Chapter 51
Chapter 51
da yafi maka Suka Yi dariya tare da tafawa,a ranar Aslam duk Wanda yasan ya talauce sai da yaje ya tabbatar Masa ba Haka bane,karshe gidan su Siyama yaje,Kawu da yaji yace banyi mamaki ba tunda dama Sam lokacin baka Yi kala da Wanda ke cikin wani Hali ba,Aunty tace uhm lallai Aslam kayi kokari da kayi haka,Siyama tace a gaishe ku,Aunty tace ai munyi waya dazu dazu ta kirani,Kawu kam cewa yayi fatan yanzu ta kusa haihuwa? Murmushi Aslam yayi cike da kunya bai ce komai ba, Kawu yace ei kaji kunya Mana yanzu ai da a baya baka ji ba so ya rufe maka ido,Aunty tace Kai Kuma ga mita tunda an riga anyi ai sai ka hakura, Aslam ya zaro kudade ya ajiyewa Aunty, Kawu ya raka shi Yana cewa wallahi idan baka kula da 'yata ba sai ka gane kurenka,Indai tayi wata uku banga tayi kiba ba zaka fadawa mutan garinku,Aslam Yana dariya a ransa yace Zama tayi Inshaallah,Yana Fitowa har zai je waje Shehu sai ya fasa yace sai nan gaba tukun ba yanzu ba ya koma gida abinsa. Aslam Yana komawa gida suna hutawa a Palo Siyama tana jikinsa a kwance me aiki ta shigo tace yayi bako,Yace Siyama ta koma sama baza a kallar Masa Mata ba,mikewa tayi ta haura sama,sannan yace a shigo da bakon Jin ance ma'aikacinsa ne,Yana shigowa sai yaga Sufyan ne ya shigo a firgice ya tsuguna a gaban Aslam yace dan Allah Sir kayi hakuri ka yafe min,Aslam yace tashi tashi ba matsala ai ba laifinka bane Sufyan na fahimci komai Kai ai baka da laifi,Sufyan Yana zufa yace ban San matarka bace ka yafe min,Aslam yace please get up ba damuwa aikinka Yana nan,Sufyan yace ba wannan ba Sir cikin Ina Ina yace ...Ni...Ni...nine na zuga Nusaiba akan sai ka saketa na aureta,tun tana gidanka nake zuwa Muna fita yawo,ni nake kaita restaurant munyi soyayya tana da aurenka,a nan ran Aslam yayi mugun baci ya tuna Sanda ko girki baza tayi ba sai dai ta shirya ta fice ashe tare suke fita,yace dama tare kuke fita Kaine kake Neman matar aure me yasa mutane wasu baku da Imani ne,Sufyan yace na tuba dan Allah karka koreni Sir,yace oh yanzu da badan ni bane da shike nan kaci banza ka cuci mutum,ka daina batawa kanka lokaci da nayi Niyyar kyaleka ashe Kai azzalumi ne ba mutumin kirki bane me bin matan wasu na sallameka daga aiki,Sufyan hawaye ya zubo Masa Yana rokonsa yace tashi ka bar min gida cikin tsawa ba shiri ya tashi ya fice,ran Aslam yayi mugun baci sai da Siyama ta fito ta zauna a gefensa tace lafiya yace Wai ashe Wanda ya auri Nusaiba tun tana da aurena yake bibiyar min Mata Yana fita da ita,Siyama nan take kishi ya motsa tace to sai me tunda Kun rabu shi ka kore shi mene na wani cewa Yana bibiyar maka Mata,au dama matarka ce shine harda tashin hankalinka haka da damuwa akan wata banzar Nusaiba,okay na gano son abarka kakeyi sai ya saketa ka dawo da ita,Aslam yace Allah ya baki hakuri ni ba haka nake nufi ba nufina a lokacin ai tana matata ba Wai yanzu ba,Juyawa tayi tace ba komai,fisgota yayi ta fado jikinsa yace ban yarda ba ai Indai kaji bahaushe anyi Masa laifi yace ba komai to wlh da komai dawo nan, dariya ya bata amma ta maze tace ka sakeni nace ba damuwa,yace akwai fa ayita ta Kare a nan baki Isa ba,baki ta turo yayi kissing dinta tare da furta to kiyi hakuri bazan sake ba Ni dai magana ta wuce ya mutu,tace amma kasan.....kafin ta karasa yace dan Allah da annabi kiyi shuru Allah ya baki hakuri ni dai Indai akan wannan ne,Siyama tayi Shuru tana zaune a cinyarsa,yace to ki min magana Mana kiyi murmushi,tace cewa fa kayi dan Allah nayi shuru to nayi shuru,Aslam yace kai Ina Shan wahala dake ai dai nace kiyi hakuri, tace na hakura karka sake min zancen Nusaiba wallahi idan ba Haka ba zaka ga danyen kai,dariya yayi yace to naji bazan sake ba yanzu ma kuskure ne ke kika fassara ni daban,cike da shagwaba tace mutum Kawai ka kawo zancen wata ballagazar banza bazara iskar damuna,Boobs dinta ya cafka ya shiga sarrafata ba shiri tayi shuru duk da cewa ba wani abu zaiyi ba face rage zafi sai ta warke tukun. Washe gari Sufyan Ya sake zuwa gidan Aslam bai same shi ba ya fita yayi murna dama Siyama yake so ya gani Yana compound me aiki tace Wai tazo inji Mijin Nusaiba,Siyama Hijab ta saka ta fito bayan sun gaisa rokarta ya dinga Yi dan Allah madam kisa baki me gidanki ya maidani bakin aikina,Siyama tace kasan kayi kuskure Babba kaima Wanda gaskiya ko ni bazan iya Masa magana ba a kanka kayi hakuri tunda yace a'a to fa sai hakuri kayi hakuri Allah ya baka wani aikin,Yace dan Allah Siyama ki taimaka min,Siyama tace Ina ma Zan iya taimakonka da nayi amma bazan iya ba kayi hakuri Kawai ta juya ta tafi abinta haka Sufyan ya fita jiki ba kwari,washe gari Aslam ya Kira Sufyan ya bashi takardarsa ta sallama daga aiki Yana ta rokonsa amma Ina baya Jin Kira. Sufyan Yana komawa gida ya iske Nusaiba ta dawo daga gidan iyayenta Wanda ko tambayarsa bata Yi ba,takardar ya wulla Mata ransa a bace yace Kinga abinda Kika jawo min ko,kin gani ko Yar iska dabba wacce bata San me take ba jahila,Yar talla, kin Sa na bakantawa Iyayena kin jawo an koreni daga aiki Allah ya Isa tsakanina dake kuma ki koma inda Kika fito gidan ubanki na sake ki saki daya,Nusaiba tace ka sakeni ? Yace ae zata Masa rashin kunya ya hau jibgarta ya Mata jina jina sannan yace wallahi ko hankici baza ki dauka a gidan nan ba baki zo da uwar komai ba duk ni na siya Miki sabo da Haka ki koma gidan ubanki haka,Nusaiba tana kuka jiki duk kulun duka tafi karfin ta taba komai Dan kuwa shi ya siya mata,Haka ta mike tana dingishi zata tafi,Hannunta Sufyan ya fisga ta Fadi a kasa ya dinga janta tana ihu Kamar wani buhun gishiri haka ya bude gate ya jefata waje ya kulle gidansa ya barta a nan tana ta uban kuka har ta gaji ta mike da kyar ta shiga Napep sai gida,tana shiga da kyar take tafiya tana kuka,Mama tana salati ta tafi kanta Shehu Kuwa ficewarsa ma yayi kala bai ce musu ba,Nusaiba ranar ta Sha gashin jiki da ruwan zafi. Raudah da Affan suna ta shirye shiryen bikinsu abubuwa na matsowa,yau Raudah Office din Affan ta ziyarta ba tare da ta fada Masa ba 11am ta tafi da basket na abincinta ta fake da Kai Masa abinci amma a zahiri so take taga ko Mata na zuwa Office din,Yana Office tayi knocking yace yes ta Bude kofa ta shigo yayi mamaki yace yau a gari Yana murna,Zama tayi a kujera tana kallon hadadden Office din tace Sannu da aiki yace yawwa suna haka sai ga wata arniya ta shigo da wasu takardu sanye da gown ko gwiwa bata Kai ba komin surarta a waje ta Sha kitson attach
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71