Chapter 29
Chapter 29
kudi dubu biyar yace gashi ki sa Kati bai San ko waya Bata da ita ba,Aslam ya kura musu Ido gashi Yana yiwa Sabeer masifa muje dalla malam Siyama kin karbar kudin tayi Affan yace mene haka Kuma bana so nayi kyauta a maida min,Siyama juyawa tayi Kawai ta Shige gida duk ta firgice ta tsorata, Affan baki ya tabe yaja motarsa ya wuce,Aslam tuni sun tafi. Siyama tana komawa gida tace kawu ya tafi Aunty na dawo Suka ce to sai bayan Isha Kya bamu labari tace to tare da fadawa dakinta ta kwanta akan katifarta ta fashe da kuka Wai Aslam ya ganta tana zance har da cewa na shiga Uku na shiga dubu tana rusa uban kuka Kamar wacce aka Mata mugun duka,Aunty ce taji kukanta ta fado dakin da gudu tana cewa me Zan gani Siyama lafiya? Saurayin ne yaci Miki mutunci ko me? Marinki yayi? Siyama tace shike nan tawa ta Kare na gama yawo ta sake sakin kuka tana shesheka tace Aslam ne Aslam,Aunty tace mutuwa yayi? Siyama tace Aunty Aslam Aunty wash...shike nan Aunty Aslam ya kamani ya ganni Ina zance Innalillahi, Subhannallahi,Ashahdu Allah ilaha illallah ta Dora Hannu aka tace Aslam kuru kuru ya ganni,Aunty Tsaki ta ja tace ke dalla rufe Mana baki mahaukaciya amma dai sonsa kike dama ko? Charity tace Mijin Nusaiban haba Aunty mijin kawata kuma abin kunya ne ai,Aunty tace to rufe Mana baki sakarya, Kawai ki Fara Mana kuka sabo da rashin aikin yi,Siyama tagumi ta zuba tana goge hawaye ta kasa tashi Sam sabo da jimami. Aslam kuwa suna tafiya Sabeer yace zamuje park din? da masifa ya furta ka kaini gida Malam Babu Maganar park din banza kaini gida gwara nayi tunani me kyau na huta,ka fasa zuw...bazan je ba karka dameni ya furta da masifa,Sabeer yace kaga nifa bani naje zance wajen Yarinyar Nan ba bare kace,to ni nace maka naji haushinta ne Ina ruwana ta kula maza dubu ma Ina ruwana,Sabeer dariya kawai yayi Yana tukinsa yace tana da saurayinta kana ganinsa dai sharr da shi gwara ka auri Nabeela, Allah ya kiyaye na auri sakin wawa Nima fa sakin wawan nayiwa wata nasan me tayiwa mijinta ya saketa ba duk bazawara ce ta kirki ba gwara wacce ma mijinta ya mutu amma Wanda ake sakowa na tsorata da su wa yasan me Suka aikata aka sake su,Sabeer yace wallahi akwai Wanda laifin mazajensu ne,Aslam yace ae naji naji bana so bata min ba ni da wata kafarta a gwame,nufinka idan ta sa min riga da wando haka Zan na ganin Ball leg dinta sun kantare,Sabeer dariya Kamar me yace yaushe kaga kafafunta maye yanzu har ka San tana da Ball leg? Kwarai kuwa ko zaka ce karya ne? Sabeer yace tabbas wlh ba musu lallai mutumin auren Nusaiba ya sake gogar dakai da ko kallon Mata baka yi,Aslam yace dan Allah ka kyaleni bana son surutun me gwamammiyar kafa dai bana Yi karka sake min zancenta ana Neman macen kirki kana kawo min bage,Sabeer yace sorry na Siyama yana dariya,ance maka son Siyama nake Yi wai nifa ban shirya aure ba ku sani ma ya furta Yana turo jajayen lips dinsa yace kaini wajen Mum ma gwara na ga uwata na huta da duk wata ya mace. Wajen Mum suka tafi can Suka zauna har dare Mum har ta Fara damun Aslam cewar ka Nemo Mata ta gari Aslam gashi ma Kai naga Kamar baka da niyya Wanda hakan hatsari ne ga duk namijin da ya taba aure bai dace ya zauna ba Mata ba ka dinga dubawa kaji,to Aslam yace kawai. Affan kuwa akan idon Raudat ya shigo da motarsa gidan tana tsaye ta juya baya ita da Landlady suna hira ya wuce da mota abinsa Yana yin parking ya fito Raudat tana kallon inda yake fitowa,part dinsa ya Shiga da sauri,Raudat ta sauke ajiyar zuciya ta Shige part dinta ita ma,ai tana Shiga ciki taji suna tafawa da Sayyeed suna magana Affan yace Kai Kuma wannan tarkacen flask din da tire Ina ka samo su? Sayyeed yace ai baka sani ba budurwa nayi Raudat ce ta dinga Miko min ta window ashe windown ku daya, Affan yayi dariya yace Kai dalla ba sonka takeyi ba mutunci ne da ita Haka take da kirki ita tana ma da mijinta matar wani ce aiki ya kawota weekend take komawa gidanta, Sayyeed ya zaci da gaske ne yace eyya na hakura gwara da ka fada min,ai Kuwa tana da kirki kalli girki ya shiga budewa Affan Yana kallo,yace ta hutar Dani dama da tunaninka na dawo na nema maka abinci,Raudat tana jinsu suka hau Hira Sayyeed har yayi wanka Affan yace ko zamu fasa gari ne?Raudat ta Riga su fitowa ta tsaya kamar zata Shiga motarta,Affan ya fito tare da Sayyeed,Affan yace Hajiya Aunty fita zakiyi ne? Tace ae Ina son fita amma bana son driving din na gaji,Affan yace muje to Mana na kaiki ni Naga yanda Kika karrama abokina na gode fa,Hmm ba komai cewar Raudat zata Shiga Bayan motar Affan yace shigo gaba Sayyeed sai ya Shiga baya shi,Sayyeed ya Bude baki matar wani Kuma Affan yace Kawai dai Sayyeed ya Shiga Bayan mota,Affan ya tashi mota Suka wuce Raudat bata San inda zata je ba,Affan yace Ina za a kaiki? tunawa tayi da wata kawarta da suke aiki waje daya wata Hafsat ta nuna Masa gidan har ya kaita kofar gidan Hafsa yace yaushe za a zo a daukeki? Raudat tace sai 10pm,Affan ya zaro Ido yace haka Kawai ki zauna a gidan wata matar tana da aure fa har goman dare ki takura musu idan mijinta Yana son yayi Yar harka fa gaskiya bai dace ba,Raudat tana dariya tace to karfe nawa Zaka dawo? Yace gaskiya 8pm Haba kina mace a dinga sakaki dake bazai yuwu ba,To sai ka dawo cewar Raudat yace yawwa 8pm ki shirya har ta juya yace Aunty ta juyo da sauri yace ba ruwanki da mijinta sawunki a likkafa ki dauke idonki dan mazan yanzu ba mutunci gare su ba wlh sai yace Yana sonki ato ki kula Kar azo kawa ta nada Miki duka a gidanta irinku Aunty sai kusa mijin wata ya kifa yaci ta ka,Dariya Raudat keyi yace gaskiya nake fada Miki ki Kama kanki ba ruwanki da mazan wasu,Raudat tace to sai dai ka dawo ta juya ta Shige tana dariya,Affan sai da ya daina ganinta sannan yace da Sayyeed Kai katon gardi dawo gaba Kuma wallahi karka sake muna kwance ko yatsanka ya taba min fatata nasan baka iya kwanciya ba na tsani jikin Namiji ya taba Ni da ace dai macece aha wannan is okay Sayyeed ya koma gaba yace nasan halinka ni a Palo ma Zan kwana Kuma kaji tsoron Allah kana kula matar wani,Affan yace ai mun Saba da ita, Sayyeed yace naga alama dalla karka Raina min hankali let's go,Suka tafi yawonsu. Tun kafin 8pm Suka koma gida da kayan ciye ciyensu ya bar Sayyeed ya sake zuba wankan 3qtr da riga me gajeren hannu farare ya tafi dakko Raudat,8pm dot yayi horn dit dit Raudat taji ta shirya tare da yiwa Hafsat Sallama,Hafsat ta rakota tare da mijinta har mota ta Mika
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71