Chapter 33
Chapter 33
katanga ana sharbar kuka tana Jin fitowar kawu ta Fara Zan mutu ubana mahaifi da zaka dawo duniya bakin cikin yayanka shi zaisa ka Fadi ka sake mutuwa ta biyu,idan da zaka dawo duniya kaga yanda yayanka ya rike yarka gudan jininka da nan take zuciyarka zata sake bugawa,Ummata kiyi fatalwa kizo kiga yarki za ayi Mata auren dole yarku ana Mata rikon sakainar kashi,Kawune yazo zai wuce ta kusa da Siyama tace sai nayi cikin Shege Aslam Zan dinga zuwa,Kawu Yana fita ya samo bulalar dalbejiya ya dawo ya hau tsulawa Siyama ta sake barkewa da kuka Yana tafkarta yace Dan ubanki sa'anki ne ni,har kin Isa ki dinga furta mummunar kalma akan Namiji Zaki je ya Miki cikin Shege da Amadou na raye na tabbatar dukan da zai Miki yafi nawa,Siyama taji duka ba sauki Kawu ba wasa zaneta yake ta fada dakinta da gudu ta kulle,Aunty tace ka bani kunya Dauda wallahi ka daina Dakar min yarinya ai da gaskiyarta kowa yasan Aslam mutumin kirki ne mene laifinsa,Siyama tana daga daki ta leko ta window Ido duk hawaye tace dan ma ka samu suruki me addini Siyama yau yini tayi ba ci ba Sha sai kuka a daki,Aunty tayi tayi ta fito taki,Kawu Kuma ya shirya ma ya tafi Kauye sai bayan kwana biyu zai dawo,Aunty tana son yarta tace Siyama so kike Hawan jini ya kamani ko bari to na Kira Aslam a waya yazo idan yazo shi ai Kya bude ki fito,Siyama ta bar Wayarta tun safe a dakin Kawu Aslam Yana ta Kira ba'a dagawa,Aunty tana daukan Wayar Infinix Kiran Aslam ya shigo taga an sa My life,dagawa Aunty tayi Suka gaisa da Aslam yace Aunty Ina Siyama fa?Aunty tace dan Allah kazo kaga tun safe gashi har magriba tayi Taki Fitowa ta kulle kanta a daki ba ci ba Sha,Aslam yace sabo da me? Kazo gidan zan fada maka komai,Aslam yace gani nan,ya taho da sauri. Affan ne ya dawo daga Office Raudat ta fito tana tafiya a durkushe ta rike mara zata shiga mota tana cije lebe, Affan har zai wuce ya dawo yace lafiya? Yaga Raudat tana hawaye tace asibiti zanje bani da lafiya ciwon mara nake yi, Affan ya bude baki yace ahh kice Kawai abin ne yazo,ke Haka kike naki? Rushing day ne? Raudat taki kulashi tana Jin kunya shi ba kunya ce da shi ba,key din motar ya karba yace na gaji amma muje asibitin na kaiki da kaina fatan kin Sa pad karki bata motar,Raudat ta shiga da sauri ya Shiga Suka tafi Suna tafiya yace Allah ya taimake mu da ba maza ne suke abin nan ba ai da mun Shiga uku,Raudat tana fama da kanta bata magana shi kadai yake surutunsa. Na gaji bakwa sharhi yau AsmaBaffa [4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️ 51-55 Official By AsmaBaffa Page naku ne ~s97863205 Aeesha Har Suka isa asibiti bata magana private ya kaita ya bude mota ya fito ya zaga ya bude Mata kofar hannunta ya riko ta fito da kyar Suka Shiga ciki,dake private ne komai kudi dandanan suka ga doctor,suna shiga namijj ne likita ya tambayi meke damunta,tace period ne duk wata nake fama fa ciwon mara Kamar Zan mutu da dai na daina amma yanzu ya dawo,Nan take likita ya rubuta wasu gwaje gwaje suka je aka mata Affan ke biyan kudin da komai,suna dawowa wajen likita ya karbi test din ya duba yace ah kina da aure? tace a'a yace budurwa ce ke? tace ae,yace ai ke ba matsala ma kina yin aure Zaki warke, magunguna ya rubuta Mata yace ki dinga siyen wannan duk wata idan Zaki Fara,tace to Suka fito,takardar ya karba ya siyo magungunan kala biyu tana cikin mota tana jiransa Yana kawowa ta balle ta sha dake wannan ciwon bana karya bane Mota yaja Suka wuce gida tun kafin su je gida Taji sauki sai gata tana cewa kaini gidan wata kawata ba wacce Muka je rannan ba,yace ba inda Zaki je ke kullum a gidan kawaye gida zakije ki huta,Baki ta bude tana kallon ikon Allah kamar ubanta yace na gama magana bana Kuma magana biyu ya wuce gida direct,Shuru tayi har Suka dawo ta fito garau da ita yace take your medications properly ya wuce bangarensa itama ta Shige palonta tana hutawa. Sai dare ya leka ta window palonta jin kida na tashi yasan tabbas kallo takeyi a zaune ya hango ta a kasa ta mike kafafu tana cin gyada tana bushewa kallonta yake sosai ya furta liman me yasa baka zaman abokin Baban Raudat ba sai ka Zama abokin Baban Siyama,ko a suna ba hadi Raudha wow inda Manzon Allah ke kwance haba wa ma zai hada,Liman bazai yuwu ba dole mu tafi Oyo state daga nan ma har Ondo duk ba matsala,Raudat ce taji Kamar ana magana kasa kasa window ta kalla ta ganshi harda dage Mata labile mikewa tayi a hankali ta karaso jikin window ya zama tana palonta yana. Nasa shima Suka tsaya suna kallon juna babu kyaftawa,juyawa tayi da niyyar komawa yace ya jikin a hankali,da sauki ta furta tana Murmushi tace na gode,ko Oyo zamu tafi ne? Harda rera waka wai Affan Ina zaka je ne.....Ni zani Oyo na kwana....tana ta dariya tace da gaske zaka rakani? a ranta tace ai kuwa da jibi jibin nan zamu tafi idan Kuwa baza ka raka Ni ba to gwara nayi zamana a nan Ina ganinka kullum,katse Mata Maganar zucin yayi yace da gaske nake yi Indai babu matsala ni sai nayi masauki a hotel ke kije gidanku,tace ae da gaske gwara naje gida naga Iyayena jibi ka shirya mu tafi,yace an gama zanje wajen ogana na sanar masa tace to tare da komawa ta zauna shima ya juya cikin palonsa ya zauna cike da farin ciki Aslam ne yayi sallam a gidan su Siyama Aunty tana zaune a bakin kofar Siyama Kamar me jira a fito a bata wani abu,Shigowa yayi gidan Aunty ta mike tana cewa sannu da zuwa Aslam,yace yawwa Aunty ya durkusa ya gaida ta da fara'a ta amsa masa sannan tace yarinyar nan daga magana tace Wai zaka Aiko da manya,Kawunta yace shi gudun abin kunya yake tunda ka auri babbar kawarta Kar a zage shi a gari,nace tunda Yara suna San juna ayi abin nan yace shi zagi yake gudu yanzu sabo da Allah ta bari Mana abi abin a hankali Kuma shine sai ta tashi hankalin mutane shine ta kulle kofarta tun sassafe ko ruwa bata Sha ba,Aslam a ransa dadi yaji yace a ransa ta min dai dai a fili yace zata fito ne kiyi Hakuri Aunty Ina kawun fa? Ya tafi Kauye sai jibi zai dawo ta window ya leka dakin Siyama ya ganta ta mike tsaye Kamar an kulle barawo a daki,Murmushi ta sakar Masa shima haka da Ido yace ta fito,jigin windown ta karaso cikin rada tace na fito? Yace ae,tawaye nayi fa,ba a yiwa iyaye tawaye ba nace abi komai a hankali ba,kasa control nayi my anger tayi rising yace to tayi falling down please come out, tace a siyo min Madara a hada min tea Kamar koko sabo da kauri,yace naji fito Aunty ta ganki,na Basu hakuri? Aslam yace a'a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71