Skip to content

Chapter 1

Chapter 1

AURENMU Book One Complete Hausa Novel 1,260 words 0 views Progress saved
Download Book

[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️ COPY BY ZAINAB BUTALAWA 1-5 Official By AsmaBaffa Page naki ne UMMU LATEEPHA Biye yake da ita a baya tana gaba Yana fada itama tana Masifa tare da furta bar maka gidanka zanyi,ya furta ki bar gidan Mana sai me nima haka nake so ki tafi dama kin isheni,ae naji tafiya zanyi suka shiga bedroom suna masifa,cikin akwatinanta ta dakko daya ta bude sannan ta bude ma'adanar kayanta ta Fara fito da kayanta,Hannu yasa tare da fisge wani leshi yace wannan ai ba kayanki bane Rannan na siya Miki da kika zo gidan nan dama ba a kawoki da kayan kirki ba,au haka kace yes wannan tsohuwar atamfar taki ce ya furta tare da fito Mata da ita,ta sake dakko wata shadda yace ajiyeta maidata ai baki zo da ita ba idan kin tuna last year na dinka Miki ita,ajiyewa tayi ta zabo Wanda tazo dasu kala biyu, fannin takalma tazo ta dauki wani white flat yace maza ajiye shi ni na siya Miki,tace na manta au Kaine fa ka siya,na tuna Miki yau to yace, amma Farooq baka da kirki amma ba komai,Farooq yace ae naji,cikin fushi ta jawo akwatinta ta fito Yana cewa itama akwatin mutunci na miki amma wlh da sai dai ki zuba kayanki a Leda,Aisha tace ni ka daina matsowa kusa dani bana bukatar taimakonka,yace wayyo yarinya Allah ya kiyaye na taimakeki rakaki zanyi Sabo da na kulle gidana Kuma karki sake kice Zaki dawo gidana daga yau,Aisha tace me Zan dawo nayi a wannan banzan gidan naka. A Palo ta tsaya tana karewa palon kallo tana son gidan bata son barin gidan yace malama ki tafi ke nake jira tana kallon gidan tace karka taba min jaka karma kace zaka taimakeni kace zaka daukar min jaka bana so karka soma bana so,cikin masifa shima yace Allah ya kiyaye na daukar miki jaka ki daina kallar min gida ki Kara gaba,Ina kaga gidan wannan gidan nasan komai yayanka ne ya siya maka Ina kaga kudin gina gida,ae naji jeki bana son ganinki,Aisha sabo da maita sai kallon gidan takeyi karshe cikin fushi da azama ta fisgi akwatinta zata fita sai suka ji ana Kwankwasa palonsu,juna suka kalla sai Suka ji muryar Babar Farooq tana cewa ko ba kowa ne? Farooq da sauri yace gani nan Muna nan,da sauri ya dauki akwatin Aisha yace maza koma ciki Umma ce,da gudu ta dauki akwatinta ta koma bedroom,Shi Kuma kofar ya bude Mata cike da ladabi ya furta Sannu da zuwa Umma,da fara'a tace yawwa Farooq Ina matar taka ne naji gidan shuru? Farooq yace tana nan aiki ma ta gama yanzu ai Yar Albarka ce akwaita da kwazo,Umma tace Kai Kam kayi dace ba irin Dan uwanka ba gashi Kuna zamanku lfy, Aisha ya kwalawa Kira ta fito harda saka katon Hijab har kasa ta gaida da Umma tace bari na kawo Miki ruwa,a'a barshi ma tafiya zanyi dan Allah ku zauna lafiya duk da nasan Kuna kokari ba a Jin kanku Kuna zamanku lafiya kowa ya sheda,Farooq yace to Mene amfanin mace da miji su dinga fada ai babu amfani,Aisha ma tace shi yasa Muka fahimci juna mu ko fada bama yi bama cacar baki, Shima Farooq yace yanzu Umma ai ba a yayin fada mu bamu San ma ma'aurata suna fada ba sai dai muji labari a makwafta,Umma tace ai ni haka nake so Allah ya Kara zaunar daku lfy ta mike suna cewa ameen ta tafi,tana tafiya Suka gallawa juna harara,Farooq yace dalla daina kallona mutuniyar banza marar tarbiyya,Aisha tace tafiya zanyi gidan Ubana dama,Farooq yace ba inda Zaki je baki Isa ba na fasa barinki ki tafi kudi na biya na aureki,gidanku son abin duniyarku ya baci,tunda na fara neman aurenki ake rokata kudi,sannan Sadakin da akace na biya wajen aurenki iyayenki ai da tsada Suka sa min, ko ke lokacin da na fada Miki sai da kika tsorata,sannan ai caka min akayi cewa Kika yi ke virgin ce da nazo na shige ki wuuufff na wuce ciki ba abinda ya tareni sai kace rijiya haka na fada cikin ki,harda cewa virgin ce amma a haka na hakura na zauna dake sabo da haka ba inda Zaki je kina nan gidan,Aisha kuka ta saki tace wlh Farooq Allah sai ya saka min sharrin daka min ni zaka cewa ba virgin ba Allah Yana ganinka ta fashe da kuka me tsuma zuciya,Tsaki yaja ya koma Palo yace ba inda Zaki je Ina gidan Nan banza shashasha. kwan....gwan...gwan taji ana uban buga Mata kofa,lemo ne a hannun na ina Sha uban kida na tashi,kofa na bude kyakyawan Matashin ne ya dauki wanka cikin kana Nan kaya farin Jean da riga sky cike da bala'i yace dalla malama kin cika Mana gida da kida ko ke kadai ce a gidan nan, da masifa nima kyakyawar budurwa dani nace ai kudin haya na biya Kai fa nasan sirrin komai baka biya kudin haya ba sai uban daukan wanka baka da sisi,Jin na fara tona Masa asiri yasan bai biya sisi ba yayi mukus ya juya gwiwarsa tayi sanyi ihu na Masa wooo yaji kunya ba uwar da ya sani Sai wanka shi a dole gaye na ja tsaki tare da komawa ciki,shi kuwa dakinsa ya koma ya Fara shiri Yana kallon Kansa a mudubi yace gaskiya na hadu zanyi cizo,ya dauki lokaci me tsawon gaske Yana kallon Kansa kafin ya fito Yana taku dai dai. Lokacin nazo fita a motata ja me kyau ko kallona baiyi ba ya tako ya wuceni a bakin gate Yana Shirin barin gidan,glass na sauke a hankali cikin nutsuwa na furta dan Allah Affan taimaka ka bude min gate,kallona yayi shekeke da bala'i yace kin ga nifa ba sa'anki bane,Kawai Dan kin mallaki wannan banzar motar kina tunanin ke wata ishashiya ce me kike da shi wannan har mota ce Yana magana Yana dukan motar da hannunsa,stop insulting my car,mota hadaddiya zaka dinga zagi,Tsaki yaja yace kinci sa'a Ina da appointment fita zanyi da kin gane kurenki ya juya yaci gaba da tafiya da gadara,haka ka iya kullum kace kana da Appointment kuma har Yanzu bama gani a kasa kullum jiya iyau na furta ina Jan tsaki na Bude motata na fito tare da bude gate na fita Office Affan gidan Abokinsa ya wuce Direct Mustapha Yana aiki a ministry of Environment,Shi kuwa Affan baya aikin komai sai dai buga buga idan ya samu ya siyi kayan daukan wanka kudin gidan haya ma a Estate din ya kasa biya duk lokaci in yazo sai anyi fada da shi,suna Palon Mustapha me kyau a zaune Mustapha yace me ya kawoka gidana ne nasan sai da dalili,Yace zuwa nayi ka ranta min dubu biyar bani da kudin abinci komai na kayan abinci na ya Kare, Mustapha yace dama na sani to gaskiya bani da kudi, Affan yace please ka taimaka min Kai fa abokina ne na gaske common 5k nasan baza ka rasa ba, Mustapha ba a son ransa ba yace ya zanyi da Kai kazo a abokina bai kamata nayi baboki irinka ba amma ya zanyi Zan baka 3k Amma ka tattabar ka biyani na gaji bashin da nake binka yayi yawa,Affan Yana murna yace karka

Table of Contents

Chapters

71 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71