Skip to content

Chapter 58

Chapter 58

AURENMU Book One Complete Hausa Novel 1,250 words 0 views Progress saved
Download Book

Raudah tare da dora ta a Kai tare da rufe motar ya turata a hankali zuwa ciki,Raudah tana ta zagin kanta a zuciyarta abinda ta aikata,Affan gwani ne wajen gyara da tsafta sai da ya gyara gidan nan tsaf sannan ya yiwa Raudah wanka shima yayi ya dorata saman kujerarta suka fito,ya shiryata cikin gown gajera marar nauyi,abinci yayi order aka kawo musu har gida suka ci sannan ya fita masallaci ita Kuma tayi sallah a zaune saman kujerarta. Washe gari tana Palo tare da Affan suna kallo Landlady ta shigo bayan sun gaisa Affan ya koma bedroom ya basu waje,Rauda ta kalli Landlady tana hawaye tace kin cuceni ke ba matar kwarai bace Kuma ba abokiyar zama bace,sam bakya Dora mutum a hanyar gaskiya gashi nan abinda Kika jawo min yanzu gashi nice a wahala,Ina zamana da mijina lafiya ke kin kasa aure kinzo kina zugani bakya taba yabon maza sai dai ki Fadi sharrinsu shi yasa da yawa wasu matan idan Suka taru basu da aiki sai fadan sharrin maza basu fadan alkhairinsu a haka wasu Wanda suke zaune lafiya da mazajensu shike nan an gurbata musu zuciya sai su Fara zargin nasu in ba a yi sa'a ba rashin zaman lafiya ya Fara kenan,Mata in Suka taru basu da aiki sai zagin maza da halayensu ki sani wata idan bata dauka ba wata dauka zata Yi karshe auren ya mutu ma,ba kowa ce take auren miji me kule kulen mata ba Kamar mijinki da Kika taba aure Bmbai yuwuwa kiwa maza kudin goro,na Zama sakarai da ilimina da hankalina na zauna Ina daukan shawararki landlady kiji tsoron Allah kije kiyi aure ki daina lalata Mana namu,kuma Indai zugace zata kawoki gidana karki sake zuwa inda nake bani ba bake har abada,kin girmeni babbar mace ce ke amma baki da tunani, Landlady tasan itama bata kyauta ba tace kiyi hakuri Raudah wlh aurena dana Yi na fuskanci halin mijina kenan sai nake tunanin kowa ma haka yake wannan yasa na kasa kara yin aure amma Inshaallah nima na gane gaskiya,Raudah tace oho Miki ni dai in bada alheri Zaki Zo ba karki sake zuwa gidana yanzu ma ki tashi ki tafi, Landlady ta mike jiki ba kwari ta tafi,Raudah tana hawaye Affan ya fito yace Wai me yasa kullum sai kinyi kuka ne kina Jin sauki fa kin kusa fara tafiya da kafafunki Inshaallah. Raudah tana kujerarta ta miko hannu tare da rike hannun Affan tana hawayenta tace dan Allah ka yafe min na tuba bazan sake ba,ta bashi labarin komai zugata da Landlady keyi tace karshe gashi ta kaini ta baro na karye ta fashe da kuka,Affan yace ai Raudah tunda naji kinyi hatsari nasan kishi ne ya fito dake shi yasa ma ban tambayeki ba nasan baki da wata matsala face kishi,abinda yasa Kuma bana damuwa so ne a kaina akeyi Kar wata ta kwace ni to ni ai na Zama dan gata gashi kin jawa kanki kin karye Allah ya takaita ma,haba wifey babu izinina Kika fito haba Raudah kishi fa idan yayi yawa zargi yake kawowa,da sauri tace wlh bana zarginka Kawai in ta zugani ne sai naga kamar haka ka yafe min kayi hakuri bazan sake ba babu ruwana yanzu gashi na karye a banza,Affan ya kyalkyale da dariya tana hawaye ta duke shi a kafada,yace ai Ni Kika jawa aikin,ki sani bazan taba cin Amanarki ba na Sha fada miki,to yanzu idan ta kasance Zan Kara kishiya yaya kenan Raudah? tace ai ma Inshaallah baza ta faru b,to idan ta faru fa? Mutuwa zanyi Kawai,yace kin gani wannan halin naki sai ke Kika ce kin tuba kuma? Baki ta turo tace ae na tuba bazanyi fada ba bazan ce komai ba Kuma bazan bibiyeka ba sai dai Kawai aga na mutu,Affan yayi dariya sosai tace ai kana da kyau ko wacce sonka zata dinga yi ni Kuma bana sooooo....ta karasa da kuka,To yanzu Raudah nifa ba ni nayi kaina ba Nima tashi nayi na ganni haka,Raudah tace ka kakalo shi Mana tunda kana ta gyara jikinka kana daukan wanka kullum kayi ta matso kyawunka kana fita gashi nan sai kafi 1h a toilet kana wanka duk ka goge fatarka kullum fari kake sake Yi kullum gashi nan bature kake Zama,Affan dariya Kamar me yace to na daina wankan sai na zauna miki a kazami gobe kice Nima Ina warin hammata,yanzu sai kince kin tuba kin daina ko? Raudah tace Zan dinga yiwa kaina Addua kaima ka tayani,Affan ya sake sakin dariya tace wannan ba abin dariya bane kaje kullum kayi ta gyara Suma ba ji ba gani ko wacce Yar iskar budurwa tana zare Ido gashi nan gaf ake da yaye dalibai daga Yan secondary zasuyi candy gashi Yan University sun kusa gamawa naji a labarai ance final exam zasu zana Kuma Yan Service sun gama miji suke jira wallahi ta Allah ba tasu ba, Affan har wani dadi yake ji ana kishinsa yace to ya Isa me Miji,Raudah tace kayi hakuri na tuba Allah kishi irin na baya da nayi bazan sake ba amma zan dinga dan yin kadan kadan shi yasa nake baka hakuri kayi hakuri dani Dan Allah har Allah ya yaye min,Affan yace to an gama Raudah,no your love zaka ce ta gyara masa Yace Okay My love,My one and only, My Heart,My soul my life Kuma Queen dita,Raudah Murmushi tayi tana Jin dadi tace ga mijina me jinyata me so na wata tazo itama Watarana ayi jinyarta haka dole naji haushi,kwana nawa baka Yi komai dani ba lafiya iceko? Affan yace Baby rigima baki da lafiya a karyen zanyi wani xxx dake,Raudah tace a'a in kana so kayi Zan maka komai Zan daure ai na Fara Jin sauki kafar basai a lallabata a gefe daya ba,Wai wayo take wa Affan Kar ma yaji Yana so ya Karo aure tunda bata da lafiya ko yayi sha'awar wata ita bata da lafiya baza ta iya Masa komai ba akan haka gwara ta daure tunda tana gani idan Yana Mata wanka Yana shiga yanayin bukatar mace daurewa Kawai yake yi shi yasa gwara ta tari abin. Affan da wuri ya amshi tayin Raudah yana murna yau zai gagije,ai Kuwa da dare haka kafa aka sata a gefe Suka jiyar da juna dadi. Washe gari Raudah tana kallon labarai a tashar hausa suna zaune da Affan taji ance gomnati ta dage jarabawar waec da dalibai zasu zana Yan secondary school an Kara wata uku nan gaba,Raudah tace Alhmdllh Yan banzan Yara aci gaba da shiga aji,Me labarai tace kungiyar Asu jibi Monday zasu Kara tafiya yajin aiki na Sai baba ta gani,Raudah ta kyalkyale da dariya tace maga karyar gama degree dan ubanku,Affan Yana jinta waya yake dannawa amma sai da ya tsaya kallon Raudah tana bashi dariya matuka. Bayan kwanaki ya Fara koyawa Raudah tafiya har ta iya ta Fara takawa da kanta har ta dawo tana tafiya normal Kamar bata taba karyewa ba,likita yace ta dinga Dan zaga unguwa tana tafiya a kafa me dan nisa,tare da Affan Suka fito sunyi gayu sosai Affan sanye da 3qrt da t-shirt komai fari,ita Kuwa Abaya ta sa silver color me shegen kyau tayi rolling suna tafiya a layin suna zancen soyayya

Table of Contents

Chapters

71 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71