Skip to content

Chapter 15

Chapter 15

AURENMU Book One Complete Hausa Novel 1,239 words 0 views Progress saved
Download Book

ta fada Saman bed bata san da mutum ba ta manta jikinta ya mutu Affan Yana bacci yaji jiki me laushi ya fado Kansa Tashi yayi da sauri yaga itace tana shigewa jikinsa da sauri ya dirga kasa daga bed din har zai kwanta a kasa ya tuna shi fa guy ne baya kazanta Tsaki ya ja yabi ta window ya koma dakinsa yace aikin banza warin balaga takeyi ma Yana karkade jikinsa harda shinshina inda ta fado Masa a jiki yace kaji ko warinta ya manne min a jiki irin wannan warin sai na balaga yanzu ma ta Fara balaga na rainata ma banza ta gyara min daki kwadayayya ta cinye min kazata ya furta tare da fadawa saman bed dinsa ya kwanta Kiran Sallah yaji an kwala yace ta cuceni ban karasa baccina ba ya tashi ya daura Alwala ya wuce masallaci yana doro da carbi a hannunsa Kalar jallabiyarsa kullum ko masallaci zai je carbinsa ma toomatch yake da carbi da kayansa carbinsa sunfi kala hamsim ko wanne Kaya da Kalar carbinsa ana taku dai dai ya shiga masallacin unguwar, Liman ya sanshi Yana shigowa zaka ji kamshinsa Yana bawa liman dariya sai dai Yana birge mutane duk gayunsa Sallah a jam'i kullum ba fashi ko wacce Sallah har sun Saba da liman da duk wani me zuwa masallacin. Sai da aka idar da Sallah Affan ya daga hannu sama Yana Addua Allah ka azurtani,Allah ka bani kudi....kudi ya Allah na halak...Liman yace samari barka da asuba Affan yace Morning liman how are you? Dariya liman yayi yace Alhmdllh, Affan ya mike tsaye yace lafiya dai liman muyi Maganar a tsaye sabo da rigata zata yamutse ka ganta ta Sha guga bana so ta yamutse na tafi hanya a haka,liman ya zaro Ido yace asuba ce fa yaro da sauran duhu wa zai ganka,Sabo da jin dadin kaina ai ni Zan kalli kaina cewar Affan,Liman ya jinjina kai Yace baka da aure ne? Affan yace wuuu Ni aure rufa min asiri da yanzu Ina nan hankali a tashe Ni da cikakken bacci munyi hannun riga,Liman Murmushi yayi yace kaga Kuma da zaka Yi auren sai kafi haka nutsuwa,Affan yace to nifa gaskiya bana son aure yanzu mace ta dameni da kudin cefane kaina ma da kyar nake rikewa,Liman yayi dariya yace baka da budurwa saurayi kamarka kyakyawa da Kai haka kowa ya ganka yaga Namiji irin Kalar da Mata ke yayi,Affan ya shafa sajensa yace ba ruwana haka Kawai soyayya yanzu sai da kudi inje in tari budurwa bani da abin bata ta ci min mutunci,Liman me kudi ne na gaske yace kaje ka kula ko wace Indai da aure kake sonta Ni Kuma ko nawa zaka Bata Yar hidimar Mata dai Zan dinga baka har muga abinda Allah zaiyi, Affan yace to yaji samun kudi yace dama Ina da budurwa Ina sonta fada mukayi akan kudin anko tana so na za ayi biki na kasa siya Mata anko kunya tasa da kaina na fece,Liman yace tayi aure ko bata Yi ba? Bata Yi aure ba jirana takeyi Kawai Liman yace ka koma ka Bata hakuri ku daidaita Yar hidimar Mata dai Zan dinga baka har a tsaida Maganar aure ya kamata ace kana da aure bai dace mutum me addini irinka ba ka zauna haka Kuma muna limamai mu zuba muku Ido bayan Allah ya hore Mana yanda zamu tallafeku, Affan yayi godiya ya fice Yana murna a ransa wurin samun kudi ya samu shi Kam Yana cewa Allah na gode ma ka amsa Addua ta sai ta fada Kan liman. Kwanan Nusaiba biyu a daki a kulle Aslam ya kulleta yace sai ta fito Masa da motarsa abinci ma Dan kadan yake Dan zubawa ya Mika mata,tana ta kuka ta dinga Kiran Mama a waya,ba shiri Mama ta sauka a kofar gidan Charity tana bakin kofar da aka kulle Nusaiba tace ki fito Masa da motarsa a zauna lafiya,Nusaiba tace sai naci uwarki shegiya munafuka,Aslam Yana gidan yaji ana bubbuga gate yaje ya bude yaga mama ce ta shigo tana karewa gidan kallo tace Ina kudinka? Ina motocinka makaryacin banza dama karya kaje kake Mana ka jefa yata a masifar talauci,Aslam yace kije ki fadawa yarki ta fito min da motata,Mama ta kalle shi tace butulu wato babu mutunci ba girmamawa Aslam bai kulata ba suka shiga ciki yasa key ya Bude dakin Daya kulle Nusaiba Yana tsaye ya tare Hanya Mama ta shiga tana shiga ya maida kofa ya datse ya kulle su tare a dakin yace ku fito min da motata na fada muku,Mama ta zaro ido tace dama haka yake baida mutunci,Nusaiba tana hawaye tace wlh Mama zai kashe mu Yana da bindiga,Mama tace kwantar da hankalinki yanzu Ina motar? tace na siyar da ita ko kudin ma ban karba ba ya kulle ni,a jikin kofar Mama ta tsaya tace dan Allah surukina ka Bude mu sai muje a karbo maka motarka,Aslam ya kalli Charity dake sanye da Riga da skert na Atamfa wasu kodaddu yace wlh mutanen nan sun maidani wani banza,tunaninsu Banda hankali, charity tace yo ai Basu san da hankalinka bane basu san Kai cikakken Namiji bane sai yanzu,Aslam yace dan Allah? Charity tace Allah,yanzu ni cikakken Namiji ne? Ae sosai yanzu na tabbatar Amma da ka zauna Kamar solobuyo,Murmushi Aslam yayi yace Ni kaina sai najini wani na sake girma yanzu, Charity tace ah ai sai yanzu ni kaina na ganka kato,yace haba,? Tace Allah da karami nake ganinka, dariya sukayi Siyama tace Kara sa key na uku a fito da mota,Aslam ya bubbuga kofa gam gam hankalin su Nusaiba ya sake tashi yace a fito da mota,abinda zai muku zakuyi mamaki idan baku fito da mota ba cewar Charity tana taya Aslam Kamar kanwarsa. Sai zuwa Safiya Aslam ya Bude kofa zai Basu abinci Nusaiba ta kwada Masa tsinin takalmi choge Nan take ya dafe Kai ya Fadi kasa a sume ga Charity bata kusa da gudu Nusaiba da Mama Suka fice daga gidan suka tafi wurin siyar da motoci zasu karbi kudi babu Wanda ya karbi mota ba alamarsa Suka tambayar duniya akace ba a sanshi ba Ashe Dan damfara ne barawon mota Kuma ya gudu da mota,Nusaiba sai da ta Fadi har kasa sabo da kudin ta gama kasafin su,ba kunya suka tashi Suka koma gidan Aslam,lokacin Charity ta shigo ta kwala ihu ganinsa a kwance jini na zuba ta Kansa da gudu ta fita ta samo wasu maza biyu Suka taimaka Mata aka sashi a mota taxi zuwa asibiti,Allah yasa Babu matsalar kirki dressing Suka Masa bayan ya farfado suka dawo gida Kansa nade da bandage Charity tana Masa Sannu sannan tana bashi hakuri har Maman Nusaiba ta shigo da gudu tana kuka tace Nusaiba ce ta Sume,Siyama ta rude ta fita taga Nusaiba a sume tayi suman karya sun hada wayo,Aslam ya fito shima da Kansa ya dauki Nusaiba Kamar bai gano su ba ya shigar da ita bedroom ya kulle ya sake sa key yace sai ta fito min da motata,Mama da tana murna Aslam ya yarda da karyar su, yace Mama tun kafin na dakko bindiga ki bar min gida,Mama da gudu ta fice daga gidan,Charity tace dan Allah kayi hakuri

Table of Contents

Chapters

71 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71