Chapter 26
Chapter 26
tarbiya da ilimin boko Dana addini,Yana yin masters sannan Mum ta kyaleshi ta damka Masa dukiyarsa a hannunsa ya koma juya abinsa,Aslam sai da ya Zama hamshakin Mai mudi Kai da gani ba karya bai fuskanci wani Jarabta ba ba ko daya kullum a huce yake,Mum gaba daya sabo da Yana damunta da aiki ya Masa yawa sai ta gudu Qatar inda kanwar Babarta ke aure a can suke zaune abinsu ,duk haka Aslam sai Sanda yaga dama yake zuwa Office Sai wasu kamfanunuwan nasa da yake lekawa Yana kula da ma'aikata tsabar son hutunsa idan yaga dama Sai yayi sati biyu a iya samansa ba tare da ya sakko ko kasa ba,har Allah ya hada shi da su Nusaiba ya sota Kuma ya aure ta a Nan jarabtarsa take shi kam. Aslam fari tas kyakyawa ne ajin farko,dogo ne amma ba can ba haka ba ramamme ba baza Kuma ace me kiba ba,sumarsa baka wuluk ce me yawan gaske taji gyara style style yake Mata Kamar dan turai,hancinsa dogo ne ba can ba bakinsa karami me dauke da jajayen lips,idanuwansa matsagaita masu kyau,sannan fuskarsa ba me Fadi ba Kuma ba sirirya ba komai nasa chas dai dai kowacce mace ta ganshi sai ta kyasa. Siyama Siyama Ahmad Sani Yan Niger ne asalinsu buzaye ne amma tun iyaye da kakanni a Kano Suka taso a Kano Suka gansu daga zuwa Neman kudi Suka dinga hayayyafa har Suka tara dangi a Nan Kano Kuma sun watsu gari daban daban wasu a kauyen Kano wasu a birni,Baban Siyama Ahmad Wanda suke cewa Amadou kanin Dauda ne kawun Siyama bayan Dauda yayi aure Allah bai bashi haihuwa ba gashi su biyu ne rak a wajen iyayensu,Dauda Yana ta aure aure amma ko wacce mace rashin haihuwa yasa take ficewa har ya gaji da aure ya hakura,shi kuwa Ahmad Yana aure shekara daya Matarsa Maryam ta Haifi yarta kyakyawar gaske fara,ai Maryam tana haihuwa abinka da zumunci irin na da Amadou ya kira yayansa yace yayi 'ya matata ta Haifi mace amma na bar maka ita halak malak sabo da haka Suna ma Kai zaka zaba Mata,Dauda harda kukan farin ciki yace na zabi Siyama a saka mata,ai Kuwa yarinya taci suna Siyama,Dauda dalilin kyautar yarsa Siyama ya nemi Hajara wato Aunty wacce bazawara ce itama bata haihuwa Kawai ya aureta tunda lalurarsu iri daya ce. Ranar da aka yaye Siyama Amadou ya dakko Siyama da kayanta kaf ya kawowa Dauda har gidansa Dake rijiyar lemo Kano yace Yaya ga yarka na kawo maka ta damemu da fitina,Dauda yace a bani a bata dama duk kewarta ta dameni ya karbe Siyama,Amadou akan hanyarsa ta komawa gida mota ta bige shi Nan take ya rasu,Dauda Kamar zaiyi hauka har gobe idan ya tuna Amadou sai ya zubar da hawaye,Siyama ta taso cikin gata so da kulawa sai abinda take so duk duniya ba Wanda Dauda yake so sama da Siyama,itama Aunty ta dauki son duniya ta dorawa Siyama sakamakon bata taba haihuwa ba,macece me iya Zama da mutane ga iya raino da kula haka ta tsaya akan Siyama har ta Isa zuwa makaranta Suka sata a makarantar boko da Islamiyya,data Kara girma har makarantar dare take zuwa shi yasa Siyama take da kokari primary ma private aka saka ta shi yasa take Jin turanci sosai,.. Sun taso a unguwar tare da Nusaiba dake layinsu daya ita Nusaiba ma har primary ta gomnati tayi sabo da talauci,Sanda Shehu yayi Dan kudin nasa basu taso ba,Kuma ba kudi bane rufin asiri ne Kawai, ana Kai Siyama Secondary school Suka hadu da Nusaiba a can,ko a class Nusaiba dama bata da mutunci idan ta Raina kurar mutum zaiga wulakanci,Bata kawa da mutum sai tasan kun fita arziki shine zata Shige maka abinda ya hadata kawance da Siyama kenan idan taje gidan su Siyama zata ci shinkafa da Miya su kuwa gidansu sai a kwashe wata guda ba ayi shinkafa da Miya ba,suna Ss2 Nusaiba ta daina zuwa makaranta sai tallan kosai kannenta ke zuwa sabo da talauci gwara ta Nemo musu ko zasu samu abincin ci,Siyama Kuwa ita da sauran sun Gama secondary school suna da shekaru 19 tana zaune sai dai tallan su har ta Kara shekara hudu Wanda da akwai kudi da tuni sun Gama degree,yanzu sun Kai 23yrs, Yan Mata ne sosai . Siyama doguwa ce Fara me round face me dauke da dogon hancinta zarkadede,idanuwanta manya dasu masu kyau kamar tana Jin bacci haka take sai ka rantse bacci take ji kullum a Haka take,gashi ne da ita sosai gata da dan jikinta mul mul ba Kashi sai dai ba me kiba za a ce ba,komai mashaallah. Nusaiba Kuwa Yan asalin Rogo ne wajen jahar Kano Shehu dan dangi ne Yana da Yan Uwa da yawa sai dai Basu da Hali duk talakawa ne a kauyen Rogo,itama Mama tana da nata Dangin da yawa a Rogo amma guda Daya ce wacce suke uwa Daya uba daya sauran duk dangi ne, Amma duk cikinsu babu me iyaye duk sun mutu tunda Suma sun tsufa bare iyayensu sai dangi,Mama me Suna Bara'atu Yar asalin kauyen kayau ce a Rogo ma a wani mugun Kauye take Wanda basu karatu Babu ilimin Addink bare boko,a haka Shehu ya nace sai ita shi yaga fetsarariya dama sai da aka fada kaf gidan su Mama basu da mutunci a kauyen basu da Kara Basu da kunya su kamar a jininsu yake Imaninsu kudi Kawai,Shehu yace ba komai zai sata a makaranta,Bayan ya aureta tun Yana zuwa cikin birni cirani har ya mallaki filinsa ya Gina ya dakko Mama daga Kauye ya dawo da ita birni,ya sata a makarantar yaki da jahilci ta matan aure inda ake koya musu ilimin addini da karatun hausa Mama ita ko a makarantar ma dakikiya ce sam bata ganewa sai ta dade a aya Daya,aya daya sai ta kwashe satikai bata iya ba,a Haka ma dan Shehu Yana koya Mata a gida,idan Suka Zo karatu ta dinga kunkuni da masifa kenan Shehu har rankwashinta yasha Yi sabo da jahilci da kin karatu,Fatiha ma Sai da ya tsaya a kanta sosai ta iya,ya koya Mata wankan haila da komai,Sallah ma Shehu ya koya Mata,a hankali Mama ta Fara Zama tsagera a unguwar,duk Sanda Shehu ya siyo kayan abinci kwana kadan sai yaji tace ya kare, sai da masu shagunan unguwar Suka fada Masa cewar matarsa fa tana kawo musu su shinkafa,taliya etc suna siya ya sa ido Ashe siyarwa takeyi ta soke kudin,Shehu ya Kai kararta gidansu yafi a irga karshe ma Dangin Mama suci ubansa ya dawo bashi da bakin fadawa Yan Uwansa tunda dama tun farko sun hanashi yaki ji,ana Haka Mama ta haifo yarta mace,Shehu yace zai maida sunan uwarsa Mama tace bai Isa ba ita tun tana yarinya take mafarkin yarta ana fada Mata a mafarki sunan yarki Nusaiba,Shehu yace sai kace wata manzo ko waliyiya to baki Isa ba,Suka dinga fada karshe dole ya hakura ya saka suna Nusaiba ta Haifi Danta na biyu Nan ma ta kafa ta tsare tace Ameer ake yayi shi za a sawa danta,Shehu ya saka,ta haifo Ihsan Tace yanzu an waye sunayen larabawa ake yayi Ihsan kawai,Shehu ya kyaleta ya saka sai da kyar da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71