Chapter 44
Chapter 44
mota tun daga nesa ya bude ta ya shiga,Nusaiba kallon motar takeyi tabbas itace Suka Zo a cikinta tare da Siyama,Kawai kallon ikon Allah takeyi,motar Sufyan ta kalla wata kucakar mota wani takaici ya lullube ta haka ta bishi Suka shiga sai gida,Aslam kuwa mamaki yake yi dama Sufyan ne ya auri Nusaiba amma take Masa iyayi,dariya yayi wani farin ciki ya kama shi tabbas yanzu yasan Nusaiba tana cikin wani hali, cike da farin ciki ya koma gida Siyama tana Palo Yana shigowa tazo ta fada jikinsa tana furta Oyoyo ya dagata sama Yana murna,tace wannan murnarfa? Ya Shiga bata labarin abinda ya faru tsakaninsa da Nusaiba ai Siyama har kasa ta durkusa da hannu biyu ta kwaso Shoki yayi dariya ta sake kwasowa tana waka da baki tace yau Nusaiba ba bacci Yar banza,mijin nata ma ashe yaron mu ne,na Kara maka farin ciki? Yace da me Yana Murmushi ya manna ta a kirjinsa tace yau Ina Sallah na gama period,Aslam harda ihun murna yace ai yanzu ba jiran wani dare ya dauketa Kamar jaririya sai bedroom dinsa Yana cewa first Evening zamuyi ba first night ba Nusaiba Kuwa suna komawa bedroom Suka shiga shi Sufyan ma bai San matar Ogansa bace yace Wai lafiya Naga kin rasa sukuni sai gumi kike yi,Nusaiba mayafinta ta jefar ta zame dankwalinta ta jefar tana fifita da hannunta tana huci tace Aslam oganka tsohon mijina ne shine Wanda ka zuga ni na kaishi Kara ka zugani na karbi takardar sakina a hannunsa,Sufyan ya dora Hannu a Kai Yana wayyo Naga ta kaina Ogana ne na Shiga Uku aikina,Nusaiba tace wa yake ta wani aikinka yanzu ya fika kudi dama ashe da kudinsa,ya zanyi na Shiga dubu ma ba uku ba, gashi Siyama ta aure min miji ya zanyi,Sufyan baki ya bude yana kallon ikon Allah yace Ina ta aikina kina ta wani kudi baki da hankali Wai dama? Nusaiba tace dalla karka dameni mafitata nake hangowa,Sufyan mamaki ya kashe shi yace amma ke butulu ce baki San arziki ba,Iyayena nake hanawa ci da Sha sabo dake sabo da ke na kasa tara komai,Sai kayi Kuma cewar Nusaiba,sai nayi fa Kika ce? ta duro ashar tace burar.....kafin ta rufe baki mari taji ta ko ina,daina gani tayi na wani lokaci ya nade hannun riga ya hau jibgarta Kamar ya samu katon gardi tana ihu nan take idonta ya kakkafe ya juye numfashinta ya koma sama sama sai ta Fara furzo da jini ta bakinta amma Sufyan ko asibiti bai kaita ba sai da Allah ya taimaketa numfashinta ya dawo dai dai ta kasa tashi sabo da dukan data ci sai Jan jiki da Haka ta jingina jikin bed tana cewa ni ka sakeni wallahi wajen Tsohon mijina Zan koma ga me kudin gaske,Tsaki Sufyan ya ja sabo da zai iya kisan Kai ya fice ya barta a gidan tana ta tunanin kudin Aslam Yaya za ayi ta koma wajensa. Affan kuwa kyale Raudah yayi sai da aka kwashe kwana uku ya tabbata ta huce sannan ya sameta a compound zata fita ya tareta yace Raudah ta,Baki ta turo gaba,yace my Life, Mene ta furta yace dan Allah kiyi hakuri,wa Zan so in bake ba,Ina nuna Miki cewar ke kadai nake da,kece kadai a zuciyata,ki rage kishin nan My life tsohuwar budurwata ce fa me zanyi da ita,Raudah tace sau Nawa kuke komawa wajen tsofaffin budurwarku kuce ai ita kuka Fara so baku mantawa da juna,Banda ni to Ni ai na baki labarin abinda Suka min ta ya Zan koma wajenta ai da na cika marar zuciya,Kiyi hakuri ba laifina bane,Raudah ta kalle shi tayi missing dinsa tace idan na sake ganin wata tazo wajenka duk abinda na maka Kai ka jiyo,Affan yace ae ki mare ni ma,Murmushi tayi tace ko da kudi ai ban iya marinka,key din motar ya karba yace muje na kaiki Office,Kar ka ja min a wajen aikin nan namu akwai Yan mata,ke Kam kishi ya Miki yawa,tace ya zama dole ai indai akanka ne,Key din ta kwace ta Shige mota tace da kaina zanje ta Shige mota taja ta tafi tana Murmushi tare da dago Masa Hannu. Aisha Kuwa babban abokin Farook ta kira tana rokonsa ya taimaka ya yiwa Farook magana,bayan kwana Daya ya samu Farook ai Kuwa Farook ya Masa kaca kaca Indai akan Aisha ne yaki saurarar kowa har wasu abokan sun Masa magana yace ba ruwan su,idan ta kirashi baya dagawa aikinsa yake kawai yana Kara gyara gidansa sosai gidan yayi mugun kyau sai da ya gama komai,Aisha har ta cire rai ma ta hakura taci gaba da zawarcinta tana daukan wanka Kai ka rantse bata taba aure ba tayi kyau da kiba haskenta ya dawo,tsohon mijinta Yana ganinta ya dawo biko Yana so ya maidata Taki yarda tayi Masa fata fata wasu mazan dama lafiyar mace suke wa,da sun ganta fes sai su dawo idan ta koma Suka lalata sai su koreta,tana zaune da Yamma yaro ya shigo yace Aisha tazo inji Farooq,Kamar a mafarki haka taji bata yarda ba ma shine,Mamanta sai Murna take Yi tace maza tashi ga dan Albarka nan ya dawo da Kansa ya huce,Aisha tace maybe ma ba shine ba,shine Inshaallah cewar Mama,Aisha ta gyara ta canja Kaya harda kwalliya sannan ta fita ta ganshi a dalleliyar mota sabuwa ya fito Yana jikin motar, Aisha ta karasa tana Masa Sannu da zuwa ya amsa da sakin fuska yace zuwa nayi naji idan kin shirya komawa gidana ko me haihuwar kike jira? Dan Allah Farooq ka daina zancen nan kayi hakuri ka yafe min nayi kuskure Kuma Inshaallah Zan gyara baza ta sake faruwa ba,Farooq yace ai kin ci mun mutunci Aisha kin nuna min iyaka ta,ko a mafarki ban taba zaton Zaki min haka ba,kayi hakuri dai nace yace munyi magana da Baba yace next week za a daura Mana wani auren shine nace bari na tambayeki naji,tace ba matsala na shirya,daga Haka suka fara hira tace kasan kawata Sayyah ko? Yace tace ai dana fito ta dinga cewa Kar na koma gidanka ashe bata kaunarmu,Haka ma fa Kawu Jinjiri Dan uwan Baba ka gane shi ai? Farooq yace ae tace ai ya dinga zuga Mama Wai Kar na koma gidanka,Farooq yace dama nasan baya kaunata tun auren mu na farko cewa yayi ma ni mayaudari ne a kula Dani ai daina gaishe shi zanyi,Wai kawarki Naja'atu ce ta ganni taki kulani tunaninta mun rabu kenan to ta Allah ba tasu ba,Mata da miji sai Allah shi yasa ko mene ya faru karka tofa zancenka a ciki duk Sanda Suka shirya to sai sun fadawa juna waye yake son su waye kuma baya son su Kai da ka shiga fadan karshe Kaine da kunya zasu koma su hade kansu. Nusaiba washe gari da katon rauninta a kumatu tazo gidansu ko izinin Sufyan bata nema ba,Mama ta ganta ta shigo tana kuka jikinta duk rauni,Shehu Kuwa ko baki bai sa musu ba bai Kuma tambaya me ya faru ba,Mama tace lafiya Nusaiba,tana kuka tace ta Kare min Mama,na gama yawo wash Ina Zan sa kaina,mutuwa zanyi,Mama tace Allah ya kiyaye, Mama gwara na mutu na huta Kawai bakin ciki ne zai kashe ni wash Allah tana kuka sosai,Mama ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71