Skip to content

Chapter 50

Chapter 50

AURENMU Book One Complete Hausa Novel 1,262 words 0 views Progress saved
Download Book

Bayan taje sun gaisa da Liman tace Liman wata barna na hango a matsayinka na Malami bai kamata ace an hada mace da namiji suna kebewa ba da sunan aiki Wai sakatariya me yasa baza a Kai Namiji ba duk sakatariya sai ace dole sai mace,Liman ya kalleta yace ai an fi son mace sabo da ita zata iya Zama ko hour nawa ne sabanin Namiji sannan yare sunfi Hausawa kwazo a wajen aiki,amma tunda Naga Kamar kina da manufa kema bari Zan samu mace me addini me saka hijab kullum me zikiri a Kai Masa ita,Raudah taji sanyi a ranta ta zube kasa tana ta godiya. Washe gari Liman ya canjawa Chinaza Wurin aiki ya kaita wajen Daya manager din nasa Affan kuma sai gani yayi an turo mace wata baka amma tana da kyau ba laifi hijab dinta har kasa,ga safa hannu da kafa,suna gaisawa ta saka Nikaf dinta tana magana tana Jan carbi, Affan Yana kallonta tana motsa baki tana cewa Lailahaillah Lailahaillah tana ta fama. Bayan kwana Daya Suka Fara aiki kullum tana aikin Jan carbi idan ta kama ma a Office dinta mikewa take tsaye ta Fara dukan kirji tana zikiri Kamar zaka kashe kanta,Affan har ya gaji da halinta ta cika musu kunne da dukan kirki tana Abu daya tana faman cewa Sayyadina muhammadu ka kula dani Allah...Allah...Allah tana dukan kirji, ta manta ma Affan aikenta yayi ta dakko Masa file sai da ya gaji ya taho da Kansa ya isketa tana ta dukan kirjinta tsawa ya buga Mata tana Adduar bata daina ba tace Sir Allah ya maka gida me kallon bangon gabas,Allah ya baka mace me zikiri....tsawa ya Mata shut up Ina file din da nace ki dakko? tace Sayyadina manzo na shi zai agaza min na ganshi, Assalamualaika ya rasulillah.... Affan yana masifa yace ke lokacin Addua daban lokacin aiki daban,Rabbana.....Rabbana...taci gaba,Affan ya zaro Ido yace ke tafi gidanku na koreki you are fired,zata roke shi ya daka Mata wata uwar tsawa wacce tasa ta fice da gudu,nan take ya Kira Liman ya sanar Masa komai Liman ya canja masa wata macen arniya ce amma Kamar musulma haka take shigarta bata dame jikinta Kuma nutsasiya ce sai dai ita Kuma akwai bin maza Kamar karya haka take in Banda son maza babu abinda ta sani, Raudah tana bala'in sawa Affan Ido akan Shige da ficensa Yau Saturday tana gida amma shi har Saturday Yana zuwa aiki,ya bawa Raudah key din part dinsa zata gyara Masa,tana cikin palon Affan ta gama gyara dakin tana kwance a kujera sai taji knocking tana budewa taga wani Matashin yaro da wata jaka me kyau yace gashi Wai a bawa me gidan inji Farha, Raudah ta karba ta rufe kofar, budewa tayi taga wata flower ta soyayya tana zuba kamshi ga wani agogo na musamman me tsada,ga wani turare kala biyu,bakin ciki ya cikawa Raudah zuciya ta dauki turarukan ta fice can baya tasa dutse ta ragargaje su,ta dawo ta dauki agogon ma ta fita tasa dutse tare da farfasa shi,ta dawo ta jefar da ledar da kafa ta dinga tattake su sai ga Affan ya dawo ya sameta a haka Yana Tambayarta Lafiya? tace Affan wace ta kawo maka gift Affan so kake hawan jini ya kashe ni,taya zaka dinga kula wasu gashi har gift ake kawo maka, Knocking aka musu tare da turo kofar aka shigo Wanda ya kawo gift dinne ya dawo yace dama wannan sakon na dawo karba ashe ba nan tace na kawo ba gaban gidan nan ta aikeni wajen saurayinta nayi mistake,Surrender Raudah tayi kunya ta kamata ta kasa ko motsi har yaron yaga sauran ledar sa flower watse a kasa,Kawai juyawa yayi tare da ficewa, Affan ransa ya baci shima kasa Mata magana yayi ya juya ya fice abinsa ya shiga mota ya bar gidan ya bar Raudah tayi mutuwar zaune tana hawayen bakin cikin halinta na kishi da dana sani,tana so ta daina kishin ta kasa,ga Affan yayi fushi tace Ina Zan sa kaina ta dafe Kai tana hawaye ta jawo Wayarta ta Fara kiransa yaki dagawa,bugun duniya yaki daga Wayar tata tana zaune a part dinsa har 11am bai dawo gida ba gashi idan ta Kira sai ya kashe wayar ma gaba daya, a ranta tayi alkwarin ta daina wannan kishin nata,ga Affan yaki dawowa. AsmaBaffa[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️ AUREN MU🛢️ 76-80 Official By AsmaBaffa Page naki ne AUTARESS Kofar gidan da Mum take yayi parking sai gasu ita da Hajiya Zainab sun dawo daga unguwa,Aslam Suka gani ya fito daga cikin hadaddiyar motar ya dakko Leda da flask,Mum tace daga Ina haka? ciki Suka shiga gaba Daya Yana cewa daga gida Mana,sai da Suka zauna a Palo ya gaishe su,ya ajiyewa Mum flask din da ledar a gabanta tare da cewa gashi inji Siyama,Mum tace me Muka samu Kuma ta bude flask din taga farfesun kaji ledar ta Bude ta washe baki tace an gode Mata Allah ya Mata albarka,yanzu nasan Ina da suruka,Aslam yayi murmushi ganin Mum ta Kira Zainab ta kawo plate ta ebi nata ta bawa Zainab nasu,Mum ta Fara yagar kaza tana cewa wannan yarinya Allah ya mata Albarka,Zainab ma tana ci tace haka ake son suruka wasu Kuwa Kai da kayan danka ya gagareka,Aslam yace ni baza ku sa min albarka? Mum tace Kai Dan Allah rufe mana baki muna Jin dadin mu wannan motar ma ta waye ne nasan baka aro kayan wasu,Aslam yace tawa ce Mana ya Fara bawa su Mum labarin komai har ya gama,Mum tana tsotse Kashi tace amma ka wahalar damu har hawan jini sai da yakamani,kiyi Hakuri Mum kin San dalilin da yasa nayi haka yanzu,ae hakan ma kayi dai dai gashi Yanzu mun samu Yar arziki irin albarka,amma cuta sai da ta kamani,Ki zabi kasar da kike so Mum na kaiki ki huta,tace ba yanzu ba aure zanyi na tafi da mijina,Dariya ta bawa Aslam yace kina son aure Mum?wa yaki ibada da ace Ina da mijina ai bazan dinga yawo kasa kasa ba da sauran kuriciyata fa,Aslam yace Mum na Miki miji, Waye? Ki auri Shehu Baban Nusaiba,Mum tace Kai nifa bana son kazami Indai tsoho ba me tsafta bane karka kawo min shi bare wannan Yarinyar tasa marar kunya bada ni ba,dariya Suka yi,Baffa Shehu ai Dan gayu ne kin girme shi fa sosai sai dai yayi manage dake cewar Aslam,Mum tace tashi ka tafi ka San inda dare yayi maka tunda magana zaka fada min,Yace Flask dinmu fa? Hajiya Zainab tace ai ba bata zaiyi ba in ka dawo sai a baka,yace idan tana son amfani da abinta fa matar gidan,Mum tayi dariya tace duk cikin zumudin Amarya ne rabu da shi Aslam kuwa kitchen ya shiga da Kansa ya dakko wani flask din da Kansa ya juye ragowar a ciki ya dauke flask dinsu ya rufe ya musu sallama ya tafi Wajen Sabeer yaje shima Sabeer tunda yaji ya dinga masifa yace ka wahalar damu wallahi sai ka biyani dubu dari biyar dina dana taimakeka da ita ai ka fini karfi,Aslam Yana dariya yace dama badan Allah ka bani ba,yace na fasa taimakon ka dawo min da abata nima na kusa aure,yace Zan maka transfer din tsiyarka yace

Table of Contents

Chapters

71 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71