Skip to content

Chapter 17

Chapter 17

AURENMU Book One Complete Hausa Novel 1,243 words 0 views Progress saved
Download Book

ba? Siyama bata boye musu ba ta Basu labarin komai Aunty tace amma Nusaiba ta bata wayonta ka samu miji haka irin mijin Novel zukeke ga kudi amma ta dinga irin wannan rayuwar gaskiya na tausaya Masa shike nan zauna mu koma siyar da alalar mu inda Muka fi wayo amma Nusaiba ta bani mamaki samun miji haka,Dauda yace to anji kin damu mutane da miji kyakyawa ne ni bani da kyan ne?kina ta wani yabon mijin wata ga naki amma baza ki yabe shi ba,Siyama tace to ai Kaine Kawu lebe Kamar sakatar kofa,zanci Ubanki Dan ubanki lebena ne kamar sakatar kofa? Siyama ta sake cewa ba lebeba hakora kamar goslow a hanyar Lagos wasu sun taho ta nan wasu ta can,Dauda yace Zaki ci ubanki ni ba ubanki bane Zaki dinga maida Ni kakanki ki kiyayeni wlh,Aunty tayi dariya tace gwara da yarka ce ta fada da nice cewa zaka Yi sai kaci mutunci na Mama ce a zaune tana waya da Nusaiba tace me nake ji Haka gida daki daya chab dama karyar tasa ta Kai haka,Bari dai sai nazo ta furta lokacin Shehu Yana gida kusa da Mama a zaune,yace Wai ke me kike nufi ne? Nusaiba kin hanata sakewa naji labari jiya Ameer ya fada min komai yanzu tsakani da Allah ki kalli gidan nan da a kuntace muke amma yazo ya Kara Mana dakuna ya Bude Miki shago bafa ni ba ke ya budewa shago ya bani jari Kuma na koma kasuwa sosai ya auri yarki yanzu tsakani da Allah dan karya zai iya yin wannan taimakon,a tunanina ke me yiwa Nusaiba fada ce ashe ke kike zugata, Babu abinda zaka fadamin Shehu dakata kana ciyar damu?, Tunda na taso a gidanka wahala nake Sha Ni da yarana,Sanda Ina da hali ba kece kika cinye kudin ba suka Kare Kika tsaneni komai nayi Miki ban birge ba ya Zan Miki face na zura Miki Ido ke da yaranki tunda kince ba abinda nake tsinana muku,Hakkin Yara a kanka yake kwarai kuwa na sani amma idan na baki kudin cefane kina bari ki basu abincin ba kadan kike dafa musu ba ki siyar da sauran komai na baki siyarwa kike yi,Mama tace to ka kyale min yata ba ruwanka yace Ina da hakki na fada Mata gaskiya,yanzu bazan magana ba tunda bai kawo kararta ba amma duk Sanda ya kawo Kara Nusaiba zata Gane kurenta auren me kudi hauka ne da arziki da talauci duk na Allah ne Kuma wlh kuji tsoron Allah ya mike tare da sa takalminsa ya fice. Mama Kuwa Ameer ta samu ta balbale shi da fada akan me zai fadawa Shehu. Charity Alalarta taci gaba da yi amma yanzu tallan ma bata fita ake zuwa a siye a gida,Nusaiba tunda Suka koma gidan haya bata girki ficewarta takeyi su hadu da Sufyan saurayinta a restaurant in taci ta koshi ta dawo gida,Aslam da Kansa yake dafa ma Kansa abinci bai iya ba amma haka zaiyi jagwalgwalonsa ya ci,yau da Yamma Siyama sai gata a gidan sanye da hijab har kasa da Leda a hannunta tayi sallama ta shigo Murmushi ya saki shi ta iske a palo yace manyan kasa ne yau a gidan, Charity dariya tayi ta rusuna tare da gaida shi ya amsa,Ina matar fa? Ta fita ta tafi gidansu yace,Siyama tace okay dama abinci na kawo maka ban sani ba ko tana girkin,yace wow na gode Kamar kin San yunwa nake ji,ledar ta Bude ta dakko abinci a robobin take away har kala biyu tace kaga wannan Fried rice ce dazu Muka Yi da Aunty wannan Kuma tuwon shinkafa ne miyar Egusi,Kawuna nane ya samu kudi shine yau Muka ce bari muji Dadi kaci kaji da Dadi harda nama,mikewa tayi ta dakko spoon a kitchen tace gashi ya karba Yana kallonta cike da mamakinta tafi matarsa sau dubu,Fara cin abincin yayi gaskiya yayi Dadi ya furta Yana ci Siyama tana Kare Masa kallo,kallon fuskarsa takeyi Yana ci har ya cinye daya ya Sha ruwa pure water yace dayan sai dare tace to,Charity ta tura dayan kasan kujera tace gashi a nan na boye maka Kar marar Imani tazo ta dauke,dariya yayi yace na gode ta hada ledarta da roba tace tafiya zanyi tunda bata nan, yace da wuri haka kiyi zamanki ki tayani hira dama na gaji da kallon film,tace to ta zauna tare da tambayarsa har yanzu baka samu aiki ba ka fara? Ae yace Mata amma Ni da abokina Sabeer Muna ta fafutukar nema ko za a dace, Charity tace to Allah ya kawo tana Jin kunya tana satar kallon Aslam ba karya ya hadu gashi Kamar balarabe fari tas ita Kuwa ja ja ce, gidan ta kalla kaca kaca tace gidan naku yayi dirty yace a haka ma Ni nake sharewa,mikewa tayi ta hau shara ta gama tayi mopping ko Ina ta gyara kitchen,toilet din ma ita ta wanke musu ita kal kal ta dawo Palo ta zauna suna kallon film game yakeyi a wayarsa ps tace game kake Yi? Yace kin iya ne? Tace ae na iya wani abokina ne Hunaif yake bani wayarsa Ina Yi,yace ko dai saurayinki ne? Dariya tayi ya kalli kyawawan hakoranta reras gata kyakyawa sosai tace ya taba cewa Yana so na danginsa suka hanashi sabo da Ina saka riga da wando Wai Yar Lesbian ce ni,Dariya Aslam yayi Yana latsa waya yace ai maganinki kenan da kike saka riga da wando ke ba a kudu ba kin San wani Yana kallonki shedar da zai Miki ta banza shi yasa ake so a dinga kiyaye shiga,da shiga ake Fara gane mutumin kwarai ga sunanki Charity kowa Charity,Siyama tace ai Riga da wandon ne yasa a unguwa aka saka min suna Charity idan na nuna bana son sunan anfi kirana da shi that's why na karbi sunan Hannu bibiyu,Riga da wandon ma kana ganinsu manya manya nake sawa bana saka damammu Kuma yanzu na rage sakawa tunda nake Yana damaging Image dina,yace yawwa ko ke fa ai yafi amma dole ace Yar lesbian ce tunda barma barma kike sawa Kalar na maza,dariya ta sake Yi akwaita da fara'a,tace Allah ya tsine musu wlh masu lesbian ga maza can suna nema Mata suna musu mugunta,dariya Aslam yayi ba shiri yace Charity kenan ke kam ba ruwanki da boye boye kamar Yar kudu haka kike Charity tace idona ne ya Fara tsikewa da duniya mu fa Yan talla ne iya shege ba Wanda bama ji,sai da na Fara talla na gano illar barin ya mace tayi talla Kaga idan mace tana talla ko wanne gara Wanda ko a Hanya Bai Isa ya Miki magana ba idan kina talla kowa zai kulaki ko wanne gaja ne Kuwa,sannan akwai Wanda a hanya bai Isa ya iya ko magana ba Amma sabo da talla zai fada maka Maganar da yaga dama,sannan me talla kowa Yana da lasisin da zai Mata magana ko a dinga tsokanarta ko wani ma yaci Mata mutunci,mace me talla Namiji zai iya janta da zancen banza ya ja mayafinta ya daketa wani ya mareta wasu Kuma duk Magana ta banza yarinya tun tana karama Matukar tana talla za a dinga Yi a gabanta,tunda waje ne na maza idan Suka taru akwai

Table of Contents

Chapters

71 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71