Skip to content

Chapter 2

Chapter 2

AURENMU Book One Complete Hausa Novel 1,237 words 0 views Progress saved
Download Book

damu muna tare fa sai lokacin Mustapha ya saki ransa suka ci gaba da labarin duniya. Affan gida yazo da Niyyar shiga sai ga wani Mallam yasha babbar riga da rawani ya tsaida Affan yace Saurayi Innalillahi wa Innailayhirraju'un, masifa ta tunkaro ka,Mallam yaga Affan Kalar Naira ya dau wanka Kalar me kudi yace kana da makiya Alhaji wasu suna nan zasu sace maka mota,Affan ya bude baki yasan karya yake shi da baida mota,yace sannan makiyanka Yan uwanka ne sun Kai sunanka za a maka asiri kwana nan zaka rasa milliyoyin kudi a cikin dukiyarka,Affan ya sheke da dariya a ransa Shi da bai da ko sisi yanzu ma bashin dubu uku ya samo da kyar,a fili gigicewa yayi yace yanzu Mallam ya zanyi kenan? Me ya kamata ayi? Mallam farin ciki ya kamashi ya samu gara zai cuce shi,yace dubu dari zaka kawo ayi aiki me zafi a kansu,Farooq yace an gama bani Address din gidan naka yanzu banda kudi a hannuna,Nan take Mallam jiki na rawa yace ya bada address Affan ya wuce gida,Yana cikin palonsa dake estate din kowa bangarensa Palo da 2 Bedroom ne a hadadden Estate a haka ma Sai me kudi ko ma'aikata ke Kama gida a ciki da gate dinsu da komai kowa da part dinsa,Yana ta kora lemo da bread babu kayan abinci. Raudat ce tayi parking motarta ta iske Hajiya Mairo a compound kusa da part dinta turaruka ta Bata kyauta masu kyau,Mairo tana ta murna mugun shiri sukeyi da Raudat har abinci ma idan Mairo taga dama a part din Raudat take ci itama Raudat tana ci a wajen Mairo duk gidan tasu tazo daya suna morar juna,Raudat tace landlady wancan Kuwa ya biya kudin haya? baki Hajiya Mairo ta tabe tace yo mutumin banza Ina zai iya kullum sai wanka bako sisi na gaji da halinsa a gidan nan nawa kwana nan Zan kore shi,Raudat kasa kasa tace mene amfaninsa face kora ko dubu Hamsim bazai iya hadawa ba bare dubu dari biyu,Suna haka sai ga Affan ya fito ya dau uban wanka cikin kana nan Kaya Yana taku dai dai Yana takama ko kallonsu baiyi ba ya fice suka bishi da kallo cike da mamakin yanda yake da mugun gadara baida aiki sai wanka kullum cikin kamshi amma babu ko kobo. Wani kanti yaje inda suke siyayya kusa da gidansu Suka tafa da me kantin yace a wannan wanka haka Affan Ina zaka je ne? Affan yace tafiya zanyi Ina so zanje Abuja ne akwai wani business da nake ya zuba karya yace gashi ma kaga Atm dina yaki aiki,me kanti sabo da yasan Affan Yana Masa ciniki Yana ganinsa cikin kyakyawar shiga ya zaci me kudi ne yace gaskiya kana tafiye tafiye Oga ko yaushe a Hanya, Affan yace ya za ayi Harkar Business ai in kana Business ba zama yanzu ma bank Zan koma Ina so zanyi siyayya kudi yaki fita dan Allah zan karbi kaya idan na dawo daga tafiya sai na kawo ma kudin, nan take me shago yace ba damuwa komai normal ebi abinda kake so,Affan ya kwashi manyan manyan madarar gari su gwagwanin Milo kayan tea sosai ya hada sannan ya kwashi su tumatir din gongoni,shinkafa yasa ya auna Masa kwano biyar,wake,taliya, macaroni komai ya har su Mai da kwai sai da ya hada akayi Total aka rubuta a list din Yan bashi ya fita,Yana kaiwa gida ya zauna ya shirya girki me rai da lafiya yaci ya koshi sannan ya fito sai gidan Mallam Wanda ya karbi Address. Affan ba kudin mota a kafa ya dinga tafiya sai da yaci bakar wahala kafin ya Isa gidan Mallam Yana zuwa yaga gidan Mallam hadden gaske sama da kasa,bai Sha wahala ba aka kaishi har part din Mallam,Mallam Yana zaune shi da wani Yana fada Masa karya dan ya karbe Masa kudi,Bayan ya sallameshi Suka gaisa da Affan, Affan yace Mallam ka firgita ni shi yasa nazo da wuri kaganni sauri nakeyi zanyi tafiya yanzu ba kudi a hannuna Kuma tafiyar wani kudade Zan karbo shi yasa nazo yanzu ka bani dubu Hamsim kafin na dawo sai na baka dubu dari biyu ma kaci harda riba,Mallam Yana Jin Haka ya haukace zai samu kudi ba bata lokaci ya irgo kudi dubu Hamsim ya bawa Affan ,yayi godiya tare da cewa sai ya dawo ya fice,Yana fita yazo ya biya me shago kudin kayan abincinsa tas harda samun canji ya shiga harkarsa. Mallam Shuru Shuru Babu Affan ba labarinsa bai San Kuma inda zai ganshi ba,Affan yaci wanka cikin wani yadi me kyau Yana taku dai dai sai ga Raudat ta taso daga aiki ta tsaya kusa da shi tare da sauke glass tace Affan shigo na rage ma hanya Naga Kamar gida zaka je,cike da rashin mutunci yace ke kin Isa ki taimakeni,akan wannan banzar motar taki har kin Isa ki rage min Hanya ya juya da Niyyar tafiya Katsam sai yaga Mallam shi da wani suna ta magana juyawa yayi da sauri ya bude motar Raudat ya Shiga gaba taja mota suka tafi Babu Wanda ya kula wani,sai da Suka Yi nisa tace da kace baza ka shiga ba me yasa ka canja? Cikin bala'i yace to sabo da na Shiga motarki shine Zaki Raina min hankali motar ki din banza motarki din wofi,Parking Raudat tayi tace amma baka San mutunci ba fitar min a mota,Tsaki yaja ya Bude kofa ya fice tare da furta banzar mota bayan ma ba da kudin halak Kika siya ba maza ne Suka siya Miki Karuwar banza da kudin karauwanci Kika mallaki mota tunaninki bamu sani ba Alhaji Sanata ko dan majalisa ya siya Miki ya daki motar da kafa yaci gaba da tafiya cikin gadara,Raudat ce ta leko ta window tace mutumin da ya kasa biyan kudin gida talaka da Kai baza ka taba iya siyen mota irin tawa ba Never, wace zata kulaka a haka Kai a dole kyakyawa kana daukan wanka ba abinka ka iya sai siyen Kaya kana nan kayan ma duk na gwanjo ne ta fisgi mota taja gaba,yace stupid girl Wai ita me mota Allah ya kiyaye na shiga motar haram. Raudat yau da takaicin Affan ta dawo tana zuwa bayan taci abinci ta fito ta faki Ido kowa ta taka tsani tayi disconnecting wutar gidan Affan ta danna switch dinsa ta sakko ta koma gidanta,Yana dawowa ya kunna ko Ina duf babu wuta ya rasa dalili gashi gudun Landlady yake tana ganinsa zata ce ya biya ta kudin haya,shima Fitowa yayi Raudat tana ganinsa ta window tana ta kyalkyala dariya Yana dubawa yasan itace sai ya kunna nasa ya kashe nata wutar itama sai gata ta fito da masifa Affan kana neman masifa abinda kakeyi ka takura min a gidan nan Zan dauki mataki a kanka, Affan yace amma ke banza ce wawiya Naga alama so kike nace Ina sonki to wannan bazai Yi tasiri ba,nafi karfinki kije ki samu dai dai dake, me zanci da Kai me zaka iya siyawa matarka kudin gida ma ka kasa biya me zaka iya,Hajiya Mairo me gidan itace ta shigo da dalleliyar motarta ta fito tace Wai ku meke damunku ne baku da aiki sai fada a gidan nan me ya

Table of Contents

Chapters

71 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71