Chapter 6
Chapter 6
maganin tsafinsu, Haka aka dinga zuwa tayasu murna har suka dawo bakin tallan su. Raudat ce ta dawo daga Office ta fito da ledar kayan makulashenta Affan ya fito zai tafi Neman kudi ko zai samu,Tsaki ta Masa tace kullum mutum sai fita kullum amma kudin haya ya kasa biya,kallonta yayi yace you are very lucky yanzu fita zanyi Ina da aikin yi da yau sai kin gane kurenki ya juya ya tafi abinsa,Yana fita wani kamfani yaje hadadde ya tambaya Oga yazo Kuwa? Manager yace bai Zo ba yayi tafiya jiya yace Dubu dari biyar zaka bani ka fada Masa,Manager jiki na rawa ya bawa Affan dubu dari Uku ya tafi,Affan kudin haya ya biya ya siyo kayan abinci da sababbin Kaya kala kala kanana da shaddoji da yadika harda takalma,Sai ganin Affan suke Yi Yana shiga ya fita cikin Kaya masu kyau,Raudat tace Amma Dan fashi ne Kai ba a sani ba da alama sana'a tayi kyau an kwaci kudin wani,Affan yace ke da kike karuwanci budurwa me zaman kanta kowa ya ji labari ai yasan karuwanci kikeyi motar ma mun San waye ya siya Sugar Daddy ne ya Gama tabeki Ina tausayawa Wanda zai aureki Yana nan zai ta wahala akanki sai ya aura yaji ya Sha wata mahaukaciyar corner kinji kunya,baza ki iya hakura da talaucinku ba,Raudat taji cin mutuncin yayi yawa ta fashe da kuka yace ai baki ga komai ba ma Sai an Miki dukan tsiya an zagi iyayenki a bariki sannan Zaki San kin Shiga duniya am warning you ki koma gida yafi Miki mutunci,ga inda larabawa ya kamata su sakawa suna Shari,ai ke titin maza ce kowa bi yake abi ta Shari sittin a fito ta Shari Mansir ko mai kin bayar a waje,Raudat tace kaima ai kwarto ne,gidan wa Kika ji na taba haurawa? Allah ya Isa ta furta tare da shigewa part dinta ya dinga dariya yace ki fito muyi mana matsoraciya yaja Tsaki ya shige bangarensa shima. Aisha matsawa tayi sai Farooq ya saketa sabo da haihuwa,Farooq yace wlh Indai akan laifin da nake Miki ne na daina Aisha na tuba bazan sake bata Miki rai ba yanzu zamu zauna lafiya Ina sonki dan Allah kiyi Hakuri, Aisha tace ba akan fada bane ko wanne ma'aurata Haka suke fada kullum Kawai ka sakeni haihuwa nake so na gaji da Zama da Kai, Farooq ya dafe Kai yace Aisha bakya tausayina? tace Kawai ka sakeni,kuka wiwi yakeyi ya buga ya raya taki yarda yaje ya sanar da iyayensa sunce tunda ta bukata ai ya halatta haihuwa take so ya barta ta tafi,Maman Aisha Kuwa har gida ta aikawa Iyayen Farooq Kan su sa a sakar Mata yarta haihuwa suke so,dole Farooq ya rubuta saki daya ya bawa Aisha tana kuka shima Yana kuka domin itama bata son barin gidan tana son mijinta amma son haihuwa ya rufe Mata Ido Haka ta hada kayanta Yana kallo tayi tafiyarta. Bayan wata daya Oga Aslam in Banda tunanin Nusaiba ba abinda yakeyi ya tambayi Mum dinsa ko Zata Gane su Sam Bata gane ba har can Taraba yaje ya zaga danginsa amma baiga ko masu Kama da su Nusaiba ba,ya shiga damuwa ba abinda yake tunawa sai Nusaiba amma bai gansu ba,yau ya fita gidan Abokinsa Yana driving yazo dai dai layin su Nusaiba sai ga Nusaiba ta dawo daga wani shago ta siyo garin kwaki,a gigice yayi parking a saitin Nusaiba tare da sauke Glass yace Hey,Nusaiba ta ganshi tabbas shine karyarsu ta Kare jikinta ya hau rawa Kar Kar, yace Kinga get in the car let's talk,shiga muyi magana,Nusaiba bata da zabi haka ta Bude gaban mota ta Shige tuni ta Fara kuka asirinsu ya tonu,kafin ma yayi magana tace dan Allah ka yafe Mana wlh dama ba Yan uwanku bane yunwa ce ta kaimu,dama haka mukeyi duk randa bamu Dora tukunya ba sai mu samu unguwa me kyau mu dinga shiga gidan mutane Watarana ma Yan polio muke cewa sai a bamu abinci mu ci mu koshi mu tafi wannan karon shine Muka fada gidanka ka kulle mu,Aslam yace oh my God da tun farko Kun fada min ai bazan sa a kulle ku ba Kun min karya kunwa kanku ya kuka Yi da iyayenku?Nusaiba ta bashi labari yayi dariya sosai a nan ta nuna Masa gidansu da gidan su Charity sannan ya tafi Yana ta farin ciki. Tun daga ranar yake zuwa gidan su Nusaiba Mama sai Murna takeyi Allah yasa ya auri Nusaibanta,gidansu ya samu aka sake Gina musu dakuna guda biyu ya Zama suna da dakuna Uku ya budewa Mama katon shago a layin Danta Ameer Yana Zama a ciki duk kannen Nusaiba ya canja musu school Mama ta koma bata da matsala suna babbar Sana'a idan Ameer ya tafi makaranta Mama ke Zama a shagon idan ya dawo sai ya karbeta,Har Nusaiba ta daina talla ya maidata school Allah Allah suke Aslam yace Yana son Nusaiba, Charity dai tana tallanta duk tasan taimakon da yayiwa su Nusaiba itama ya bawa Dauda kudi ya ja jari,Nusaiba an samu suturu masu tsada wanka take dauka sosai ta Zama Yar gayu yanzu sai ji da Kai takeyi ana haka Aslam ya sanar da Mum dinsa ya samu matar Aure, tace a satin Nan zata Zo Nigeria,Aslam yau driver ya kawo shi ya Sha wanka na daban Yana zuba kamshi cikin wani shadajjen yadi milk,Nusaiba ta fito suna tsaye a jikin motarsa yace kin San me yake tafe dani Kuwa Nusaiba,tace Ina jinka Allah Allah take ya furta,yace tunda na ganki naji Ina sonki a Raina Kuma Ina so na aureki da gaske nakeyi,Nusaiba tana ji tace ka turo manya ko gobe ma ba damuwa,mamaki yayi amma yaji dadi yace Inshaallah gobe Mum zata Zo idan tayi bincike Zan turo Manya ki fadawa Abba yayi nasa binciken,Nusaiba tace kyale Abba Indai Mama ta yarda ba matsala ba sai anyi bincike ba,ka Sanni na sanka mene a ciki,Aslam Yana ta mamaki dai haka,shi kuwa Shehu ana fada Masa ya shiga bincike Kuma ya samu Aslam mutumin kirki ne Dan manya Dan asali. Mum tana zuwa washe gari taje gidan su Nusaiba Kuma ta yaba da hankalinsu ba a dauki lokaci ba aka kawo kudin aure sannan aka saka rana wata Daya kacal,Mama harka ta bude itama kullum Shar zaka ganta da yaranta Shehu ya samu jari Babba sai harkarsa take dama baya iya ciyarwa, Charity tuni an Fara shirye shirye Charity gidansu na bulon siminti ko Ina a sumulmule su dan fi su Nusaiba danshi danshi,Nusaiba tana tashi fitar da anko ko shawarar Charity bata nema ba ta fito da leshi Dan dubu goma Sha biyar, Charity tace Haba Nusaiba kamar kin manta inda Muka taso ya rayuwarmu take kaf kawayenmu talakawa ne Yan talla ko ni da nake babbar kawarki a Ina Zan samo wannan kudin haka,Nusaiba ta yatsina fuska tace ke karki damu zansa my Love ya dinka Miki haka na fitar da anko biki ne na masu kudi wacce taga zata iya tayi wacce baza ta iya ba fine dama Mum dinsa Bata Jin dadi ba wata Dinner za ayi ba,dalla share zancen nan na baki labari nasan fa ana daura aure zamu tafi honey moon irin su
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71