Skip to content

Chapter 3

Chapter 3

AURENMU Book One Complete Hausa Novel 1,255 words 0 views Progress saved
Download Book

hada ku? Affan ya bude baki zaiyi magana Hajiya Mairo tace rufe min baki Kai har kana da yanci a gidan nan kudin haya ma ka kasa biya,kana da bakin magana rufe Mana baki,ai Kuwa sai yayi mukus baida bakin magana,Raudat ta kyalkyale da dariya sanye take cikin Arabian gown me kyau tana kamshi tace ka biya kudin gida? Ko kudin gida ka kasa biya ai Kai ba Dan gida bane ihu ta Masa wooooo ko kudin gida ya kasa biya get out, Affan sadaf Sadaf ya koma cikin part dinsa bai da sisi baida inda zai samu kuma. Kuka tafashe da shi tace wlh Shehu Allah sai ya tambayeka yaranka shida amma ka kasa ciyar damu kullum sai Yar sana'a ta nake cinyewa,Tsaki Shehu ya buga yace ai yaranki ne ke Kika haife su yanzu Dan kin basu kudinki shine matsala,amma Shehu kasan ni ke daukan nauyin kaina da yarana kana da kudin ba Babu ba baza ka iya ba,gasara nake siyarwa itace sa'a ta amma Watarana har da rana Koko muke sha ga yarka Nusaiba har ta girma ta Zama budurwa ko yaushe Yarinyar nan kamar almajira haka take yarinya kyakyawa amma kamar almajira Shehu kaji tsoron Allah,Nusaiba ce ta shigo cikin jemammun Kaya da katon botikin kosai a kanta tayi sallama tace Mama na manta da yajin kosan,Yajin Nusaiba ta dauka ta tafi tallanta wurin tasha inda mutane ke taruwa,Nusaiba tana ta ciniki tana irga kosai a Leda ga duk Wanda ya siya,ta mike tsaye tana mikawa wani drivern babbar mota,wani bugagge yazo ta Bayan Nusaiba ya taba mata duwawu,Nusaiba tace Ina Wasa da Kai,Ni Yar iska ce? Ka taba ganin Ina wasan banza? Ni ba irin yan Iskan Yan talla bace neman halak na fito,zaka taba min duwuwu tayi fatali da ledar kosanta bundle sabo da masifar Nusaiba ta shatile Masa kafafu ya zube a kasa ta dinga dukansa ta rufe shi da Naushi a Fuska sai da ta farfasa Masa baki mutane ana ta bata hakuri,wani yace kiyi hakuri Nusaiba sabon zuwa ne bai sanki ba,Nusaiba cike da masifa tace ba ruwana ni tunda kaga haka dama ba mutumin kirki bane yazo ya taba min duwawu ta ja tsaki tare da tara Yara Almajirai ta raba musu kosan sadaka ranta ya baci haka ta koma gida Tunda Mamanta taga ta shigo ranta a bace tasan wani ya tsokaneta,Shehu Abbanta Yana zaune Yana shan shayi a gaban yaransa kanana su Kuma yaran kokon da babarsu ta dama na siyarwa shi suke Sha,Shehu ne ya kalleta yace to jarababbiya masifaffiya uban me aka miki marar kunya kullum baki da aiki sai fada da mutane,kiyi fada da mace,kiyi da Namiji,kiyi da Yara gaba Daya zubar min da mutunci kike yi a layin nan,Nusaiba tana kumbura da tashin hankali tace Kai ka sani Abba, Mama kema kin sani bana fada sai da dalili Abba ai dole nayi fada kosan ma na bada Sadaka,Abba yace uwarki Kika yiwa asara ba abinda ya dameni abinda nake so na ji Mene dalilinki na dukan wani? Nusaiba tace duwawu ya taba min duwawun da ba a tabawa sai da sadaki abina me kyau ko uban waye ba sai na illata shi ba,Abba Yana ji shima ransa ya baci Yana son yarsa bai so a lalata masa ita Shuru yayi yace kina da gaskiya,Mama tace kinyi dai dai ya zaci irin yaran nan ne yan talla lalatattu amma laifin mahaifinku ne da ya dauki nauyinku ai da haka bata faru ba Itama Nusaiba Koko ta zuba tasha Amma ubansu a gabansu yake Shan shayi me kauri Kuma uwarsu zai sa ta dafa shayin ya siyo Madara da komai ya hada abinsa da kauri ya Sha a gabansu suna kallo yaran kanana Nusaiba ce Kawai Babba,Babar Shehu ce tazo daga kauye da Leda katuwa ta mikawa Mama tace gashi kanzo ne da nake shanyawa na taho muku da shi kwa rage zafi,ta Mika Mata Sabulun wanki da Omo da yawa sai masara kwano uku da gero kwano biyu,ga wake kwano daya,barkono har da kuli tace nasan halin Shehu ga wannan kwa rage zafi ba yawa,Mama tana ta godiya,su Nusaiba sai Murna sukeyi Watarana sai su kwana Basu ci komai ba lokacin Nusaiba ta ebi Kanzon ta musu dafadukansa suka ci Suka koshi shi kuwa Shehu dama a waje yake cin lafiyayyen abinci yaransa da matarsa ko oho. AsmaBaffa [4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️ 6-10 Official By AsmaBaffa page naku ne Zuwa dare dukkan matan a daki daya suke kwana da iyayensu sabo da rarashin zuciya irin ta Shehu, dukkan yaran basu bacci ba sabo da Babu abincin da zasu ci Shehu suna saman gado shi da Mama su Kuma su Nusaiba suna kasa a kwance saman tabarma, mazan Kuwa suna kitchen a gefe daya suke kwana gefe daya Kuma kwanika da tukwanen abinci, washe gari da rana babu abinda su Nusaiba zasu dafa har ta lallaba kannenta suka tafi Islamiyya wacce dama ita kadai suke zuwa gwara ma kannen Yan primary suna zuwa ta gomnati ita kuwa rabonta da makarantar boko tun mda ta Gama primary,Bayan sun dawo babu abincin da zata ci Ameer Wanda ke binta yace wlh Aunty Nusaiba yunwa muke ji Babu komai da dare,Mama tana jinsu suna zancen ta kalli yaran nata cike da tausayawa tace bani da komai a gidan Nan sai masara sai dari da hamsim,kanwarsu me bin Ameer wato Ihsan tace mu Kai Nika Mana Aunty sai ki Mana tuwo ko ba Dadi sai muci haka tunda mama wake da geron sana'arta take gyarawa Mama tace wannan shawarar tayi ta zaro dari da hamsim tare da mikawa Yasmin ta karba ta siyo waken Miya na hamsim,manjan hamsin sai Maggi dama da daddawa sai wani ragowar tattasai guda uku suka Yi miyar kuka tuwon masara,Suna cin tuwon Mama tana furta Allah ya baki miji me kudi Nusaiba wanda zai kaini paris,Nusaiba tace gwara da kika ce Paris irin su Dubai inda tourist ke cika gari,me za ayi da London Mama baki ta tabe tace tsoron ai London bata Yi ba kasar leburori ce Kuma ko kin samu me kudi karki sake ki taimakawa Shehu ya Gama zaluntar mu,dama wa zai bawa Abba ko sisi cewar ameer suna ta labarinsu,Ihsan tace Ina ruwan Abba Kuma ma ai uba ubane ko me yayi ai taimako Zakayi sai Allah ya buda miki,Nusaiba tace hmm tunda muka taso cikin kuntatawar Abba muke,to ba sai muyi hakuri ba cewar Ihsan,duk abinda ya faru akwai dalili shi yasa idan Kika ji Mata ko Yaya suna abu wasu dole akwai dalili, Siyama ce ta shigo tare da kwada sallama,Nusaiba tace shegiya Charity ce,Ziyama wacce aka fi sani da Charity tafawa sukayi da Nasaiba, Nusaiba ta Fara tsokanarta Charity,itama Siyama tace begin at home, Charity we dey begin at home,Dariya sukayi,Siyama ta kalli Nusaiba tare da furta Wai kayan nan basa isarku ne kullum Hijab da su Atamfa,Nusaiba tace kalleki wa zai kalleki yace Yar musulma ce Kuma bahaushiya kin wani saka Riga da wando ga pcap Kuma wasu tsofaffin da ace ma sababbi ne da sauki,Charity ta kalli kanta tare da furta baza ki gane bs Nusaiba,ya yau me kuka dafa? Mu fa gidanmu yau ko gafzar ma Babu ga jarin Ummi ya karye,Nusaba

Table of Contents

Chapters

71 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71