka komai sai me kyau,sun gama gayyatar mutane ranar Alhamis duk Dangin Affan maza Suka tafi daurin aure da da abokansa duk acan zasu kwana a daura aure su taho da Amarya,Yan uwansu na zamfara duk sun tafi,an musu masauki a hotel duk mutum biyu daki daya haka Suka kwana washe gari ana yin Sallar Juma'a aka daura Auren Affan da Raudah Kan sadaki Naira dubu Hamsim,Affan Yana gaisawa da mutane Zo kuga wanka wajen ango kowa sai kallonsa yake sabo da gayu,ya juyo kenan Suka hada Ido da Yusuf Yayansa ya saka Dan Yadinsa da gani kasan wahala yake Sha,Cin Amana ba kyau,Affan ya karasa wajensa suna mugun Kama yace yaushe kazo Yaya? Baka gayyace ni ba naji labari nazo ai, Affan gefe ya ja shi yace a Ina kaji labari? Yace Nabeela ce ta fada min komai naka har IV ta tura min a waya,Na dade Ina Neman Ina zan ganka na roki gafararka Affan ban ganka ba sai da Allah ya hadani da Nabeela ta fada min inda kake da aikinka da kake da aurenka,Affan kayi hakuri ka yafe min,nasan naci amanarka a matsayinka na dan uwana,ka sadaukar da komai naka a kaina dan na samu ilimi nayi kudi na dawo na dauki nauyinka amma ban saka maka da komai ba sai jefaka cikin kunci nasan na zalunceka Affan na jefaka cikin kunci ka yafe min Affan na gane kuskurena Kuma Inshaallah Zan gyara ka karbeni a matsayin dan uwanka Karo na biyu,ka bani dama na gyara kuskurena,Yusuf Yana hawaye Yana magana yace I missed you Affan,Affan yace ba komai Yaya na yafe maka da Kai da Nabeela na yafe muku,tazo wajena naji abinda ya faru da Kai Allah ya kiyaye gaba,Yusuf yace Ameen yanzu da kyar na samu Offer teaching a secondary school kasan aiki a kasar nan,Affan yace karka damu Yaya Inshaallah Zan sa uban gidana ya baka jari ko da milliyan uku ce ka Fara kasuwanci ko ya yake kaga kana aikinka kana kasuwancin ko yaya ai yafi,Godiya Yusuf ya dinga zubawa yace ba komai ai kai dan uwana ne jinina bani da kamarka Yaya,muje ku gaisa da Liman shine uban gidana ya jashi Suka gaisa,ya kaishi wajen surukinsa Baban Raudah suka gaisa daga nan mutane duk sun tafi kowa ya hada karensa daga Sayyeed sai Ango sai Yusuf. Hotel Suka koma Affan cikin kayan da yazo dasu akwai shaddar da bai saka ba sabo da tela Wai ya Masa Katon dinki me Fadi Yusuf ya Fishi kiba kadan sai ya bashi yace yayi wanka ya saka suje yaga Raudah yawa ne aga Yayana guda da local yadi,Dariya Yusuf yayi yace kana nan dai Affan Kai da wanka Amana ne haka yayi wanka yasa shaddar dai dai shi yayi kyau Kuwa ya fito Suka tafi,Raudah anci gayu Yarabawa sun cika gidan suna ta kade kadensu na yarabawa suna tikar rawa,Raudah ma tana cikinsu sabo da abokan arziki ne Kawai, Affan ya kirata a waya tazo su gaisa da Yayansa,Raudah ta fito harda Jin kunya ta rusuna harda durkusawa ta gaida Yusuf ya amsa Yana cewa tashi tashi Raudah na gode Allah ya baku zaman lafiya,kin ganni feel free duk abinda ya Miki ba daidai ba just call me,dariya sukayi Sayyeed yace mu wuce dare da nayi,Affan a gurguje ya sa Mata number Yusuf ya bawa Yusuf Number Raudah Suka taho gaba dayasu Uku a jirgi Affan shi ya biya Yusuf. Suna zuwa Kano sai da ya kaishi gidan Amarya da ya gida ya gani,Yusuf yace gidana da ka sani da fa sun kwace amma dana dage da addua sun dawo min da gidana motocin Suka rike Kawai, Affan yace Allah zai baka wata Inshaallah Zuwa dare aka kawo Amarya a jirgi daga Yan Uwa sai wasu yarabawa Mata su Uku abokan arziki,a gidan Liman ake shagali can aka sauki bakin Amarya da amaryar gaba daya tana can gidan Liman,Yusuf a wajen Su Affan zai kwana gidan hayar Affan inda suke zaune da Raudah can aka sauki baki maza,Suna kwance a bed daya Affan da Yusuf sai hira suke Affan yace muyi bacci ni gaskiya bacci zanyi gobe Ina wajen Amarya bani ba bacci gobe gwara nayi nawa yau,Yusuf yace zumudi Affan ko kunya babu, ya kamata idan anyi nisa da amarci kazo kaduna gidana kaga matata da yaro na,Affan yace zanzo amma ya kamata ka maida Nabeela tunda gaba dayanku Kun gane kuskuren ku,Nabeela Bata so na Affan sabo da kudina ta aureni lokacin amma a gaskiya Kai ta ke so ni yanzu na samu me so na tsakani da Allah Waheeda matar arziki ta isheni idan ta samu miji tayi aure, Affan yace to shike nan Allah ya bata na gari ni dai gobe i yanzu Ina can ana min shagwaba da kuka,dariya Yusuf yayi yace wlh karka daga kafa ranar farko ta wuce ka tafi ko wacce rana dadi,Affan yace ahaf ai sai dai in Suma naga tayi Suka Yi dariya suna hira har bacci ya kwashe su. Washe gari da Yamma Amarya Raudah tayi wanka ta hade cikin wani material pink ya hadu ta zuba kyau dinkin fitted gown kamar readymade ta sha mayafi me daukan Ido shima pink komai pink takalmi da jaka pink lady in pink,Wanda Suka kawota ne Suka kaita gidan Miji ko digon hawaye Raudah bata Yi ba sabanin ta taba aure sannan Kuma ba a gida take zaune ba idonta Kar a cikin Mayafi. Abokan ango duk sun ware Yusuf Kuwa Affan Dubu talatin ya bashi cash cikin gudunmuwar da ya samu ya tafi gida abinsa Yana farin ciki. Yan Kai Amarya suna kaita Suka bi jirgi Suka koma tun yamma aka bar amarya ita kadai sai Landlady data Kara gyara Mata gidan ta kunna turarukan wuta ta fesa room freshner a ko Ina bedroom
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71