Chapter 30
Chapter 30
Mata turarukan wuta masu kyau a Leda,Affan ya kalli Raudat kadan ya juya da mota Suka hau kwalta sannan yace mijinta har da rakiya Ina ruwansa dake Kai wasu mazan ma Sai a barsu gaba Daya wasu rako Suka yo,Raudat ana ta Jin dadi har da narkewa a jikin mota taki magana ta rasa yanda zata Yi sabo da murna,yace naji kinyi shuru? Raudat ana wani tararrabewa an samu waje tace kaina ke min ciwo a ranta tana istingifari da karyar da ta shararo, Sannu ya furta tace yawwa,yace a tsaya a siya Miki paracetamol? No ta furta Ina da shi a gida yace sai a kyaleki kina cuta Kuma, yayi parking bakin wani chemist ya shiga ya siyo Mata paracetamol da ruwan roba ya dawo dauke da Leda a hannu daya hannun a aljihu Yana taku dai dai yana zuwa ya Mika Mata yace Sha,ai Raudat tabara ta fara tace bana son magani Allah,yace ashe Kuwa baza mu koma gida ba a nan zamu zauna harda gyara parking,farin ciki yasa Raudat ta Kara narkewa tace please kayi hakuri,Affan tsigar jikinsa tashi takeyi idan tana Masa Shagwabar nan tana tuna Masa da Nabeela,Murfin robar ruwan ya balle ya balli paracetamol biyu ya zuba a cikin murfin ya dan zuba ruwa ya wani narka maganin sai kace zai bawa dan yaye yace tsaya na baki to Yana kallonta,sabo da shine zai bata kalau take amma tace to tayi wani kasa da kai lagaf, Hannu yasa tare da dago kanta a hankali harda cewa haa ta bude ya zuba Mata ta shanye ji tayi kamar ta Sha alawa sabo da shi ya bata, ruwa ya bata a baki ta shanye abinta ta wani kwanta a saman kujera Yana cewa sannu yaki tashin mota sai data kwashe 30mnt tace naji sauki har na daina ji sannan ya yiwa motarsa key yace me kike son ci? tace Ice cream ai Kuwa ya tsaya ya siya Mata wata katuwar roba guda biyu da su yogourt me sanyi ya dawo ya leko ta windown ta yace abinci fa ranki ya dade Hajiya Aunty? tace naci a wajen Hafsat,duk da haka sai da ya siyo Mata tsire lafiyayye sannan ya shiga mota Suka tafi, ana tafiya tana Shan ice cream dinta Yana driving yace ni bazan Sha ba? tace Sorry gashi yace tuki nake ai tace to sai munje gida,yace ki bani a Baki ,Ido Raudat ta zaro taji kunya tace bazan iya ba,yace kaji locality me nake ji ba dadi haka sai kace wani suna Siyama,dariya tayi taki bashi bai ce komai ba har ya kawota gida tayi godiya ta wuce part dinta shima ya shige wajen Sayyeed,tana zuwa tayi sufa akan gadonta tana tsalle da murna. Siyama kuwa bayan ta Gama kukanta har kwana uku bata ga Aslam ba tana ta faman tunaninsa katsam ta fito daga wanka da Yamma yaro ya shigo yace Wai ance Siyama tazo inji Aslam,da sauri tace kace gani nan, ai ko Mai bata shafa ba ta zura skert da riga na material ta saka hijab me Kama da doguwar riga har kasa ta tafi wajensa,tana zuwa yaga fuskarta duk ruwa tayi wani fresh yace daga wanka Kika fito ne? Siyama tace ae Ina yini ya amsa da lafiya lau,tace rannan kazo Wanda ka gani ba Saurayina bane ba sonsa nake ba,yace in ma kina son abinki Charity me zance ni zuwa nayi na duba lafiyarki tunda yanzu kin watsar dani kinyi hadadde,Siyama kamar zata Yi kuka tace ba Saurayina bane tiryan tiryan ta bawa Aslam labarin Affan,yace hmm kice miji aka miki,a'a nifa ance maka sai na yarda za ayi auren idan bana so shike nan Kuma bana sonsa,Aslam ya sake cewa bari mu Fara ja baya Siyama tace kash kajika da wani zance akan Affan din me aka yi aka yi shi wani banza da shi zaka bani kunya Allah yawa kake yi,Aslam yace to shi kina ganinsa me kudi,kudin me wa yake ta kudinsa nawa ya tara,Aslam Yana ta bugar cikin Siyama bata gane ba,sai da ya gama Jin komai sannan yace to Hajiyar wanka in tafi ko na tsaya akwai labari? Siyama tace jeka,yace oh korata ma kike Yi kenan,Siyama tace nayi Fushi sai ka dinga min wasu maganganu haka marasa dadi,Aslam a hankali yace Ina sonki Siyama.....Baki ta bude tace so kuma Aslam? Yace ae ba sai kin so ni ba Kawai na fada Miki mind dina na gaji da hiding, idan Kika bari Kika auri wani laifinki ne na daina kulaki Kuma har abada ko a hanya gwara ma ki aure ni,Siyama ta rasa wanne irin murna zata Yi ta boye tace tun tuni sai da ka bari aka turo min wani wajena yanzu ya zanyi da Kawu? Yace ki San yanda Zaki yi please I love you,ban taba son wata haka ba sai ke sai Ina kusa dake nake gane ni Namiji ne tun tuni tun farkon zuwanku gidana na zaci ba so bane Kawai yasa Naga Nusaiba tafi min na aureta,Siyama ta rufe baki a ranta tace zuki ta mallen maza kenan sabo da ba Nusaiba,ganin bata da Niyyar bashi amsa ya juya ya Mata sallama ya tafi,Siyama Kuma ta Shige gida da sauri tana zuwa tayi ball da bahon wankansu ya fashe fas,Aunty tace Yar nan lafiya? Siyama ta kankame hannu tace wayyo Yana sona dadi kasheni cikin farin ciki ne, Aunty rungume ni dan Allah Zo ki rungumeni, Aunty taki kulata zuwa tayi ta rike jikin bango tana zan sume Iska zata daukeni wayyo Sanyi dadi Allah na gode maka tayi ihu,Aunty tace wallahi sai kin siyo Mana sabon baho akan Namiji Kika fasa Mana baho,za a siyo karki damu ta fada dakinta harda rawar sanyi tsabar farin ciki sai kace tana Jin sanyi haka take karkarwa. Aisha watanta biyu a gidan Bashir duk ta rame tayi baki ta fita a hayyacinta gashi Hariji sannan Kuma Babu abincin kirki Yana samun kudi amma ya daina bata ci na kirki,a wata biyun ta samu ciki amma shi Bashir baya son haihuwa,ga mijinta can Farooq Yana son haihuwa basu samu ba taje tayi aure Kuma inda ga haihuwar amma ba a son yaran,gaba daya Bashir ya tsaneta sabo da ciki,ko ya ta bashi haushi sai duka a Haka cikin nata ya zube Aisha tayi barin Yan biyu twins,tayi kuka sosai ga rama ta kekashe ta bushe,Farooq Kuwa har wasu lokuta baiyi aure ba ya kasa kula kowa har ya gaji Mamansa ta hada shi Nabeela bazawara ita Kuma Maman Farooq kawar Maman Sabeer ce a can taga Nabeela,Aisha sai labari taji Farooq yayi aure tayi bakin ciki tayi kuka ta gode Allah har ta samu wani cikin,Bashir tsana ta dawo sabuwa dal Nusaiba bayan ta Gama Idda da kwana uku Sufyan yazo gaida Shehu,Shehu ya sauke shi yace yaro daga yin iddarta da kwana uku har yaushe ta sanka da zaka ce zaka turo wannan ya nuna cewar tun tana da aure ka Santa dama kana sonta ko karya ne? Sufyan yayi mukus yace bazai yuwu ace daga Gama Idda da kwana uku Wai har kazo daga wata uwa duniya kana sonta Kai ba dan unguwar nan ba a Ina ka ganta sai dai idan dama tun tana da aure kana zuwa,Mama
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71