Chapter 8
Chapter 8
bare ma su roki me gadi ya basu aro. Mun jawa kanmu mun Sha kokonmu amma Muka ki godewa Allah cewar Charity a haka me aiki ta sake kawo musu lafiyayyen abinci haka suka sake cika cikinsu amma idan suka tuna gida sai kuka har bacci ya kwashe su. Washe Gari Suka Yi Sallah suka fito suna tunanin ganin wani ba kowa sai me aiki tana girki sunyi sunyi akan ta fadawa oga zasu tafi Amma tace ya Mata warning baza ta je ba,Wasa Wasa har Suka kwashe kwana uku a gidan basu ga ko Kare ba tun suna cin abinci suna murna har bacin rai da tsoro ya hanasu ci,ga abincin suna gani amma sun kasa ci ba kwanciyar hankali. Gidan su Nusaiba tun suna tunanin yawan banza ta tafi har Suka dawo kuka da addua,Shehu sabo da Yana cikin bacin rai har da basu kudin cefane,Mama ta dafa shinkafa da wake da Mai da yaji,Ihsan tace ga shinkafa yau zamu ci amma abin haushin Aunty bata nan suna bakin ciki suna murna ta wani bangaren zasu ci shinkafa,mutanen layin sai jaje ake musu ana tayasu da addua Allah ya bayyana su Nusaiba,Shehu akan baya so ya kashe kudinsa yace ba inda Zan Kai Sadaka a tayani da addua da kaina Zan roki Allah watakil ma nafi malaman matsayi a wajen Allah muyi addua da kanmu,Mama tana hawaye komai na sana'arta ya tsaya yarta ta bace tace ai ba malamai aka ce ka bi ba cewa akayi ka bada a masallaci a tayamu da addua sai kayiwa Almajirai Sadaka,Shehu yace ai ke baki San Allah ba tunaninku mata kullum a bi malamai idan baza kiyi Addua da kanki ba ki barshi,Mama cikin jarinta ta dauki dari biyar ta bawa Ameer danta tace ungo kaje masallacin juma'a kaga yau Juma'a ka siyi ruwa na du kudin ka rabawa Alummar annabi Allah ya bayyana Mana su Nusaiba,Ameer ya karba da sauri ya tafi zai siyi ruwa ya rabawa Alummar annabi Sadaqa,Mama tana da filinta na gado ta ajiye abinta,sabo da tayi Sadaka Allah ya bayyana Mata yarta tace zata siyar da filin,Shehu Sadakar dari biyu ya kasa Amma tana daga filinta zata siyar yace zai siya ya lallaba Mama zai siyi fili,filin a Kauye yake Bai wuce dubu dari biyu ba amma Shehu yace filin Bai wuce dubu dari da talatin ba Mama bata San Kan komai ba yace ya siya zai bada kudi ya lallaba ya karbe takardu tayi signing da komai shima haka ba shedu bata fadawa kowa ba Shehu ya hana kudi tana ta binsa karshe ma Sai labari taji ya siyar da filin dubu dari uku Kuma ko ficika bai bata ba,idan tayi yaji ta tafi ta barwa wa yaranta ga yarta har sati guda shuru,Mama ta kwana takeyi tana kuka tana kaiwa Allah kukanta. Charity idonsu duk ya kumbura sabo da kuka basu ga kowa ba Kuma an hanasu fita,Oga zai iya sati biyu a gida ba tare da ya leko ko compound ba Haka yake shi,Sun wanke kayansu ya bushe sun maida shi jikiksu bayan sunyi wanka,Palo Suka dawo Suka zauna babu Wacce tayiwa Yar uwarta magana sunyi jugum jugum a Palo,Tv tana yi Amma ko kallonta basu Yi,kamshi suka ji ya mamaye palon,wani me uban kyau Suka gani yana sakkowa daga steps sanye yake cikin wani silk doguwar Riga Kuma armless gefe da gefe an tsagata Silver color takalminsa ma haka sumarsa ta Sha gyara na musamman fadar kyawunsa bata baki ne komai nasa na daban ne,sheki Kawai yake da walwali,kwarjininsa ya kamasu Suka kasa magana har ya samu kujera ya zauna irin Zama na isassu na masu Hannu da shuni kana gani kasan Hutu ya ratsa shi. Gyaran murya yayi kadan lokacin Charity tace Ina yini cike da Ladabi Nusaiba Kuwa ta kafe shi da Ido tana kallonsa sai da Charity ta dan bigi hannunta sannan tace Ina kwana au na manta Ina yini? A takaice ya amsa ya kalli Nusaiba yace ke kina kama da Baban Mum da gani jikarsa ce ko?,da sauri Nusaiba tace ae,ya kalli Charity yace ke da alama Yar Hajjo ce ta gangare ko? Charity tace ae,yace sorry Allah yaji kanta,Charity tace Ameen harda kuka dan a barsu su tafi tace ka tuna min da babana Yana can shi daya gwara na koma, Oga yace har Kun gaji baza ku tafi yanzu ba ya Dace ku huta sosai ya furta tare da mikewa ya fice suna ji ya shiga mota, Nusaiba suka sake fashewa da kuka,tunda ya fita bai dawo ba sai tsakar dare sunyi bacci lokacin harda siyo musu kayan makulashe da safe suna tashi suka gani a bakin kofar su Leda guda, Charity tace wlh da wannan kayan dadin gwara muna gidan Iyayenmu,Nusaiba ta kalleta tace hmm ai ni abin ya isheni gashi Muna fadar gaskiya za a kamamu sai gidan kaso masu kudi zasu Yi tunanin ma da abinda ya kawo mu,ai Kar mu sake mu fada Kuma Kinga Yana kamamu sai Iyayenmu sunji abinda muke yi,Nusaiba tace badluck, har suka gaji suka fito suna zaga gidan ko Ina sai da suka gani sun Sha kallo amma Sam abin baya birge su burunsu su koma gida,Palo suka koma sai gashi a zaune Yana kallon film sannan Yana latsa wayarsa. Zama suka Yi can nesa da shi yace hope Kuna Jin dadin birni ya furta Yana kallon Nusaiba, Charity tace sosai ma Alhmdllh amma gida muke so mu tafi yau Iyayenmu zasu Mana fada,Ogan yace ai Indai kunce a nan kuke ba matsala kadaici ya min yawa kuyi zamanku kwa dan ebe min kewa ko ba komai na dinga Jin motsin mutane, Nusaiba ce ta kalli Charity suka hada Ido idanuwansu ya ciko da kwalla zasu Yi kuka ya tashi ya haura sama shi dama ya gaji da Shuru shi kadai a gida ga Yan uwa sunzo yaji motsin mutane ko da na yan satikai ne, Yana fita Charity tace kamar fa wannan mutumin kwakwalwarsa a takashinsa take ta kowa a kansa aka Masa brain amma Banda shi tasa a takashi aka Masa ita baya tunanin Iyayen nu chab Aisha ce ta shiga motarta tana tukawa a layin har makwafta suka tsiri zuwa suna gaida su Sabo da aga ta siyi mota ko Ina da key a hannunta tana karkadawa,Sunday Yana gida Aisha anci gayu ta fito tace Maggi fa ya Kare sannan ba kayan miya ko yaji Banda shi bare nayi Mana shinkafa da wake,Farooq yace Wai ku Mata me yasa baku da hankali ne sau Nawa Ina fada miki idan Abu ya kusa karewa ki sanar min amma kinki ji sai komai ya Kare kat Zaki zo ki fada min to yanzu kin San wata yayi nisa ba kudi sai mu yini haka ya furta Yana Jan tsaki,Aisha tace Farooq kafa isheni tsakani da Allah na gaji Kai ba haihuwa kake ba how many years? 5yrs da auren mu maimakon ka lallaba ni sabo da nice ke hakuri Ina taimaka maka wajen Zama da Kai ba haihuwa Alfarma fa nake maka,for how long Zan dinga jira ba haihuwa ta juya ta saka Hijab ta fice ba ko neman izini haka tasa kudinta tayi cefane ta dafa abincinta ita kadai taci na Rana ta boye
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71