Chapter 23
Chapter 23
uban kuka a zaune a Kan gadon tashi yayi da pillow daya ya koma Palo saman kujera a can ya kwanta ta biyoshi tana tattaba hannunsa tana kuka tace wlh yau babu bacci a gidan nan haka Suka kwana baiyi bacci ba itama bata Yi ba Kuma bai Mata abinda take so ba tunda shima wulakanta shi take yi a Kai tun Yana nema har ya hakura. Washe gari Mum ce ta shirya da Yamma zuwa gidan su Nusaiba,Mama ce kadai a gidan duk yaran suna makaranta Ameer Yana shago,Mama ta gane Mum sai ta bata rai ta hade rai ko tabarma Mum ce ta gaji da tsaiwa ta jawo kujera ta zauna tace Ina yini, gatsine Mama tayi sannan ta amsa da lafiya bata sake magana ba,Mum tace nasan kin ganeni zuwa nayi akan Maganar Nusaiba abinda takeyi bai dace ba a matsayinki na uwa....dakata cewar Mama ta daga hannu sama tace Kinga nifa bance danki ya zauna da yata dole ba a sakar min yarinya dole ne mun gaji da talaucinsa makaryacin banza yazo da mota ya Mana fafa da kudi ashe karya ne a saketa idan an gaji Zaki Zo kina Mana ihu a gida,Mum Ido ta zaro tace abin har ya Kai haka? Ya wuce haka ma ehe sabo da Haka Kar na Kara jin kin ce ma ke surukata ce,Mum ta mike tace Allah ya kyauta ubangiji ya ganar daku,ameen sai me Kuma cewar Mama,Mum tace babu fita tayi daga gidan Suka hadu da Shehu yace ahhh Kece a gidan ya akayi baki jira na dawo ba? Sannu da zuwa yaushe Kika dawo? Mum tace hmm jiya naji abubuwa marasa dadi har Nusaiba ta Kai karar Aslam Office din Yan hisba Wai ya saketa shine nazo sasanci Amma Maman Yarinyar nan ta bani mamaki taci min mutunci,Shehu ya dinga bawa Mum hakuri yace wlh abinda nake fuskanta Nima kenan,sabo da mamansu nayi kuskuren Hana yarana abinci,Mum tace ashsha bai kamata ba Shehu ko me zata Yi ka dinga ciyar da yaranka,yace Inshaallah ai na Fara gyarawa yanzu Kam Ina Basu abinci amma fa kullum sai dai na auno sabo da idan na zube kayan abinci siyarwa takeyi duk da bai kamata na fada Miki ba amma Abu ne Wanda muke fuskanta Ni da danki ya kamata kisan Nima ta gagareni wlh ban Isa da ita da Nusaiba ba sauran yarana dai na Isa da su amma Banda Mama da Nusaiba kuyi hakuri yaushe za aje Office din Yan Hisban? Mama tace kayi bangarenka Kawai basa ji ne karka damu mun San Kai mutumin kirki ne wlh amma gobe Inshaallah Dana zai saki Nusaiba kowa ya huta,Shehu yace ba damuwa bazan ga laifinku ba,a nan Suka Yi sallama da Mum shi Kuma ya Shiga gida ya budewa Mama wutar masifa amma ko a jikinta tace a saki yata a huta da ya saketa zai sake ganinmu ne,Shehu yace Matukar aka saki Nusaiba to kema kin daina Jin Dadi a gidan nan,dalla rufe min baki me zaka iya, yace ana sakin Nusaiba kema wlh sai naci mutuncinki,Mama tace wlh ba inda zaka Yi Dani ko sakina kayi Ina nan gidan yarana nane sai nayi zaman Yaya na. Yau Nusaiba da bala'inta ta dora tana cewa Allah ya Isa idan baka sakeni ba,Azzalumi ka kawo ni gidan wahala gidan talauci macuci tana ta zage zage. Washe gari ranar da za a koma Wajen Yan Hisba Nusaiba ta riga kowa zuwa har da saka katon Hijab,Abbanta ta gani yazo Shehu sai Mama itama tazo,Mum tazo tare da Aslam,ana zuwa shugaban hisba yayi magana yace Nusaiba Kin nemi saki Kuma kin Fadi dalilinki mijinki bai da lafiya baya iya biya Miki bukatunki bashi da lafiya Nusaiba tace kwarai kuwa,Yace kin shirya biyansa kudin da ya kashe kafin aurenki har sadaki? Ko kin shirya Yi Masa wani auren? Nusaiba tace na shirya biyansa abinda ya kashe,Shehu yace kinyi asara Nusaiba yaushe Kika Zama haka,Aslam yayi murmushi Kawai,Dan hisba yace Aslam me kace kai? Yace ba damuwa taje na saketa Saki daya,Takarda ya rubuta ta saki ya mikawa Nusaiba ta karba harda saka Hannu biyu tace na gode Allah ya saka da Alkhairi Allah ya biya bukata na gode na gode wayyo Allah dadi kashe ni, ta kalli Mama tace Mama Kinga takardarta ki tayani murna yau an sallameni freedom ya samu,Mama ta karbi takardar sakin tana cewa kawo na sa Mata Albarka 'yata,Kowa kallonsu yake da mamaki a wajen,Shehu yace mahaukatan banza. Aslam ya kalleta Kawai ransa a bace bayan an gama Shehu yace akwai shagon da Aslam ya budewa Uwar Yarinyar nan Nusaiba sabo da Haka a maida Masa da shagonsa,Yan hisba suka ce wannan kyauta yayi sai idan da Kansa yace a biya shi,ai kuwa Aslam yace a biya ni,Mama ta bude baki tace dama taimakonka badan Allah kayi ba Dan iskan yaro mutumin banza matsiyaci,Aslam bai saurari Mama ba yace hukuma ta sheda na barwa Shehu Baban Nusaiba shagon gida Kuma dama shi na gyarawa ba ku ba,Shehu yace bani mukullin shago ya Zama nawa,Mama tace akan shagon banza kaje can danka ne a ciki ka karbi shago kayi arziki da shi,Shehu yace ae naji,Aslam yace Ina bukatar sadaki na,Nusaiba nan take tace kawo account a maka transfer, Ya kalli Shehu yace Abba bata accnt dinka Shehu ya karanta nan take Nusaiba ta tura kudin Sadakin dubu dari,Aslam yace Suma kudin na bar maka Abba,Shehu yace Saura lefenka Aslam yace ai sutura ce tazo ta kwashe kayanta na bar mata,Mama tace to mun rabu karka sake na ganka a gidanmu,Aslam yace dole nazo gaida Abba Watarana,Shehu yace kwarai kuwa zamu ci gaba da zumuncin mu Mum tace to Alhmdllh Muje Aslam aka kashe magana kowa ya Kama gabansa,Suna Fitowa Nusaiba ta Kira Sufyan tace an sake ni fa,Sufyan yace Alhmdllh Mama tace kashe wayar sai kinyi Idda yazo ta kashe kuwa Nusaiba sai gida suna murna da shewa Kamar Wanda aka musu gafara Suna zuwa unguwar su ta Fara zuwa gidan su Charity duk gidan ba kowa sai Charity a gida tana zaune tana Jin radio sai ga Nusaiba tayi sallama amsawa tayi Nusaiba ta bude jaka tare da dakko takardar sakinta ta mikawa Siyama tace kin gani na gama da shi idan kina sonsa kije ayi dake ni nan da kike gani na gama da shafinsa, Charity ta karanta tace Yanzu ke a tunaninki farincinki kenan? Nusaiba tace yes Yana da kyau ya cika Namiji amma baida kudi bashi da magana,takardar ta karbe tare da maida ta jaka tace gobe Zan ebo kayan sawata sabo da haka idan kina ciki kije ayi dake ni bani bukata ta juya ta fice,Siyama tayi Shuru tana tausayin Aslam Kamar taje gidan ta duba shi sai kuma ta fasa Sabo da shi kadai ne yanzu bai da Mata ko taje ma baza ta shiga cikin gidansa ba. Bangaren Aslam kuwa Mum ya maida masukinta ya koma gidansa ya kwanta saman kujera shi kadai a gidan Kamar maye shi Kam yaga wulakancin mace ya zauna Yana tunani shi kadai Kamar maraya abin tausayi tashi yayi Kawai ya tafi gidan su Sabeer Abokinsa sabo da ya rage kadaici ,Babar Sabeer tace Aslam mutumin naka Yana bangarensa Dake su Sabeer masu rufin asiri ne
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71