Skip to content

Chapter 52

Chapter 52

AURENMU Book One Complete Hausa Novel 1,251 words 0 views Progress saved
Download Book

tayi kyau gata da hips,Raudah baki ta bude tana kallo shi bai kula bama Signing ya Mata tare da Mika Mata ta karba ta dauki Hanya zata fita tabi ta gefen Raudah,da yatsa Raudah ta dan taba Duwawun matar, Affan yace mene Haka beb? Tace wannan wace? Yace Secretariat ta ce,tace kana nufin kullum sai kaga wannan? Yace mene ne Wai? Baza ka kawo Namiji ba sai mace to duwawunta kake kallo ko me,kalli fa duwawunta kullum da safe sai ka ganta Ina can na saki baki hai a bude Saurayina yana nan yana kallon duwawun Chinaza,wlh Affan idan ka kalli duwawunta bazan yafe ba,Affan yace Wai in tambayeki baki yarda dani ba,haba Raudah kishin nan naki yayi sau nawa zan fada Miki ke kadai nake da ita,bazan iya cin amanarki ba,I will never ever cheat on you Karki bari muyi auren zargi so kike kishi ya halakar dake,Ni wlh Kawai ka canja sakatariya zuwa sakatare Namiji gaskiya ban yarda ba,yace ba laifin data min baki Isa kisa na sallameta ba Kuma bani na kawota ba Liman ne ai kin san gidansa tunda munje tare kin gaishe shi je ki fada Masa ya canja ta Indai kin San haka zaki to karki sake zuwa Office Dina ya mike tare da dukan table sai data tsorata yace tashi ki tafi gida bana son zargi bana taba ko hannun mace akan kishin banza kizo ki sani gaba ki hanani sakewa ba ke kadai kike da saurayi ba sannan idan niyyar cutarki nayi ta ya Zan Bari ki gane, tashi ki tafi bazan cuceki ba Ina sonki babu wacce nake so sai ke bana ko budurwa bare neman Mata bana son zargi,Raudah mikewa tayi ta Fara hawaye yace oh my God me na miki? tace ni dai karka kalli duwawunta,yace to naji bazan kalla ba idona ma Zan rufe muje na rakaki mota a haka ya lallaba Raudah ta koma gida. Tunda ta koma gida part din Landlady ta shiga suna Hira tace karki yarda da Maza Yar uwa maciya amana ne duk yanda kike da kyau sai sun kula Mata,ki kula da Affan sosai yanda yake da kyau Mata bibiyarsa suke kisa Ido akansa idan ba Haka ba wata ta kwace Miki shi,Landlady ta dinga zuga Raudah,Raudah har da bata labarin sakatariya,tace to ki shiga ki fita a sallameta a canja masa Namiji ko mace me addini, Raudah ta Fara tunanin ya zata yi ai da yamma ta shirya sai gidan Liman Bayan taje sun gaisa da Liman tace Liman wata barna na hango a matsayinka na Malami bai kamata ace an hada mace da namiji suna kebewa ba da sunan aiki Wai sakatariya me yasa baza a Kai Namiji ba duk sakatariya sai ace dole sai mace,Liman ya kalleta yace ai an fi son mace sabo da ita zata iya Zama ko hour nawa ne sabanin Namiji sannan yare sunfi Hausawa kwazo a wajen aiki,amma tunda Naga Kamar kina da manufa kema bari Zan samu mace me addini me saka hijab kullum me zikiri a Kai Masa ita,Raudah taji sanyi a ranta ta zube kasa tana ta godiya. Washe gari Liman ya canjawa Chinaza Wurin aiki ya kaita wajen Daya manager din nasa Affan kuma sai gani yayi an turo mace wata baka amma tana da kyau ba laifi hijab dinta har kasa,ga safa hannu da kafa,suna gaisawa ta saka Nikaf dinta tana magana tana Jan carbi, Affan Yana kallonta tana motsa baki tana cewa Lailahaillah Lailahaillah tana ta fama. Bayan kwana Daya Suka Fara aiki kullum tana aikin Jan carbi idan ta kama ma a Office dinta mikewa take tsaye ta Fara dukan kirji tana zikiri Kamar zaka kashe kanta,Affan har ya gaji da halinta ta cika musu kunne da dukan kirki tana Abu daya tana faman cewa Sayyadina muhammadu ka kula dani Allah...Allah...Allah tana dukan kirji, ta manta ma Affan aikenta yayi ta dakko Masa file sai da ya gaji ya taho da Kansa ya isketa tana ta dukan kirjinta tsawa ya buga Mata tana Adduar bata daina ba tace Sir Allah ya maka gida me kallon bangon gabas,Allah ya baka mace me zikiri....tsawa ya Mata shut up Ina file din da nace ki dakko? tace Sayyadina manzo na shi zai agaza min na ganshi, Assalamualaika ya rasulillah.... Affan yana masifa yace ke lokacin Addua daban lokacin aiki daban,Rabbana.....Rabbana...taci gaba,Affan ya zaro Ido yace ke tafi gidanku na koreki you are fired,zata roke shi ya daka Mata wata uwar tsawa wacce tasa ta fice da gudu,nan take ya Kira Liman ya sanar Masa komai Liman ya canja masa wata macen arniya ce amma Kamar musulma haka take shigarta bata dame jikinta Kuma nutsasiya ce sai dai ita Kuma akwai bin maza Kamar karya haka take in Banda son maza babu abinda ta sani, Raudah tana bala'in sawa Affan Ido akan Shige da ficensa Yau Saturday tana gida amma shi har Saturday Yana zuwa aiki,ya bawa Raudah key din part dinsa zata gyara Masa,tana cikin palon Affan ta gama gyara dakin tana kwance a kujera sai taji knocking tana budewa taga wani Matashin yaro da wata jaka me kyau yace gashi Wai a bawa me gidan inji Farha, Raudah ta karba ta rufe kofar, budewa tayi taga wata flower ta soyayya tana zuba kamshi ga wani agogo na musamman me tsada,ga wani turare kala biyu,bakin ciki ya cikawa Raudah zuciya ta dauki turarukan ta fice can baya tasa dutse ta ragargaje su,ta dawo ta dauki agogon ma ta fita tasa dutse tare da farfasa shi,ta dawo ta jefar da ledar da kafa ta dinga tattake su sai ga Affan ya dawo ya sameta a haka Yana Tambayarta Lafiya? tace Affan wace ta kawo maka gift Affan so kake hawan jini ya kashe ni,taya zaka dinga kula wasu gashi har gift ake kawo maka, Knocking aka musu tare da turo kofar aka shigo Wanda ya kawo gift dinne ya dawo yace dama wannan sakon na dawo karba ashe ba nan tace na kawo ba gaban gidan nan ta aikeni wajen saurayinta nayi mistake,Surrender Raudah tayi kunya ta kamata ta kasa ko motsi har yaron yaga sauran ledar sa flower watse a kasa,Kawai juyawa yayi tare da ficewa, Affan ransa ya baci shima kasa Mata magana yayi ya juya ya fice abinsa ya shiga mota ya bar gidan ya bar Raudah tayi mutuwar zaune tana hawayen bakin cikin halinta na kishi da dana sani,tana so ta daina kishin ta kasa,ga Affan yayi fushi tace Ina Zan sa kaina ta dafe Kai tana hawaye ta jawo Wayarta ta Fara kiransa yaki dagawa,bugun duniya yaki daga Wayar tata tana zaune a part dinsa har 11am bai dawo gida ba gashi idan ta Kira sai ya kashe wayar ma gaba daya, a ranta tayi alkwarin ta daina wannan kishin nata,ga Affan yaki dawowa. AsmaBaffa [4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️ 81-85 Official By AsmaBaffa Page naki ne FUTURE RM Kuka Raudah ke yi yaki daga Wayarta Yana can wajen abokansa sai kusan 12 na dare ya dawo Yana bude kofarsa ya ganta a palonsa,tana ganinsa ta mike tsaye yazo zai wuce ransa a bace ta zube har kasa ta durkusa tana hawaye tace dan Allah kayi hakuri ka yafe min na tuba,Affan ya kalleta

Table of Contents

Chapters

71 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71