Chapter 14
Chapter 14
lafiyayyen abinci shima haka suna ci suna labari,yace tunda na ganki naji Ina sonki Nusaiba,Dan Allah ki so ni ki aureni,Nusaiba tace Ina da aure Amma karka damu auren ya kusa mutuwa,Matashin me Suna Sufyan yace Alhmdllh Allah yasa ya sakeki da wuri muyi aurenmu,Nusaiba tayi Murmushi tana kora lemo har Suka gama hirarsu wurin magriba ya kawota har bakin gate ta fita tana Masa bye bye ta Shige gidanta,tana Shiga Aslam Yana sama Yana kallonta ta saman yace daga Ina kike Ina motata da Kika fita da ita? Kallonsa tayi Kawai ta dauke Kai,da sauri ya sakko cike da bala'i bata taba sanin ya iya Fushi ba sai yau sai da ta tsorata cikin tsawa yace Ina motata,Tace karka dameni mari ya kwada Mata Karo na farko kenan,Siyama ta fito taga abinda ke faruwa yace Ina motata,Nusaiba ta firgita dafe da kumatu ta fada cikin Palo da gudu Wata wire doguwa Siyama ta Mika masa tace ungo ka zaneta sai ta fito maka da mota karka yarda tunda bata Jin magana,karba yayi ya bita ya zaneta tas yasa key ya kulleta a wani daki yace sai ta fito Masa da mota sannan zai Bude ta,Nusaiba ta fashe da kuka ba shiri ta Kira Mamanta,tana dagawa tace kizo Mama Aslam zai kashe ni wlh ya min dukan tsiya sannan ya kulleni a daki sai na fito Masa da mota,Mama tace karki damu gani nan zuwa gidan duk zafin talauci ne ya dame shi Aisha zaune take a dakinta da aka gyara Mata cikin gidansu na rufin asiri babansu ya sata a gaba da fada yace yanzu ke abinda Kika Yi kin kyauta haihuwa bata Allah bace, ba fa lallai ki samu miji kamar Farooq ba amma tunda haka kika zaba ga gidan nan kizo kiyi ta zama Allah ya bada sa'a wata haihuwar ma ba gwara babu ba da ita wasu yaran ma in Banda su addabi alumma me suke yi yanzu watakil Baki San Wanda Zaki Haifa ba Allah ya dubaki ya hanaki amma baki gode ba Kawai ke dai ki Haihu ai shike nan ya mike ya fice. Aisha tana gida Farooq yaje biko yafi sau Nawa Taki yarda har ya gaji ya hakura,Umma ce ke fada na gaji da kwanciyar nan taki Aisha tunda Kika zo bakya hasala komai a gidan nan sai kwanciya baiwarki ce ni da Zan zauna kullum sai dai na dafa na baki kici ko Sanda kina gidan mijinki Haka kike yi,Aisha ta mike zaune cike da Takaici domin kullum aikin gidan nan kusan ita ke Yi amma mamanta ta hanata sakewa ta Saba da gidanta sai abinda taga dama gaba Daya a takure take jinta,tashi tayi tace gaskiya ni na gaji kullum aiki kullum aiki,idan baki ba Kuwa wallahi babu ke ba cin abinci a gidan nan,Aisha ta zauna Kuwa taki tashi ita kuma Ummanta tana Gama abincin ta hanata ranar yini tayi suna fada da Ummanta kowa na Jin haushin kowa,Aisha sai gidan Yan Uwa taje taci abinci ta dawo. Washe gari ma Aisha ta daura gaba da Ummanta ba Wanda yace wa wani ko kazil suna ta gaba da juna,Umma bata Mata magana itama Aisha haka,Takaici yasa Umma ta Kai karar Aisha wurin Babanta tace Wai ka Haifi yaro a cikinka ya dinga gaba da kai Alhaji ka duba Aisha Wai dani zata Yi gaba,Alhaji yace ba ruwana karki sake kawo min Maganar Aisha ke Kika je Kika zugata ta fito daga gidan mijinta sai ku zauna tare gaki gata nan ai,Umma ta fito tana hawaye tace dama nasan baza ka Mata fada ba tunda ba kaunata kake ba Watarana Naga Alama Aisha dukana zata Fara Yi a gidan Nan,Aisha tana ji ko magana haka tayi mirsisi da ita ta Danna headphone a kunnenta tana Jin Waka tana bi da bakinta baza ma taji fadan ba bare ma ta sakko,kwafa Umma ta ja ta koma ta Fara wanke wankenta Aisha baza tayi ba. Affan tubewa yayi ya Shiga wanka ya fito daure da guntun Towel,Raudat tana bedroom itama ta window tana hango shi Yana shiryawa Yana ta faman shafe shafe da feshe feshen jikinsa da turaruka Yana ta kalailaita har yafi mace,tunda yazo taje sumarsa yafi minti talatin Yana Abu Daya akan Suma,Raudat baki ta tabe ta saka doguwar rigar baccinta me Dan kauri ta kwanta tare da shigewa bargo duk bata da sukuni sabo da Affan zai kalleta komai sai ta faki idonsa take yi,Yana kallonta duk abinda takeyi kayan baccin ma a toilet ta shirya,Dan gajeren wando ya saka sannan ya zauna a bakin bed Yana Shan ruwa,windown ta ya bude glass yace iska Wai zai Sha,Raudat ta mike ta zuge,ya sake tashi ya bude,ta fito daga bargo ta zuge kafin ta koma ya Mika hannu ta cikin window ya jawo rigarta ta manne a jikin bango rankwashinta yayi ta saki Kara yace karki dawo nan na fada Miki idan ba haka ba Zan dawo cikin bedroom dinki,Raudat da taurin Kai tace wlh baka Isa ka hanani sukuni ba ta maida Hannu zata kulle window ya taka windown ya dane ya shigo cikin bedroom dinta ta window daga shi sai gajeren wando,ihu ta saki kwarto Jama'a kwarto,yace yau sai munyi musayan bed ki kwana a nawa yau a naki Zan kwana tace Allah kiyaye ka shafa min kazantarka a gadona,takawa yayi da Niyyar Daukanta tayi sauri ta taka window tare da dirgawa cikin bedroom dinsa tana ihu,Windown ya kulle yaje ya fada saman gadonta ya kwanta,tace Allah ya Isa mugu azzalumi taci gaba da tsaiwa tana kallon dakinsa ya Sha furniture komai me tsada da kyau ko Ina kamshi yake a ciki Kal Kal Tsaki ta ja ta shiga kitchen dinsa kamar na Amarya komai akwai Raudat tace lallai ya shiryawa karya mutumin nan ta duba sosai tana Bude flask taga soyayyar kaza ta hau kaza da ci taci da yawa sai da ta kusa cinyewa sannan ta duba fridge taga wani katon juice an tsiyayi rabi a ciki ta dauka taci gaba da Shan abinta ya leka ta window Yana kallonta bata sani ba kwayar maye ya saka Mata a ciki yasan kwadayinta sai ya kaita ta Sha,Nan da nan Raudat ta Zama wata Yar kwaya ta kasa bacci taji wani karfi ai sai ta hau gyaran gidan ko Ina sai ta share ta goge ko ba dirty Bata Yi bacci ba Yana dakinta Yana sheka bacci akan gadonta ita Kuwa tana ta gyara Masa gida lungu da Sako har kasan bed sai data janye ta share ta goge ta gyara komai ta fada toilet ta wanke ta goge ko Ina ta dawo aiki bai isheta ba ta fito da kayan fridge ta wanke komai ta goge ta maida kayan neat ta dawo ta rasa me zata Yi ma ta bude kofa tsakar dare ta fita ta Fara sharan uban compound da parking space kowa na bacci tana ta fama kafin gari ya waye ta share compound din me dauke da Interlock ya dawo tsaf,flowers din dake compound har su ta share kasansu kafin gari ya waye taji jiki bata sani ba sai data gama ta fada dakinsa inda ta fito lokacin Sallar asuba yayi lokacin kwayar ta Fara sakinta ta window ta sake haurawa zuwa dakinta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71