Chapter 63
Chapter 63
uwarta sai mutum ya fasa zuwa,akwai mutum biyu ma sunzo amma tun daga zuwa daya Nusaiba bata sake ganin sun Zo ba an zuga su a unguwar ,wannan karon Ido rufe take Neman miji ko ba me kudi ba ma amma talakan ma ta rasa shi. Yau tana part din Amarya tana Mata uban aiki Landlady taga tana hawaye,tace Nusaiba lafiya? Nusaiba ta zauna ta bawa Landlady labarin abinda ta shuka kaf tana kuka tace yanzu miji nake nema ko talaka ne wlh Zan zauna na rike mijina amma Kinga talakan ma na rasa duniya me yayi, Landlady tace wlh kin bani takaici ko Mene ke Kika jawowa kanki Nusaiba yanzu ai an waye kina gani yanzu manyan mata ma kula suke da mazajensu bare Yan matan yanzu,shawarar da Zan baki ki yiwa iyayenki Biyayya har Maman taki ki samu Wanda Kika batawa ki tabbatar sun yafe miki sannan ki dukufa da addua ba dare ba rana Allah zai kawo Miki miji kin samu dama me kyau har biyu kinyi watsi da ita ai gashi nan yanzu son kudi da son zuciya da hauka sun kaiki sun baro yanzu wa gari ya waya? Nusaiba tace Inshaallah zanyi yanda Kika ce,Nusaiba haka ta sake gyara halinta tana ta Addua tana yiwa mahaifinta biyayya amma ta kasa zuwa Neman yafiya wajen Sufyan da Aslam sabo da kunyar abinda ta aikata. Mama tana Kauye lokacin da Nusaiba ta kwashe kudin tsohuwa Yan gidan Suka samu Mama Suka zo Suka tasa ta gaba lallai sai an biya su kudin me daddawa Suka kwace karamar Wayar Mama tare da siyar da ita dubu hudu Suka dauke dubu Uku dubu Daya Suka jefawa Mama canjinta,ita kanta Mama wahala ta isheta baza ta iya ba gashi lokaci Yana ta tafiya haka ta hado komatsanta ta dawo ta tafi gidan su Siyama tana rokon Kawu yasa baki Shehu ya maidata wallahi ta gane kuskurenta baza ta sake ba,Kawu yace ai Kinga irinta yanzu gashi kalleki dan girman Allah kin dawo sai kace dodanniya ,kin ganki Kuwa sai kace horror ba kyan gani da ace da dare ne na ganki ai sai na Suma idan nayi arba da kamanninki sabo da zance gamo nayi,Kawu ya gama Mata tatas sannan yaje ya samu Yan uwan Shehu ya lallabasu aka Kira Shehu aka zauna dashi akan yayi hakuri ya maida Mama,aka buga aka buga Shehu yace bai yarda ba,an rasa inda za ayi da Shehu har Mama ta kwashe kwana uku gidan su Siyama Shehu bai San da zamanta bama,sai da ta daidaici Sanda yake dawowa daga masallaci da sassafe da sauran duhu ta fice ai Kuwa taci sa'a ya dawo ta tare shi,zubewa tayi a kasa tace dan Allah Shehu ka yafe min wallahi bazan sake ba na tuba kayi hakuri dan girman Allah, Shehu ko kulata baiyi ba ta rike rigarsa tana kuka tana rokonsa ya fisge rigarsa ya shige gida bangaren Amarya,haka ta dawo jiki a sanyaye. Duk dangi da duk me fadawa Shehu yaji yaje wajensa akan Maganar maida Mama dakinta Shehu yaki landlady da kanta tayi Masa magana yayi hakuri ya dawo da Mama ko dan yaranta amma Shehu yace ba ruwanta wannan tsakaninsa da Mama ne dole ta kyale shi. Kawu ne yace yanzu shawara ta karshe ki tafi gidan Aslam ki roke shi yayiwa Shehu magana Indai Aslam ya sa baki to aurenki zai koma dai dai amma Indai ba Aslam ba Sai dai na fada Miki ta bature Sorry Sorry. Mama tsoro ya kamata tace Aslam din da ya tsane mu ko naje bazai kalleni ba karshe ma ya ci min mutunci Aslam baya kaunar mu ko daidai da kwayar zarra ne,ai yayi dai dai mene ne baku Yi Masa ba lokacin Yana auren yarki idan zaki je kije idan baza ki je ba to gobe ki bar min gida na gaji cewar Kawu,Aunty tace idan tsoro kike ji zan rakaki,Mama tace dan Allah ki rakani wallahi idan naje Ni kadai Aslam zai iya harbe ni da bindigarsa ni tsoronsa nake ji yanzu ban taba sanin Shu'umi bane sai da ya rabu da yata sai da ya rama abinda Muka Masa babu irin bakanta Mana zuciya da baiyi ba abin nan ya min ciwo karshen cin mutunci Aslam ya kashe kudi me yawan gaske aka Yi min kishiya kalli gidanta kalli namu ta fashe da kuka Aunty sai da abin ya bata dariya Aslam yayi dai dai cewar Aunty. Washe gari da Yamma Sunday Aslam Yana gida Yana zaune a center carpet Yana shan lemo Yana aiki a system Siyama kwance take a cinyarsa tayi dai dai da dan cikinta tana ta Wasa da botin din rigarsa Suka ji door bell sai da dan cikin Siyama ya motsa sakamakon karar da yaji ba zato,Siyama tace wash dan cikina zai fasa min ciki ni bana son karar nan tsoratani take yi yace Zan cireta to tunda baki so amma idan muna sama fa taya za muji knocking? ai idan na haihu sai a maida yace to ba damuwa,tashi ki bude kofa Siyama direct tace bazan iya ba wlh na gaji kayi hakuri,dariya yayi yace wannan ciki Ina ganin ta kaina da shi,tashi to na bude Siyama tace bazan iya ba dan Allah karka tashi naji dadin kwanciyar nan Allah kace su shigo mana,Aslam yace yau baza kiji kunyar ba kenan? Tace ko Kawu ne sai dai yayi hakuri bazan tashi ba,da Kansa yace ku shigo Aunty ta bude kofa tare da shigowa bayanta Mama ce sanye da Hijab,Aslam Yana ganin Mama ya daure Fuska tam ba mutunci,Siyama kuwa bata tashin ba kamar yanda ta fada,Aunty ce ta harareta ba shiri ta mike zaune a gajiye ba dankwali ma a kanta doguwar rigace a jikinta Yar kanti tace Aunty Sannu da zuwa,ta gaishe da Aunty ta gaisar da Mama ta amsa tana washe baki harda cewa Siyama Allah ya raba lafiya,Kitchen ta shiga ta kawo musu lemo da snacks ta zauna kusa da Aunty ko minti daya bata Yi ba ta kwanta a cinyar Aunty,Aunty tace ke dagani a kanki aka Fara ciki da kinzo waje ki kwantawa mutum a jiki,Siyama kin tashi tayi har Aslam ya gaida Aunty Kawai ko kallon Mama baiyi ba ya mike zai haura sama Aunty tace Aslam wajenka nazo fa,dawowa yayi ya zauna yace Aunty gani,Aunty tace wata Alfarma nazo nema wajenka dan Allah Aslam abinda Mama da Nusaiba Suka maka ka yafe musu kayi hakuri Allah ma Yana yafe Mana bare dan Adam ka yafe Mata,Mama ta karbe harda durkusawa a kasa dan Allah Aslam ka yafe min nasan munyi maka laifi ka yafe min dan Allah,Aslam ya kalleta shekeke bai ce kala ba,bazai yafe ba,Aunty tace kayi hakuri Aslam Allah Yana son bawa me hakuri da yafiya,ganin Aunty ce take ta rokonsa Kawai yace to amma fa bai ce ya yafe ba,Aunty taci gaba tace dama Shehu ne tunda ya saketa yau wajen watanta hudu yaki ya dawo da ita babu irin hakurin da bata bashi ba yaki yarda kowa a dangi da Yan Uwa har abokai sunje wajensa akan Maganar yaki amincewa,Kuma wlh ta tuba ta gane gaskiya a matsayinta na Yar uwa musulma akace yau Allah ya shiryata ai abin farin ciki ne ga mu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71