Skip to content

Chapter 61

Chapter 61

AURENMU Book One Complete Hausa Novel 1,244 words 0 views Progress saved
Download Book

zubar da jini mijin bai samu damar saduwa da ita ba suna ta fama su kadai. Kawu da Shehu watansu kusan biyu a kasar waje ana kaisu yawan bude Ido Suka koma Saudiya a karshe Suka sauke farali can suka hadu da Aslam da Siyama, daga nan gida Suka dawo Suka bar su Aslam a can,Shehu yayi bulbul yayi kyan gani gashi suna ta waya da Landlady ita ta Dade da dawowa Nigeria sun gama shirya aurensu ,sai daga baya yaji ma ashe tana da kudi Shehu bayan sun huta da sati biyu ya samu Mama cikin dare suna kwance ya tashe ta yace tashi zamuyi wata magana,Mama ta mike tana Jan tsaki wacce magana ce wannan sai cikin dare mutum yana baccinsa Fadi ni naji mene? yace dama fada Miki zanyi Zan Kara aure wani watan idan Allah ya kaimu za a daura min aure,ban gane ba wanne aure? Wanda Kika sani dai shi Zan Kara ma'ana Zan Kara Mata ku Zama ku biyu,banyi dan naci zarafinki ba,ahayye eheheheeeeee heeeeeeyy Mama tayi shewa tace dama ka dade kana cin amanata ban sani ba kwarto a wanne dakin zaka sakata daki uku ne daki daya namu daki daya na Mata daki daya na maza to Ina waje? Shehu yace Aslam ne zai min auren nan fa kwandala bazan kashe ba shine zai min komai yace, yace idan so nake ma zai bani gida na saka Amarya,nace a'a gwara na hada Kan Yara na gida na Zan kawo ta tunda gidan zaiyi part guda yace zai gina min part daban a cikin gidan nan a wancen part din dana katange ban gina ba,Mama ta fashe da kuka da ihu cikin dare tace amma Allah ya tsinewa Aslam Albarka bazai ga annabi ba,Su Nusaiba sunji ihun Mama Suka firfito,Mama cikin tsakar daren ta fito tsakiyar unguwa tana zunduma ihu da kuruwa sai da makwafta suka fito Shehu yace kowa ya koma gidansa akan Zan Kara aure take wannan haukan,aka dinga tir da halin Mama,da kyar su Nusaiba Suka lallabo ta ta dawo gida tace wallahi yau bazan kwana a daki ba a tsakar gida Zan kwana tun suna lallashi har Suka gaji Suka koma daki ita Kuma Mama a tsaye gari ya waye Mata tana faman zunduma ihu,Shehu bakin ciki Kamar ya kashe shi ta gama tozarta shi,Kamar Wasa da safe sai ga motar yashi tana ta saukewa a kofar gidan Shehu aikin Aslam ne,Mama tace Nusaiba ku fita ku barbaje yashin nan a kasa duk ku tirje shi,sauran yaran Suka ki zuwa Nusaiba ce take taya uwarta kishi ta fito Kamar sabon kamu tana eban yashin tana watsarwa a cikin kwata,Allah ya kawo Shehu ya kamata ya nada Mata shegen duka Kamar zata mutu,Shehu Yana shiga gida Mama taci kwalar Shehu tace idan kayi min kishiya shegiya nake algungumi azzalumi Allah ya isa shine ka samo me kudi zaka auro bazan yafe ba sabo da mu talakawa ne wallahi sai ka sake ni ka sakeni,a gaban yaranta tayiwa Shehu haka Shehu hannunta ya cire daga jikinsa ta karfi yace ki tafi gidan ubanki na sake ki saki daya,Mama Hannu ta daura a Kai tana ihu shine ka sakeni Allah ya Isa kuka take ta tattara nata ya nata cikin fushi ta tasa keyar Nusaiba kadai Suka tafi Kauye garin su Mama su biyu,shi kuwa Shehu yace Allah raka taki gona aka ci gaba da gini. Aslam tsabar muguntarsa ya samu part din Amarya aka kera shi Kamar gidan wani hamshakin me kudi 3room and Palo aka Mata sai kitchen dinta da komai,babu inda za ayi gate wani makwafcin Shehu zai tashi daga unguwar yayi sabon gida Aslam ya siyawa Shehu gidan aka bajeshi tare da hade shi a bangaren Amarya aka mata gate me cin mota biyu abinta ko Ina yasha tiles da Interlock kyau Kam ba a magana gidan ya keru,ita Kuwa bangaren Mama Yana nan sai paint aka mata Kawai shi ma me paint ne yaji kansu ya musu komai siminti ne,Mama Kuwa da Nusaiba tunda Suka koma Kauye garau garau ma da kyar suke samu ga kazanta,daga dankali sai kunu sai tuwo,dambu,danwake shima kadan ake basu,Basu taba sanin da a Rahma suke ba sai da Suka zo Kauye ashe a gidan Shehu ba karamin dadi suke ji ba,sun rame sunyi baki,tsakanin Nusaiba da Mama sai fada suke Yi babu mutunci a tsakaninsu Yau suna zaune a wani dakin kasa Wanda shine makwancinsu sai tabarma wata yarinya ce ta shigo ta ajiye musu kunu a wani dan karamin kofi Wai shine abincin ranansu ai Nusaiba tace wallahi duk da bani da kudin mota gida zan koma wajen mahaifina,Mama ashariya ta dannawa Nusaiba tace sai kin dawo marar mutunci marar biyayya ga uwarta,tace ae naji tafiya zanyi wallahi yau bazan kwana a garin nan ba,Fitowa tayi ta shiga dakin wata tsohuwa a gidan me siyar da daddawar miya,Nusaiba tasan inda matar ke Adana kudinta sai ta dinga Jan Me daddawa da surutu suna ta hira har lokacin Sallah yayi tsohuwar ta mike ta fice zata Yi Alwala tana shiga bandaki Nusaiba ta bude wajen ajiyar ta kwashe dubu uku tasan zai isheta kudin mota har da rara,ranar kuma an daura auren Shehu da Amaryarsa Landlady kayan daki na gayu da tsada Landlady ta zuba a gidan kana gani kasan ba karya,a ranar da yamma Kuma ta tare ba kowa a gidan sai Raudah Wanda ma har Affan yazo Daukanta zasu tafi gida sai ga Nusaiba da Kaya niki niki a Ghana must go ta dawo. Affan ya dau wankan sugar yana tsaye a jikin mota yana jiran Raudansa Nusaiba sai kallonsa takeyi har da goge Fuska ko zai kyasa yace Yana sonta,Jakarta ta rike a hannu a Dan gayence Wai Kar ta kwafsa,zata wuce ta gaban Affan tace sannu lokacin Rauda ta fito taji Nusaiba tana cewa bawan Allah wani gidan kake nema ne? Affan ya kalleta sama da kasa yace ke lafiya Ina ruwanki dani karki jawo min matata yau ta hanani bacci mijin tace ne ni nan da kika ganni bani da amfani wajen Yan matan waje gwara kija tsummar ratuwarki ki Kara gaba gwandala ta baza kici ba,Nusaiba dariya tayi irin ta samu Hanya tace hmm amma matar taka ta birgeni haka ake son mace,Affan yace ae ai ta Isa ne kin san wasu ai basu Kai su mallaki miji ba sabo da Basu iya allonsu ba basu da hali na gari shi yasa ake yawan sakin Mata basu iya Zama da miji ba,Nusaiba sai taji Kamar da ita yake,yace Amaryar Shehu Muka kawo ai Shehu yayi dacen mace yanzu zai samu kwanciyar hankali ance uwar gidansa ballagaza ce ita da yarta Basu San me suke ba ance ma ko a unguwa an tsane su,Nusaiba Kamar ta fashe da kuka bawan Allah ya tsaya sai caba Mata magana yake,ita bata San ma Affan bai San ko Shehun ba sai dazu ya ganshi Suka gaisa labari Suka ji a layin ana fada, Raudah ce ta karaso tana hararar Nusaiba ko kunya Raudah babu akan kishi ganin layin ba kowa sai iya su harda shafa gemun Affan ana Masa shagwaba tace muje ta juyo ta kalli Nusaiba tana Mata up and down,Affan yace baiwar Allah ko Zaki Mana wanke

Table of Contents

Chapters

71 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71