Chapter 21
Chapter 21
da akwatinsa,Yusuf ya rike hannun Affan yace ka tsaya na samo maka aikin gomnati,yace bana so ko karatun Kai ka saka Ni? Yace to ga jari Zan baka Affan yace bana so ya fisge hannunsa,yace Zan baka aiki a company na dake kano yace bazan taba zuwa aiki ba bani bukata,Yusuf yace jarin milliyoyi Zan baka Affan yace bani bukata,Yusuf yace kafi so kayi ta gayunka kana zaga gari ba sana'a? Yace ae ya fice abinsa ya tafi ya shiga motar Kano daga nan ya irga kudin asusunsa wajen dubu dari hudu ya tara asusun ya Dade tun yana secondary yake uban yawo da shi Yana jefa duk abinda ya samu,Yana zuwa shine ya Kama gidan haya gidan da Raudat ta Kama yace yanzu ya daina wahalar da kansa,duk yawan uban wankan da yake dauka yace ya fita Yana da appointment kasuwa yake zuwa ya zauna a shagon wannan mutumin Alhaji da yace ya dinga zamar Masa Yana biyansa Kuma ba laifi Yana samu sai dai abinda ba naka ba Sam baya isarsa komai sai dai Yana kashe Yan bukatunsa kanana,ranar da baya zuwa kasuwa Kuma Friday,Saturday,Sunday to sai yawo wurin Yan abokan arziki,gashi ya Kama gida me tsada Kuma Kaya me tsada yake sawa yanzu yace ya girma ya gaji da Shan wahalar rayuwa dole sai yaji Dadi,shine data kure Rannan ya rasa ta ya zai biya kudin haya yaje company na Yusuf Yayansa yayi awon gaba da wajen dubu dari biyar ya kirashi ya dinga masifa Wai ya bashi ayyuka da jari duk yaki Yi shine zai ebar Masa kudi bai San dole ce ta sa ba badan dole ba Affan baya bukatar abin hannun Yusuf Raudat bata San ta Sha aiki haka ba sai da safe bayan ta shirya tana karyawa ta tuna da irin aikin da ta Sha jiya sai take ganin kamar a f Mafarki,fita tayi bata sake kula Affan ba bare suyi fada ta tsorata da lamarinsa,taga lallai da gaske ya daura dambar fada da ita,bata San shi Affan ya tsani Mata ba tun daga Kan Nabeela abinda ta Masa,shima Affan bai San Raudat ta dawo daga rakiyar maza ba tace ita da aure har abada haka soyayya ma baza ta sake ba. A hanya Suka hadu da Affan ya dau wanka cikin kana nan Kaya Yana taku dai dai ya Sha kyau dukkan matan dake Compound din basa iya dauke Ido da kallon Affan Dan gayu haka,ta fito zata Shiga motarta Saura kadan suyi karo da juna tace Sannu Ina kwana,Kallon up and down ya Mata ba karya ta zuba kyau ta Sha wata Arabian gown me shegen kyau da tsada kamar Yar India kyakyawa da ita dagwas,Baki ya tabe yace Ina da appointment karki bata min lokaci da gaisuwarki in Banda gulma yaushe Kika Fara gaishe ni a gidan nan,Raudat ta tsaya tana kallonsa ya Mata kyau,yace banyi Niyyar aure yanzu ba fa ko kin kalleni a banza duk wata mace tayi hakuri Affan ba yanzu ba na Mai rabo ne,Allura ce a ruwa me rabo ka dauka,Dariya ya bawa Raudat ya kalleta yace no..no.no fari da kwarkwasa basa Jan hankalina ki Adana abinki ga sugar Daddy dinki,Dariya ta sake saki yace baki da aikin yi ya juya ya tafi Yana wani taku cike da takama irin mazaje,Raudat ce ta fito da motarta daga gidan Yana tafiya a gefen titi har wani tattalewa yake Yi tsabar gayu Yana basarwa wani lokacin Kuma asa Hannu a hantsar Jean din a tattaro Cuccumber yanda gayu ke yin wannan iskancin a titi,Raudat a hankali take binsa a baya da motarta tana kyalkyala dariya tana kallon gayu,Masallaci taga ya shiga ashe Sadaka ya saka ta dari biyar a cikin asusun masallaci ya fito ya Kara gaba tana ta binsa har ya shiga Napep tana bin Napep din Yana kallonta ya gane motarta,cumb ya zaro ya shiga taje Suma kamar me,Dan karamin turare ya dakko a aljihunsa ya fesawa sumar zuwa sajensa Raudat tana saitin Napep din,Lekawa yayi da Kansa yace uwarka ya zageta yana turo mata pink lips dinsa gaba,Dariya ta sake yi ta daki sitiyari Yan dubu dubu na dubu uku ta dago Masa ta glass da hannu yace ta Miko su Ina son su,Raudat glass ta sauke kasa tana kallon titi tana Miko Masa kudin ta napep din kowa na kallo a titi ga Wanda ya kula Affan yasa hannu har cikin motar Yana cikin Napep zai karba Me Napep ya taka da gudu,Yace dalla slow down yayata ce zata bani wasu canji Zan siyo Mata kifi,Me Napep yace sorry Malam yayi Slow Raudat ta sake mikowa tana tuki da hannu daya wuf taji Affan ya karbe kudin kamar zai fado daga Napep din Saura kadan Allah ya kiyaye,motarta ta take da gudu tayi youturn ta wuce Office abinta,Shima ya tafi uzurinsa. Aslam Yana zuwa Office din yace sai jibi zaizo ayi magana yau baida lokaci babarsa ce ta dawo daga kasar waje tana airport zaije ya dakkota Suka ce ba damuwa,Nusaiba ta dinga Jin haushi ita ta matsu ya bata takardarta,Mum ce tazo ya sameta a airport,tana ganin danta a taxi ta Fara hawaye,karasawa yayi ya shiga share Mata hawaye ta rungumeshi tana kuka tace haka Allah yaso Dana, yace Mum me yasa kika zo ban sani ba nace sai na samu aiki zance kizo,Hankalina ya kasa kwanciya sai naga dana,kana ganin Mum kasan itace ta haife shi Fara ce tas shi Kam har ya fita fari ma,da sauri ya siya Mata lemo da ruwan roba Suka shiga taxi zuwa gidan hayarsa,Mum ganin gidan shima sai da tayi kuka,suna shiga ciki Nusaiba ta dawo tana zaune tana kallo,Sallama sukayi ta amsa da kyar ko kallon Mum bata Yi ba,Mum tace yata baki ganni bane ko ba Nusaiba bace nasan ai kin Sanni tunda kafin ayi auren nazo ganinku,Nusaiba baki ta tabe tana Mata kallon banza tace Ina yini daga haka bata sake magana ba,Aslam ne yace Mum zauna ya Kai Jakarta bedroom dinsa,yaje kitchen da Kansa ba abinci ba a dafa ba gashi yaji tana cewa yunwa take ji,Fitowa yayi yace Nusaiba dan dafawa Mum wani abu,direct tace na gaji,da sauri Mum ta kalleta tace ke Wai ko baki da tarbiyya ne? Ae sai kizo ki koya min,Aslam ne yaje ya kwashe ta da Mari uwar tawa zaki fadawa haka ya fisgo wayar charger,Mum ce ta rike shi tace kayiwa Allah ka kyaleta Ina da Yan Uwa Ina da gidan Zama wajen dangina karka damu Indai nice,kaga dakko min jakata muje can,Mum hawaye ne ya zubo Mata tace tabbas Aslam Allah ya jarabceka,Siyama ce ta shigo da sallama,Aslam yaji wani sanyi da farin ciki da ya dade bai ji ba yau yafi murna da zuwan Siyama,Tana zuwa ta Gane Mum ta taba ganinta sau daya da bikin Aslam da Nusaiba,Durkusawa tayi ta gaishe ta,Mum ta amsa da fara'a,Aslam yace kawar Nusaiba ce nasan baza ki gane ta ba,Mum tace Masha Allah ziyara Kika kawo? Siyama tace ae,ya sunanki? Siyama cewar Charity,Yaushe ta zo ne ta tambayi Aslam yace yanzu fa Kinga Ina cewa ta tsaya ma ayi Mata girki taci Wai zata tafi gidan Yan uwanta Mum guda tayi Fushi da gidan danta,Dariya Siyama tayi tace ai kuwa girkina Mummy zata Fara ci
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71