Chapter 40
Chapter 40
ya gaji. Aisha wannan karon tana hakurin dannewa basa fada da Mahaifiyarta suna zaune lafiya Sabo da sunyi nadama Matukar gaske,aikin gidan kaf kusan Aisha ke yinsa,tana son cikin nan nata duk da uban dan baya so amma ji takeyi da cikin nan,har tayi kyau ta Fara murmurewa, Farooq yayi murnar fitowar Aisha amma yaji haushi da aka ce tana da cikin wani ba nasa ba,Aisha tana ta murna zata samu danta ko ya Kawai tana wanke kayanta dana Ummanta ta Fara zubar da jini,ta tsorata sosai Suka tafi asibiti har da Baban Aisha aka je, lokacin cikin Aisha ya zube gaba Daya har ma sai da aka Mata wankin ciki,sabo da taji jiki kwanan su biyu a asibiti sannan suka dawo gida taci kuka ta koshi sai da Babanta yayi ta Mata nasiha sannan ta hakura,Ciki na zubewa mutane munafukai suka kaiwa Farooq gulmar cikin Aisha ya zube ta wani bangaren yaji Mata ciwo ta wani bangaren yaji Dadi. Bangaren Siyama kuwa sati Daya Kawai dangi aka fadawa Suma kawu yace ba taro Yan daurin aure ne Kawai zasu Zo,Dangin uwar Babar Siyama ma haka ya fada musu,Babu Wanda aka ce yazo sai iya maza Yan Uwa,shima Aslam ya fadawa Mum, Mum tace amma nayi maka farin ciki son ai gwara ma haka ba sai da taron ba babu komai an gode amma duk da haka ayi order abinci a Kai musu su bawa danginsu Suma mu dai ta bangaren mu tunda dama wannan iftila'in ya fada maka dama bamu da Niyyar taro sai na Yan daurin aure Kawai Nan Suka Yi kulla kullarsu da Mum dinsa yanda baza suji kunya ba,Haka aka tura manya da kudin komai da komai ko Siyama bata sa rai da lefe ba,Aunty dai ta dage tana ta gyara yarta sannan tana zuwa gyaran jiki, Saura kwana uku biki aka kawo lefe sunyi mamaki akwatina goma cif Kaya na gani na fada ba abinda babu,aka dinga zuwa kallon lefen a unguwar,Maman Nusaiba taji labari ta kyalkyale da dariya tace dan karya ne haka yakeyi yanzu ana kaita zaice yaci bashin bank ba kudi sun shiga uku ta sake sakin dariya,Shehu yace kinyi asarar halinki ke dai Kam tir. Aslam ne ya fito tare da Siyama yazo zance Suka Yi kicibus da Nusaiba mijinta ya kawota a mota ya juya,Aslam bai ma ga ko motar ba lokacin yayi nisa tuni ya bar layin,Nusaiba ansha wanka kana ganinta kasan tana hutawa ko kallonta Aslam baiyi ba ta gefenta ya wuce, har da kallon Siyama tayi dariya tace an kusa cin bashin banki ki daina murna an kawo Miki akwati goma Nawa kusan guda ashirin ya kawo amma karshe a ya na kare da talaucinsa, Siyama tsaki taja,Aslam yaja hannun Siyama yace let's go My Heart Suka wuce,Nusaiba ta bisu da kallo tace a hau taxi lafiya nasu ko kalleta ba abin Kuma ya Mata mugun ciwo a rai wato Aslam Kamar ma bai taba saninta ba haka yake nuna Mata ta wuce gidansu dai tana takaici. AsmaBaffa [4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️ AUREN MU🛢️ 61-65 Official By AsmaBaffa Page nakuli ne Rukey Muaz Ana gobe daurin aure Siyama tasha gyara sai kamshi take zubawa Kawai ta Sha lalle,Kawayenta ta gayyata Zulfa'u,Sakna,Raihanatu da Nana sune Kawai a gidansu suke tayata Zama,sai bangaren Dangin mahaifiyarta Mata su biyar,sai bangaren dangin Aunty Mata su wurin goma haka bangaren Kawu da Mahaifin Siyama Suma sun kai goma gida ya cika tam duk da Kawu yace bazai taro ba dole sai da aka zo Masa,haka Aslam ya dinga dariya Jin Kawu yace bazai taro ba amma iya dangi sun cika gidan haka ya Aiko musu da kayan abinci shinkafa ta dafawa da danya ta tuwo,mangyada manja,Maggi iri iri,kayan Miya buhu biyu,su Alayyahu,kabewa, Albasa,Taliya macaroni komai sai da aka kawo da yawa su Aunty Suka dinga mamaki kamar me kudi haka ya aikowa da Kawu dubu dari biyu,ya bawa Aunty dubu hamsim haka Siyama ma ya Aiko Sabeer ya kawo Mata kasonta sai,Kawu ne yaga mutane sun cika gidan ya Kira Aunty gefe yace nace fa ba shagali ba biki ya akayi Yan Uwa Suka cika min gida to wlh babu wacce zata Kai Amarya ko wacce gobe ta bar min gida,Aunty tace to tunda an sanarwa Yan Uwa ai ba wacce zaka kora idan Kuma zaka iya bismillah,Kuma biki babu wacce aka yiwa aure ba dangi sabo da Haka itama Dole Yan uwanta suzo Amarya Kuma ba komai ango yazo ya dauki matarsa ai dai an daura aure ko to Alhmdllh,Kawu Yana magana kasa kasa Kar dangi suji yace Ni dai ba wacce na gayyata biki,Kai ka sani cewar Aunty ta juya ta koma suna ta girke girkensu Kuma ta gayyaci Yan unguwa Wanda suke mutunci da kawayenta. Washe gari daurin Aure ranar asabar karfe 11am,Aslam shi Kam yayi gayya sosai Suka Zo da danginsu na jini Yan uwan Uba dana uwa aka taru a masallaci Shehu ma shine wakilin Aslam shi ya karbi auren Aslam aka daura akan sadaki dubu dari,ana daura Aure Aslam Yana cikin abokai yaga Affan da liman sunzo Yana sani Aslam da abokansa yace Dan Allah a nuna Mana Wanda na kasa a samarin Amarya,Sabeer yace waye Muka zo muka kasa Muka cinye shi da yaki? Affan ya gane da shi suke,yace gani nan ya mikawa Aslam Hannu suka gaisa yace Congratulations a zauna lafiya,Aslam yace Kar ma a zauna lafiya,Affan yace to fa Yana dariya yasan kishi ne kawai,Sabeer yace Wanda Muka kasa ayi Hakuri banda gaba,Affan ya dinga dariya shi ko a jikinsa ya tashi Yana kwambonsa ya wuce,Liman ma ya taya Aslam murna sosai ,Aslam yau anji shadda ta musamman Fara tasha aiki da babbar riga da hula yayi kyau kamar a sace shi ga abinci da yayi orda fried rice da rabin kaza har da masu rabawa ana ta bawa mutane a ledar take away a zuwan gidan Amarya ne Suka kawo. Siyama kuwa ta Sha leshi dan ubansu golden and white,Kawu yace babu batun shagali ko angon bai je wajen Amarya ba Kawu ya Hana,Amarya tana zaune cikin Yan tsirarin abokanta suna cin abinci Kamar ba Amarya ba komai bata akeyi tana lashewa da ance gashi zata ci abinta, sun Kuna Bluetooth speaker suna Jin kidansu suna nishadi tunda ango ya bugo Mata waya yace sai na Zo daukan Amarya,Siyama tana Jin kunya tace ka daina zumudi fa period na Fara jiya da dare,Aslam yace ba komai bukatar maje hajji Sallah tunda an daura yanzu hankalina a kwance yake nasan kin Zama tawa,Murmushi yace 4pm zanzo daukan abata ki shirya da wuri,Siyama Wayarta ma ta kashe duk sai taji ba dadi abinka da wacce bata taba barin gida ba kullum kana tare da iyayenka dole idan za a rabaka da gida kaji ba dadi,Siyama kuka ta Fara Yi tun da wuri kawaye suna tsokanarta ta dauki pad dinta ta Shige toilet tana hawaye a cikin toilet din ta fashe taci kukanta ta koshi duk ta bata kwalliyar tata sai fuskar ta wanke gaba daya ta fito idonta yayi alamar Kuka,Aunty tana Sallamar baki ta kalli Siyama Suka hada Ido tace ke Kuma meye na kukan duk rashin kunyar tana ina? Yan Uwa Suka saki guda da shewa Siyama sai sabon
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71