Skip to content

Chapter 37

Chapter 37

AURENMU Book One Complete Hausa Novel 1,260 words 0 views Progress saved
Download Book

to shike nan ta turo baki tana cewa ai ba ni kadai ce na damu ba na daina damuwa ma,na daina tunani Kawai uzurina zanyi,dariya Aslam yayi Wai masifa takeyi nan bayan kasa kasa take magana a hankali Kar aji wai,da dan karfi yace haka zaki min,zaka jawo Kawu yaji kayi kasa kasa ta furta tana rufe baki da hannunta, Murmushi ya saki hankalinsa kwance ko a jikinsa yace ki daina fara'a a gidan nan yarinya karki bari a hanaki Saurayinki idan Kika yarda babu Wanda ya Isa ya aure ki,Siyama tace ai Ina ta yin tawaye yau ma kin cin abinci nayi sai 2pm,dariya ta Kama Aslam yace ai baki gwaninta ba dan 2pm kowa lokacin yake cin na rana,tsutsar cikina ta tashi kwana biyu rashin mutunci suke ji,dariya yayi ba shiri yace to kici ki koshi karki zauna da yunwa kinji,Siyama har da kuri tace gobe za aga bala'i sai 4pm zanci abinci,Aslam yasan baza ta iya ba amma yace ni dai na fada Miki karki sake a baki wani sai ni,tace af bata bakinka kake Yi ai ka lashe zaben zuciyata ta nuna kirjinta ta bangaren hagu tace Kaine a nan barin ta sake nuna hagu tace nan ma ka Sha kwana ta nan barin Kaine,tsakiya ma Kaine ka gama mamayeta,dariya yayi yace na gode haka nake so nima haka ko Ina kece you are my world,yace Ina so na tafi,tace ai kuwa Kawu basuyi bacci ba ka jira kawai,Allah yasa da motar Sabeer nazo tare muke , Alhmdllh tace suna ta hirarsu ta masoya ko bacci basa ji har Suka shiga labarin duniya,Siyama tace ta wani Yoruba malamin mu yace babu makaryaci irin bahaushe yanzu idan bashi da lafiya kana cewa ya jiki zai ce da sauki bayan 20mnt sai aji ya mutu,dariya Suka yi Aslam yace su ai idan ba sauki Kawai ba sauki mu musulmai Kuwa ba haka tsarin musulunci yake ba,Wai yasan ba sauki sai yayi karya yace da sauki amma sai aji ya mutu,suna ta nishadinsu basu sani ba sai gani suka Yi 11:30pm,Siyama tace bari na duba maka ko sunyi bacci,Fitowa tayi a hankali taje ta leka fuskar kawu har da sa Hannu ta fifita fuskarsa Shuru Yana ta baccinsa,Aunty ma haka ta sake lekata a hankali tace Aunty Aunty, tana ta bacci shuru da sauri ta koma ta fadawa Aslam sunyi bacci muje,Takalmansa ta kwashe ta rike a hannunta Suka fito Yana gaba Yana tafiyarsa normal har Suka je bakin kofa a hankali ta bude Masa kofar gidan ya fita sannan ta ajiye Masa takalman ya saka ya dawo zauren again sai kace maye tace ka tafi Kar Kawu ya tashi ya Kama ni,rungumeta yayi kamshinsa ya cika Mata hanci me dadi, tace Kai bafa kyau amma shedan yasa tayi Shuru harda lumshe ida ta zagaye shi da hannayenta dagata yayi sama a haka,dariya ta danyi ya ajiyeta a kasa sannan ya janye jikinsa tare da furta good night Yau ki kwana kina mafarkina Kuma ki ganni na aureki Muna soyayya,dariya take kasa kasa tace hmmm ai da na fika murna Zan hango mu a Palo ina zuba maka abinci,zanyi na ganmu a kitchen Muna girki,Aslam yace ban iya girki ba fa ni,dole ka dinga tayani Kuwa Indai kana gida,ki dinga Jin tausayina Baby,ai sabuwar hira Suka dasa ya manta ma Sabeer Yana jiransa a mota,yace zanzo jibi da dare yanzu na gane yanda zamuna yiwa su Kawu tace to sai kazo dare yayi fa 12am ,yace Kuma Sabeer Yana jirana ba,fita yayi ta tsaya a bakin kofar tace sai jibin Zan jiraka yace ko kiss Babu? Tace sai a gidanka yace Allah yasa ta furta ameen Hannu ya Miko Mata ta kai zasu tafa ta janye,dariya ta bashi ya tafi gari duk ba mutane,sai da ya kule sannan ta maida kofa a hankali ta rufe ta dawo tana shigowa Kawu ya farka tare da hasketa da touchlight me mugun haske kamar ta Kama barayi,yace daga Ina kike? tace kofa naje rufewa na zaci ba a rufe ba Kuma ma Ina zanje babu mayafi,Kawu yace to wuce ki kwanta tace to Sum sum ta wuce dakinta ta kwaso kayan shimfidarta ta shimfida a gefen Aunty ta kwanta cike da nishadi sai Murmushi takeyi ita Daya. Aslam kuwa Yana komawa Sabeer har yayi nisa a bacci cikin motar ya tashi Yana masifa a Ina ka zauna haka? Na fada maka fa ka shirya jirana domin Zan iya dadewa tunda gidan Zan shiga nan ya bashi labari a dakinta Suka buya,yace amma ka cika Dan Iska Aslam tab wannan ai ganganci ne,Tsaki yaja yace ba abinda bazan Yi ba akan Star dita,zaka ga star ya yiwa mota key Suka tafi gida a gidan su Sabeer ya kwana yau. Siyama kuwa ta kwanta yau soyayya ta hanata bacci in Banda Aslam ba abinda take tunawa a ranta Katsam taji Aunty tana kiranta kasa kasa kamar munafuka,Siyama tayi Shuru a zuwan bacci takeyi,karaf a kunnen Siyama taji Kawu Yana magana kasa kasa tayi bacci? Aunty tace ae yayi nisa ma baccin,Siyama harda Jan munsharin karya,Kawu yace tashi mu tafi Aunty ta mike kamar barayi Suka Fara tafiya Sadaf Sadaf suka fada daki,Siyama tace iyye tana dariya a boye tace an shiga Uku yanzu Kawu dama bai bar Harkar nan ba ya tsufa ai wannan sai yara,can Kuma tace na tuna Aunty da kuruciyarta itama tana bukata,lallai Kawu dama haka yake Dan is....bakinta ta rufe tace amma ni ya hanani sakewa da masoyina shi ya ja tasa sun tafi duniyancinsu ba komai akwai Allah. Washe gari da safe farkawa tayi taga Auty a shimfidarta kawu ma a tasa,Siyama tace wato da aka gama sai aka dawo dama haka ake Mana wayo,yau zanga tsiya wlh kaima baza kaji Dadi ba Allah ya kaimu dare cewar Siyama,Kawu yace ke sai Rana ta fito ne zakiyi Sallah? ta mike taje da brush tayi tare da Alwala ta koma dakinta bayan tayi sallah taci gaba da baccinta hankali kwance. Wani Daren Yana zagayowa Siyama ta koma palon Aunty tace yau a nan Zan kwana Naga ta tsiya,Siyama tayi baccinta Aunty ba yanda bata Yi da ita ba akan ta koma dakinta taki tashi Wai ita a nan zata kwana,Aunty fita tayi inda suke kwanciya a tsakar gida ta guntsawa Kawu tace nifa yau a matse nake da wuri nake so ga Siyama ta kwanta a palon tace ita a nan zata kwana,Kawu yace rabu da ita bata ji ai,Aunty tace ni a daki Zan kwanta ma can cikin uwar daki,Kawu yace jeki idan baccninta yayi nisa Zan shigo,ai Kuwa Siyama Taki bacci tayi alwala ta saka hijab ta Fara Nafeela ai da tayi raka'a takwas sannan ta zauna saman Sallaya,ga dare Yana yi gashi ko yaushe Kawu ya leka tana zaune a sallaya tana lazimi, window din bedroom din Aunty Kato ne a bude yake dan tsaf mutum zai wuce Siyama tana can bata sani ba tuni Kawu ya haura ta window dama matan aure da iya sanin makamar wayo Aunty tasa kawu ya rufe Mata Baki Kam karma wani sauti ya fita suka gama abinsu ras Kawu ya sake haurawa ta Window ya dawo saman katifarsa Siyama Bata San me akeyi ba tana Palo,Aunty ta gani ta fito

Table of Contents

Chapters

71 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71