Chapter 32
Chapter 32
dubu biyar ya mikawa Aunty yace gashi Aunty Kya sa ko Kati ba yawa,Aunty tace harda kokari haka to fa an gode an gode Allah ya Kara sutura yace Ameen Suka koma dakin zaure Wanda ya Sha gyara sai kamshin turaren wuta yake Yi. Suna shiga Siyama ta dawo ta dauki nata abincin ta wanke hannayenta tare da daukan wani spoon din ta shiga daki ta saka hijab me hannu ta koma wajensa,tana shiga ta iske shi a tsaye tace baka zauna ba,yace tsutsar cikina ce ta tasheni,dariya Suka Yi gaba daya suka zauna tace dan Allah kaci da yawa nasan baka ci komai ba,yace indomie naci Mana,indomie abinci ce? please....ta karasa da shagwabar da hankalin Aslam ya tashi Yana Mata wani irin kallo cike da so Wanda yasa yace kin San me tace sai ka fada yana kallonta Ido cikin Ido ya furta Ina sonki Charity na matsu na jiki kusa dani, Charity tayi Murmushi tace hmm ban baka labarin wata kawata ba Haleesa wata daya da aure jiya naje gidanta na samu tana sheka amai nace haleesa lafiya? Charity tana wani magana ana Yi da hannaye ana style da hannaye Wanda sun Sha lalle me mugun kyau Wai dan Aslam ya gani,tace Ina fada maka ta sake daga hannayen tana jujjuyasu tace dan ubanki Charity ciki ne dani, ai tunda na bude baki kasa rufewa nayi,tana bawa Aslam labarin shi Kuma ita yake kallo kamar tv Yana dariya tun dazu yaga lallen amma ya nuna Kamar bai gani ba shine yanzu labarin ma Sai an sake nuna Masa lallen. Magana yayi yace ya birgeni haka ake son Namiji kema Watarana haka Zan Miki naki,Charity ta bude baki kunya ta kamata ta rufe Ido da tafukan hannaye tace ba ruwana ni dai Kawai sai a ga Yar Baby ta ace Yar gidan Charity ce wallahi haka zance duk Wanda taji yace da mamanta Charity Kar ta sake ta yarda,Aslam yayi Murmushin Jin dadi yace har na hango kanmu,Ki fadawa Kawu Zan turo a kawo kudi,Siyama tace da wuri haka? Yace kin San Kuwa yanda hankalina ya tashi da naga kina zance bazan iya ba wani yazo a samu matsala,Siyama tace Ina tsoro Kar Kawu yaki yarda sabo da Nusaiba,Aslam yace karki yarda a hanaki aurena kinji dan Allah bance ayi musu rashin kunya ba dole muyi musu biyayya abi a hankali amma ki dage kice sai ni,Aslam Yana yiwa Kansa campaign yace wasu tanadi da na mana sai dai munyi aure,Siyama tace duk abinda ake ciki ka dawo jibi,yace gobe Zan dawo ni ban gaji da ganinki ba tace Allah ya kaimu,mikewa yayi yace zanje wurin Mum,tace kace Ina gaishe ta yace zata ji itama ya zaro dubu biyar ya bata taki karba yace bana son musu,ta karba tare da furta na gode ka manta ledarka da ka shigo da ita tana kusa da Aunty,Aslam yace wayarki ce,waya na siya Miki Zaki ga Simcard din a cikin ledar ki saka sai na kiraki anjima ya rike hannunta ta zame a hankali yace Ni kike ma Haka Yana Murmushi tace muna yin aure kazo kayi ta rikewa,an gama ya furta Suka fito ta rakashi da motar Sabeer yazo ya shiga abarsa ya tafi ta koma ciki taci gaba da dura abincinta. Washe gari da safe taje gaida Kawu Aunty tana dakin tace Kawu ya amsa tana kunya tace Aslam yace zai fito,Kawu yace daga Ina zai fito? Takara zai fito ko kuwa daga daki? tace zai turo nake nufi,kawu ya gane fa yace baro zai...a'a fa kawu zai turo da manyansa neman aurena ,Kawu yace Yar jakar uba ai na gane so kike ki jawo Mana zagi da abin kunya a unguwa,yanzu idan aka ji mijin kawarki Zaki aura ai mun shiga uku a layin nan da zagi,Aunty tace sai ace ma itace ta rabata da gidan mijinta gashi Yanzu ta aure mijin nata ai ki auri Affan yafi Miki Siyama,Kawu yace rabu da Yar banza Ni baza ayi haka dani ba ki jawo min zagi,Baban Nusaiba Yana ganina da mutunci ace haka ta faru ai ba mutunci,Kece fa babbar kawarta kaf unguwar nan tare aka sanku yanzu sai aji kin aure tsohon mijinta bazai yuwu ba sannan naga Alama kina son Aslam baki son Affan zanje na bawa liman hakuri abin bazai yuwu ba amma ki sani bazan aurawa Aslam ke ba,nasan ya cancanta mutumin kirki ne amma ya auri babbar kawarki ya dawo ya aureki haba Siyama ai da kunya Siyama tace to ni shi nake so bazan taba son kowa ba sai dai na mutu ba aure Kuma ai lokacin da yake baku kudi karbewa kuke Yi baku ce mijin kawata bace bai Dace ba sai ku karba ko musu bakwa Masa Sabo da lokacin Yana da kudi Sanda zanje gidansa wanke wanke da shara kune kuka Amince baku gano rashin dacewa ba budurwa dani katuwa naje gidan best friend dina wanke wanke da shara bakuyi tunani haka ba kuka Kora ni naje can yanzu Muna son juna shine zaku ce mijin kawa ne Kuma ai ya saketa tayi Aurenta Kuma ita tace a saketa tazo ma tace idan na gani Ina so naje ayi Dani sabo da haka na gani Kuma Ina so a aura Masa ni Yana so na shima Kawai in Kuna son zaman lafiya ku bashi ni a huta,rufe Mana baki shashasha abinda babba ya hango yaro ko ya hau bushiyar rimi bazai hango ba, wallahi wani yaron ba amma ni abinda babba bai hango ba na hango cewar Siyama,zageni ki huta Siyama cewar Kawu, Siyama ta mike tsaye tana hawaye tace da Ina da iyaye ai baza suyi min Haka ba Dan anga ubana ya mutu uwata ma ta mutu shine ake ta nuna min iyakata ta nufi kofa zata fita ta sake cewa Kuma Allah Matukar a watan gobe ba ayi aurenmu ba sai naje ya min cikin Shege,sai na jawo muku abin kunyar da yafi na auren tsohon mijin kawata da wancen abin kunyar gwara na wannan ta juya ta fice ta sake cewa Kuma za a gani kwana nan Zan Fara amai,Kawu da Aunty Suka saki salati Aunty tana yau ga zamani karshen duniya kaga Dauda ka barta ta aure shi wallahi yaran yanzu basa Jin magana basu da hankali ba irin yaran da bane masu biyayya yaron yanzu sai hakuri da addua duk inda ka kai da tarbiya sai addua,Siyama dai bata Mana musu tana Mana biyayya tsakani da Allah tunda kaga ta dage a wannan gaskiya da matsala. Kawu yace ke har kin tsorata karya take baza ta iya ba ni nine ubanta bazan yarda ta jawo min zagi a gari ba,Aunty tace gaskiya ka ba yarinya zabinta mene aibun Aslam kaima wallahi butulu ne tunda har ya baka jari ka tsaya da kafafunka yanzu bama cikin wahala amma yanzu akan wata banzar Nusaiba da mutanen gari za kayi butulci,Dan Adam ai ba a iya Masa ko kayi ko kar kayi sai ka samu masu zaginka da masu yabonka haka duniya take bare Nusaiba da uwarta Wanda kowa yasan me Suka aikata ai Bari kaji ba a birge dan Adam Kawu tashi yayi a fusace ya fice daga dakin gaba Daya. Siyama an kifa Kai a jikin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71