Skip to content

Chapter 53

Chapter 53

AURENMU Book One Complete Hausa Novel 1,258 words 0 views Progress saved
Download Book

shi mamaki take bashi yanda taci kuka,kamar bazai hakura ba yace tashi na hakura ni ki daina durkusa min haka,na hakura ya zanyi Dake tunda Ina sonki na fada Miki bana son kishin zargi idan kishi yayi yawa zargi yake sawa idan nayi niyyar kula wata har zan bari ma ki gane kin San maza kuwa,bana son zargi a rayuwata bana so karki sake min irin haka,Raudah da tana ganin Affan Kamar sai yanda tayi da shi sai taga ashe ba haka yake ba baya takuwa ko kadan Namiji ne bai son raini,tuni ta Shiga hankalinta,yace kije kiyi bacci,ta mike sum sum har ta fita ta dawo tace baka ce kana so na ba,bazan fada ba yau Banga dama ba ya furta Yana hararta,tace to ni Ina sonka yace can da yawarki,tafiya tayi dai zuciyarta ba dadi da safe bata je aiki ba Monday guda Affan bai ce Yana sonta ba tana nan tana bacin rai, Tuesday ma kin zuwa tayi tace bata da lafiya sai ta warke,Affan yaga motarta kwana biyu ba inda ta fita ko a compound basu hadu ba Kuma ko ta window bai leka ba bata leko ba zai shiga mota ya fasa yazo yayi knocking door nata ta bude ya ganta ras da ita taci kwalliya,tace Ina kwana lfy Alhmdllh kwana biyu bakya fita lafiya? Kai nake jira kace kana so na sai na fita,Affan Ido ya zaro yace kina da abin mamaki Raudah....kuka ta saki kaji ko kaji ko Beb dinma ka daina fada sai Raudah,Murmushi yayi Yana kallon ikon Allah,yace sai ance ana sonki dole shine Kika San ana sonki? tace ae ni Indai ana so na Kuma ana son zaman lafiya kullum sai ance min I love you morning, afternoon and night,I love you ya furta tace naji na yanzu Saura bashin na jiya sai da ya fada yafi sau biyar sannan tace yayi haka a dawo lafiya,ya tafi Yana dariyar Raudah. Siyama ce ta zuba wani abinci zata ci Aslam yace yayi kadan ki Karo a gidanku ba haka kike ci ba,tana shagwaba tace ai tunkafin ayi min aure Sam bana iya cin abinci bana son ci ma dole nake yiwa kaina Aslam a ransa yace to ga Kawu yace idan yaga ta rame akwai matsa dole na samo Mata multivitamin,tashi yayi yace da kin fada min tuntuni ai da na samo Miki maganin cin abinci ki dawo normal haka akeyi,Bari naje chemist tace to,yaje chemist din layin yace Multivitamin zaka bani maganin cin abinci babba,me chemist yace Kaine baka iya cin abinci? Yace ae me chemist shi ba likita bane Yar makarantar ma school of health technology ya Fara aka kore shi ai Kuwa ya dauki me karfi maganin boosting din apetite da Kuma multivitamin ya bashi me kyau me karfi yazo ya ebo ruwa ya balla ya bata ta Sha ashe muguwar yunwa yake sawa tare da shegen bacci,Minti talatin ta shafa cikinta tace ji nake Kamar an sace min kayan cikina Honey wayam ba komai,abincinsa da bai ci ba yace sai anjima ta dauke ta cinye tas,tana ci wani mugun bacci ya kamata ta mike tsam ta tafi bedroom dinsa ta kwanta bacci take ba ji ba gani har dare bata tashi ba,zuwa yayi Yana tashinta yace wannan wanne irin bacci ne magriba ta wuce fa har na dawo daga masallaci Daukanta yayi tare da direta a kasa tana tangadi ta shiga toilet da kyar tayi Alwala da Sallah a wajen ta kwanta sai bacci Aslam yaji gidan ba dadi abokiyar tasa tana ta bacci Sallar Isha ma da kyar ta iya tashi ga jikinta ya mutu,Har 11pm tana bacci Aslam sai me aiki ya sa ta Masa girki, yayi wanka tare da Shirin bacci yazo Kawai ya dakko rigar bacci wata sabuwa ya cire Mata kayan jikinta garin cire kayan bacci sha'awarsa ta motsa ya fasa sa Mata kayan yaja ta suka Shige bargo tare zaiyi shagali tana ta faman bacci jiki a mace Yana Fara taba ta sai dai ta bige hannunsa tace ni bana so wlh ka kyaleni bacci,Aslam takaicin magani yasa ya kwashe su tare da watsa su a dustbin yace baza a sake shansa ba haka Kawai ya jawo min tsiya Magani dai sai da safe ya saki Siyama da safen ma ba sosai ba,zata tafi kitchen ya riketa yace kalli hannuna yanda ya dawo red sabo da dukanki,dariya tayi tace maganin nan ne gaskiya,Nima Naga alama tace baccin Dadi a Kara min,yace na zubar da dan Iska jiya ya hanani Jin dadi sai hakura nayi amma yanzu ba fashi Siyama tace ai banci abinci ba yunwa nakeji yace to gama aikin ,ta fita ya koma baccinsa,tana kitchen din amma ciye ciyenta takeyi tun kafin ta gama Kamar zata cinye abincin gidan,tana gama soye soyenta ta zauna ta karya ko jiransa baza ta iya ba sai data gama ta koma bedroom dinta wanka tayi ta shirya cikin Dan Bum short black sai wata rigarsa silk white da digo digon baki me dogon hannu ce da kwala,pcap ta saka me black da adon fari,gashinta kwance a baya tayi bala'in kyau,ta fito daga room dinta sai gashi ya fito sanye cikin Jallabiya arsh Yana kamshi, ka tashi har kayi wanka ashe,Yana can Yana aikin kallonta bai ji me tace ba sai da tace hello sannan ya dawo hayyacinsa,tace ka tsaya kana ta kallona,kinyi kyau da yawa ne shi yasa,jawota yayi jikinsa Yana shakar kamshinta Bayan ya karya ya dauketa sai dakinsa domin bazai iya hakuri ba a matse yake,Haka ya soye ya barta da jinya. Amarci suke Sha Kamar ba gobe zuwa wata uku Siyama ta murza kiba tayi wani kyau da haske kana ganinta kasan tana hutawa hankalinta a kwance yake,lokacin tace zata je gida ta gaida su Kawu,Ranar wata Sunday Suka shirya cikin sutura me tsada sunyi kyau matuka Suka fito Yana kallonta yace dole Kawu yace na iya kiwo ya bude Mata mota ta shiga sannan ya zaga ya Shiga yayi driving din su zuwa gidan su Siyama,Yana yin parking ya fito kenan ya Bude mata kofa ta fito sai ga Nusaiba ta dawo daga shago hannunta rike da leda ta siyo manja bai fi na dari ba,ta rame tayi baki sai kallon Siyama takeyi da Aslam tana zare Ido,Aslam ko kallonta baiyi ba,Nusaiba kishin Siyama take yi Bata kulata ba,Siyama ce tace Yar budurwar bazawara daga Ina,Nusaiba Tsaki ta ja tayi gaba fuuu,dariya ta bawa Siyama tace Nusaiba kawarki ce Charity fa Nusaiba ko kulasu bata Yi ba ta fada gidansu tana kuka a gaban Mama,Mama tace wanne Iskanci ne wannan wallahi Kika fasa manjan nan sai dai kuci shinkafa da waken nan babu mai wallahi kudin cefanen da ubanku ya bayar na dauke dari biyar na zuba a dashi dama da irin wannan Yar cuwa cuwar muke yin dan adashin nan namu,Nusaiba tana hawaye tace ni gwara Ina gidan mijina ko gidan Sufyan ne ya fiye min,Mama tace ki Bari kiyi idda Inshaallah hannun Aslam ma zaki koma,ai na kusa iddar Ina sane dake akwai abinda zanyi karki damu yarinya,Nusaiba sai lokacin ta danyi murmushi. Aslam kuwa gidan Kawu Suka shiga Aunty sai Murna Siyama tayi kiba an Kara kyau alamar kana gani kasan tana cikin kwanciyar hankali,Kawu ne ya

Table of Contents

Chapters

71 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71