Chapter 67
Chapter 67
tana ta kallon yanda yake murna itama haka,tun daga ranar Affan kullum kafin ya fita sai ya Dora bakinsa a cikin ya kwararawa dansa Addua sannan yace Baby Daddy zai fita a Mana addua idan ya dawo ma haka sai yayi Masa addua yace Daddy ya dawo,Raudah Kuwa yanda take ji da cikin nan nata Kamar kwai. Aisha ma da cikinta Farook murna ba a magana,haka Sabeer matarsa har ta samu ciki sai amai take fama,Nabeela ma tana fama da nata. Yau Shehu ya sanarwa Landlady zai raba musu kwana ya gamsu da shiryuwar matarsa ya Kira Mama ya kira Landlady ya musu nasiha sosai da yaransa ma ya tarasu sun Sha nasiha sannan yau ya Fara kwana a dakin Mama yaji ta zam zam Kamar ba ita ba to ta Sha gyara,Kuma Mama haka suke gaisawa da Landlady ba gaba sai dai dan kishi na Mata Wanda baza a rasa ba dole. AsmaBaffa [4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️ 99-100 Official By AsmaBaffa Page naku ne Hafsa Abdullahi Fateema Farouk Nusaiba tana zaune yau Mama ta aiketa kasuwa zata Yi Mata cefane ta shiga Napep sai me Napep yace Zan Sha Mai Hajiya tace to,gidan man da Affan yake nan ya shiga,Yaron Affan Salahu Wanda Suka Yi hatsari da Raudah akan machine dinsa Yana gidan man Affan ya sashi aiki da machine dinsa a gefe yaga Nusaiba a Napep sai kallonta yake Yi sai ta Masa Kama da matarsa data mutu da ciki wajen Nakuda,Kawai ganin tana Kama da matarsa yaji Yana sonta,Yana ta faman kallonta Kamar maye,wajen Napep din ya karasa yace Yan Mata sannu,Nusaiba rabon da wani Namiji ya kulata a duniya har ta manta sai yau,farin ciki ya kamata amma ta danne tace yawwa,yace dan Allah ya sunanki? tace Nusaiba yaji sunan matarsa data mutu mamaki ya kamashi yace ikon Allah dan Allah Dan yi dariya na gani,dariya ya bawa Nusaiba ta murmusa yace har dariyar iri daya wlh sannu baiwar Allah wallahi birgeni Kika yi haka Kawai naji Ina sonki Sunana Salahu,Nusaiba a ranta tace ji wani suna dan Allah sai ace Nusaiban Salahu ko dadi,kallonsa tayi sama da kasa Salahu matashi ne Kamar su Affan wankan tarwada ba laifi baida makusa kuma Yana gayunsa da tsafta Dan birni ne, a ranta tace karfa kiwa kanki tace na gode a fili,Yace dan Allah Dan bani number dinki idan ba damuwa,Nusaiba harda Jan aji sai da ya dinga rokonta sannan ta bashi da kyar tana yanga,Salahu Kuwa haka yake son mace me yanga sai ta birge shi tuni ya Kara Jin sonta. A hankali waya Suka Fara da Salahu kafin wani lokaci Salahu ya siye zuciyar Nusaiba yace shi da gaske yake daga nan ya dage da zuwa zance da machine dinsa yace yafi son bazawara yanzu sunfi hankali sunga rayuwa,Yana zuwa zance an kusa turo manya aka samu munafukan layi Suka fadawa Salahu tsiyar da Nusaiba ta shuka aka sake ta,shi yasa ake so ka shuka Alkhairi duk tsiyar me hassada bazai samu abin fada akanka ba,gashi Nusaiba ta kamu da mugun son Salahu Kawai taga ya daina zuwa Kuma ya daina kiranta a waya idan ta kirashi sai yace zai Kira bazai kirata ba,Addua taci gaba da Yi ba dare ba rana tayi ta kuka a boye ba tare da wani ya sani ba,Soyayya ta sa Nusaiba kuka sai yanzu tasan mene so akan Salahu,sabo da sauran Wanda ta aura kudi Kawai ta hango Basu samu damar zuba soyayya da ita ba sai Salahu talaka me rufin asiri. Tun Mama bata fahimci haka ba har ta gane bata tambaya ba ta rabu da ita,Shehu ne ya Kama Nusaiba tana wanke wanke tana kuka bata San ya shigo ba,Kujera Fara ya ja ya zauna ya dakko lemonsa na roba ya balle Yana kurba Yana kallon Nusaiba ya harde kafafu,Mama ce ta fito tace yau me Zan gani Nusaiba me ya faru,Ka gani Abban Ameer, Shehu dariya ya dinga Yi Yana kora lemo abin Yana Masa dadi yace sai kin tambaya akan mene yarki soyayya ta fada talakan da kuke gudu a kansa take wannan an zuga shi ya daina zuciya dama bata San so bane shi yasa da kudi ne a zuciyarta ba soyayya ba yanzu Kuma da damarta ta gudu ba me kudi talakan ma Neman sa akeyi Ido rufe to an same shi da kyar Kuma ya subuce ga sonsa take sosai,Mama taji tausayin yarta Jin Nusaiba ta sake rushewa da sabon kuka tace yarka ce dai wallahi ba daidai bane,Shehu Yana kora lemo Yana tuntsira dariya Nusaiba da Mama an shiga wani hali Yana kallonsu Mama tana lallashin yarta. bangaren Salahu yana mugun son Nusaiba amma abinda aka fada Masa shi ya hanashi ci gaba da nemanta amma zuciyarsa ta kasa hakura da ita. Siyama cikinta ya tsufa haihuwa ko yau ko gobe,washe gari Monday Aslam Yana da meeting ya fita da sassafe ko bacci bata tashi ba nakuda ce ta tasheta, Jin ciwon na musamman ne Kawai bata nemi Aslam ba sabo da tasan meeting ne da shi akan wani contract zai iya rasa wa sai ta Kira Aunty,Aunty da sauri tazo tare da Yayarta Suka Kai Siyama asibiti,Kamar jira ake ana basu daki Siyama ta haifo danta Kato Namiji kyakyawan gaske,Kuma ta haihu lafiya Kamar ba ita ba, nan da nan aka Mata duk abinda ya kamata zuwa 2pm aka sallame su duk Aslam bai San me akeyi ba,Aunty gidanta ta wuce da Siyama a can tayi Mata wanka da towel ta koya Mata sannan tayi na sabulu da kanta,Aunty ce ta wanke jariri tsaf aka sa Masa sabon kaya farare masu tsada da kyau aka sashi a showel fari Yana kamshi,Siyama ma shiryawa tayi cikin doguwar rigar atamfa sabuwa a gidanta Aunty ta dakko mata ta shafa turaruka ta zauna taci abinci ta koshi,Jariri sai cin hannunsa yake Yana Jin yunwa,tana gamawa Aunty tace a bashi nono,Siyama ta dauki jaririnta tana washe baki ta tsura Masa Ido tace yanzu Aunty dana ne wannan? Hararta Aunty tayi tace nono akace ki bashi,Siyama ta saka hijab Wai baza a gani ba,Nusaiba ce ta shigo ganin yaro taga me jego an lulluba da hijab,tace malama ki fito da nono ki ba yaro,Siyama tace Aunty na rasa bakin yaron fa,Ina Zaki ganshi kin lulluba,Da kyar ta samo bakin yaron tace Bismillah dan yaro kayiwa ubanka kaka gida,Aunty ce ta maketa a kafada tace ke dai anyi marar kunya wlh,Siyama tace Aunty ai gaskiya ne shike nan ubansa yau sunyi handing Over,Nusaiba ta fisge hijab din data rufe kanta,Siyama ta Fara masifa wai mene haka Zaki ga sirrina ta jawo ta sake rufawa kanta da jariri,Nusaiba tace ga yaron irin ubansa, Sai da ta gama bashi nono ko koshi baiyi ba tace ya isheka haka karka yi katon ciki, ta mikawa Nusaiba yaron tace gashi kalli danki Kamar zai ce min Mummy, Nusaiba ta karbi dansu tana gani tace wannan yaron wayo zaiyi,Siyama tace bakya ganin idonsa Kar Kamar zai Kira sunana,kalli girarsa cewar Siyama,Nusaiba tace irin ta ubansa ce ya fiki karfin jini,Aunty ce ta tashi Jin rashin kunyar da suke yi Siyama a hankali tace ba dole ba ya fini karfin jini ai ansha aiki ayi fama anyi gumurzu,Nusaiba tace ai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71