Chapter 19
Chapter 19
kusa zuwa inda yake ba Siyama ce ta taho da gudu ta fisgi hannunsa tace mota da sauri suka tsallaka suna tsallakawa motar ta wuce da mugun gudu,ta kalleshi tace tunanin me kake Yi haka ta furta tana kokarin zare hannunta a nasa Wanda ya damke hannun nata cikin nasa Yana Jin wani shock da bai taba jinsa a jikin wata ya mace ba,Napep Suka shiga zuwa gidansa Siyama ce ta biya kudin ta hanashi ya biya kudin,suna zuwa Nusaiba chatting take abinta ga ledar kayan nan a gefe,Siyama tana zuwa tace ke ballagazar matar aure shashashar matar Aslam, kallon Charity Nusaiba tayi Kawai ta ja tsaki,Siyama ta zari ledar Aslam ya zauna tace Ogana me za a dafa Murmushi ya saki yace kiyi farfesu Kawai sai Dan abincin dare,an gama ta furta tana kallon Nusaiba tayi fatali da kafar Nusaiba dake mike a hanya tace matsa can Yar banza Yar wofi,wawiyar banza,Dariya Aslam ya shiga yi Nusaiba ta galla Masa harara tace dan uwarki ba Charity kike ba ko Ngozi kike nafi karfinki wahalalliya me bauta a banza, Siyama ta yiwa Nusaiba dakuwa ta shiga kitchen tare da kunna gas ta Fara aikin girkin sai wurin magriba ta gama farfesun ta ebi dan kadan a roba me murfi ta rufe,Ta fuskanci yana son tuwon danyar shinkafa shi tayi Masa da miyar danyar kubewa ta Gama komai yayi Alwala zai fita masallaci tace na gama, yace Banga kinci ba tace gashi na eba ta nuna Masa robar, tare Suka fita ta shiga napep shi Kuma ya wuce masallaci. Nusaiba tunda tana zuwa restaurant bata damu da abincin Aslam ba Sufyan Yana mugun kashe Mata kudi yanzu burinta Aslam ya sake ta,washe gari Mama Shehu ta tambaya tace zata je kauyensu ya barta tana tafiya sai gidan Nusaiba da Yar Jakarta wai tazo zata kwana biyu a gidan yarta,Nusaiba ta dauki Jakarta ta Kai bedroom ta hau girke girke Aslam Yana zuwa yaji kamshin girki na tashi yasan da dalili shigarsa bedroom kenan ya iske Mama a ciki yaga Kuma jakar tata tabbas kwana zata yi, mamakin suke mugun bashi,Mama ganin ya shiga ta fito,a gabansa a palo Suka zubo abincinsu Suka ci Suka koshi ko tayi basu Masa ba Yana Jin yunwa sai fita yayi yaci a resturant bai dawo ba sai 10pm lokacin Mama da Nusaiba sunyi Shirin bacci sun kwanta a saman gadon me gidan sun shige bargo tare,Aslam ya dan leka ya girgiza Kai yace idan baki da kunya Mama kin hadu da Dan zamani,bedroom din ya Shiga Mama ta bude baki,toilet ya Shiga suna ji Yana wanka Mama tace yau na shiga Uku da fitsararre,sai da yayi wanka ya fito daure da guntun towel,Mama Hannu ta dora a Kai tare rufe Ido tana yau na shiga Uku yau Naga jaraba,cikin bargon ta Danna kanta,turaruka ya fesa ya zura Jallabiya arsh,Kawai Saman bed din ya nufa yace Mama Dan matsa gefe kadan gadon zai iya daukar mu mu uku ba damuwa,Mama taga da gaske hawa zaiyi ya kwanta ta dirga kasa harda faduwa tace amma Kai ba dan arziki bane ban taba ganin suruki marar tarbiyya ba sai kai ta fice Palo tana cewa Nusaiba Miko min jakata a Daren nan Zan koma gida,Nusaiba ta mike tana hararar Aslam ta dauki jakar Mama da tarkacenta ta fito,Aslam ya kwanta a saman bed dinsa tare da Jan tsaki yace iskancin banza tunaninku ku kadai ne Yan iska uwar banza ya lulluba da bargonsa,Ita Kuwa Nusaiba a daren ta fita ta samawa Mama Napep ta koma gida,Shehu sai ganinta yayi ta dawo,yace ya na ganki ke da Kika ce Zaki kwana a kauye,Mama tace Wlh mutan gidan da naje domin su sunyi tafiya basa gida shi yasa na dawo,Shehu yace ke Kika sani kuma. Washe gari da wuri Nusaiba ta Kai karara Aslam Office din Yan Hisba tace so take a fadawa mijinta ya saketa bashi da lafiya baya iya biya Mata bukatar Aure sannan ma ita ta daina sonsa ya Fadi abinda ya kashe zata biya shi ya saketa,Aslam yana gida ya fito zai fita Kawai yayi arba da jamian hisba mutum biyu suka Mika Masa takarda ana nemansa a Office din Hisba yasan Nusaiba ce kawai Sabo da haka Kawai sai ya nufi can a Napep. Wacece Raudat Raudat Ibrahim Waku 'yace ga Ibrahim Waku hamshakin me kudi ne dan asalin jahar Gombe Wanda ke zaune a Oyo state,tunda kasuwanci ya kaishi can ya shahara ya Zama hamshakin me kudi na gaske ya tattara da yaransa su Raudat gaba daya ya koma Oyo da Zama,matarsa daya tal Hajiya Rahmatu itama Yar Gombe ce, yaransu biyar Raudat ce babba sai kannenta biyu maza biyu mata,Raudat tana gama secondary ta samu Saurayinta Hussain dan Kaduna state,Hussain talakawa ne a zahiri ba son Raudat yake ba irin masu auren Mata ne dan kudinsu dan ace Kawai ya auri Yar me kudi,Baban Raudat tunda yaga Hussain da Kuma cewar baya sana'a ko kadan yace ta hakura amma taki ji Sam dole aka Yi Mata auren wuri Bayan anyi auren Raudat da Hussain Baban Raudat shine ya Kama musu gida haya a Kaduna sannan gara ma kayan abinci mota guda aka ajiye da komai sannan baya Bari yarsa Raudat da talauci,Raudat komai ita ke Yi a gidan ta koma itace mijin ba karya akwaita da hankali ga hakuri duk wani kyan haki Raudat tana da shi dai dai gwargwado,Hussain Kawai sai dai ya kwanta an bashi jari ya cinye an sake bashi har Karo na uku amma sai ya kashe,tunda Raudat ta aure shi bai taba kwanciyar aure da ita ba Basu taba sex ba sabo da bashi da lafiya amma yaki yarda fada bashi da lafiya,abinka da yarinya itama sai ta kasa fadawa kowa suna zaune haka har kusan shekara Hussain ga mugun son Mata bai da aiki sai kula Mata duk kudinsa Yan Mata ke cinyewa shi Kuma dayar ma da ya aura ya kasa biya Mata bukata amma Yana hangen na waje,a Haka ko Raudat bata bashi kudi ba sai wulakanci da cin mutunci iri iri Indai tana son zaman lafiya to ta bashi kudi,abinda yake batawa Raudat rai Shan giyarsa sai ya Sha giya yazo ya Mata dukan taiya,duk ta rame sam bata San mene dadin miji ba,ana haka ya fara Mata sharri sai ya shirya zance na karya ya fadawa dan ginsa da abokansa,akwai Sanda ma yace bata bashi abinci Kuma har zaginsa takeyi,Watarana ma ya dinga fadawa abokansa ai maza take bi da Aurenta har kunnen Danginsa zance. Su Kuma dangi ba bincike ba komai suka saka Raudat a gaba Babar Hussain da kanta ta sa Hussain ya saki Raudat dama bai damu da ita ba itace take sonsa kawai a hakan ma da ya saketa sai da ta Sha kuka auren shekararsa Daya da Dan watanni ta koma gidansu,tayi jinyar zuciyarta sosai kafin ta hakura da son Hussain shi kuwa Hussain baya ta tata Sam,Babanta ne ya maida ta school tayi degree tana gamawa ya samo Mata aiki Babba da NGO su Kuma duk inda aka turaka aiki dole sai ka je,Kano Suka kawota supervisor ce sune suka rabawa irinsu sababbin motoci masu tsada,dama Kuma a can Oyo tana da tata motar da Babanta ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71