Skip to content

Chapter 42

Chapter 42

AURENMU Book One Complete Hausa Novel 1,249 words 0 views Progress saved
Download Book

kuwa tsohuwar unguwarsu yaje unguwar masu kudi ita Siyama tana ta faman kuka a lullubeta cikin Mayafi har age gida bata sani ba sai da yace fito ta dago da kanta Mamaki ya kamata tace me za muyi a wannan gidan ta kalli gidansa ne katafaren gida na da Wanda ta sani Sanda Yana me kudi,Kuma duka ga motocinsa nan har da wasu sababbi ma,masu aikin gidan tsofaffi Wanda ya sallama ta gani ya dawo dasu kenan,ga inda an Kara gyara shi ya koma wani irin mugun hadadden gida har ya da a baya tsaruwa,baki ta bude yace Baby fito Yana Murmushi ya jawo hannunta ta fito tace ba dai duk talaucin da kace ba karya ne? yace ki saurareni Baby kiji ba abinda ya faru da dukiyata tun daga lokacin da nace Nusaiba ta ebi kudi a cikin kudina ta bawa Mamanta ta kwashe kudin duka na Fara zargin sabo da kudina ta aureni badan Allah ba shine nayi Mata haka Kuma ko Mum da Sabeer ban fada musu komai ba tunaninsu da gaske na talauce,Siyama ta Fara mamaki tace yanzu kana nufin duk banki da kace sun kwace komai karya ne? Yace ae,Fuska ta bata tace amma ka dauki hakkinmu hawaye ya zubo mata tace me yasa kayi Mana haka, rudewa yayi ganin ranta a bace,tace ta ya za ayi ace dama Kawai fada kayi ka shirya zance Muka dinga Shan wahala a kanka muna Jin tausayinka hawaye ya zubo Mata,yace please Baby kiyi Hakuri ke kin San dalilin da yasa nayi haka sabo da na San me so na tsakani da Allah kuma gashi na sani ya karasa Kamar zaiyi kuka kiyi hakuri muje ciki ta shiga yasa me aikin ta shigar Mata da kayanta kaf bedroom din Amarya,ya zauna Yana aikin lallabata ya Sha fama kafin ta hakura ta sakko hannunta ya rike kin zauna a Palo Baby muje sama Suka haura sama jikinta a sanyaye tace ya akayi Naga motar da Nusaiba ta siyar maka Wanda tace Wanda ya siya ya gudu bai bata kudin ba? Yace ai Wanda ya siya motar yarona ne tunaninta ban me nake ba ni na tura shi ya siyi motar ya gudu Kuma,Saurayinta data aura ne kadai ban sani ba ban ma taba ganinsa ba amma komai da takeyi Ina sane Suna Shiga bedroom dinsa ya rungumeta a jikinsa yace ko za a hanani yanzu? Murmushi ta saki tace yaci gaba da rungumeta Yana shafa wuyanta,tsigar jikinta ce ta tashi Wanda ya jawo ta lumshe idonta,yace kinyi wanka a gida ko yanzu zamu Yi Yana magana yana goga Mata Hajiya Babba wacce ta mike sosai,tace yanzu nayi wanka yace Nima Haka, toilet dai ta Shiga taci gaba da kukan barin gidansu ta wanke fuskarta ta fito tare da zabo rigar bacci ta gaske ta saka shi yayi shirinsa ma,kayan makulashe Suka lashe sannan Suka Yi brush ta Fitowa ya dauketa sai saman bed ya kwantar da ita a hankali... Nabeela ce ta samu ciki a gidan Farook murna wajen farouk ba a cewa komai,Kamar gaske sabo da bata son Farook taje a boye ta zubar da cikin aka Mata Allura,Bayan ta dawo gida cikin dare ta fara bleeding yayi yayi ta bari a tafi asibiti taki yarda sabo da Kar a ganeta sai da ta kusa mutuwa Farook ya kasa jurewa ya dauke ya dauko Mamansa Suka tafi asibiti,ai Kuwa bayan komai ya lafa likitoci sun samu nasarar ceto ranta, likitan yace Farook ya same shi a Office,bayan Farook ya shiga ya zauna likitan ya dago ya kalli Farook ya Fara fada taya za ayi a Mata allurar zubar da ciki me karfi haka,Farook yace Allura Kuma?likita yace Kai mijinta ne ko kuwa cikin Shege ka Mata sakamako ya nuna Allura ce me karfi ta zubar da ciki,idan matarka ce ka binciketa gaskiya,Farook duk da ransa ya baci amma ya danne bai nuna ba Sam Sai da aka sallamesu bayan kwana biyu taji sauki sosai ta warke ya sameta a bedroom tana zaune,Yace Nabeela wacce Allura Kika yi na zubar da ciki? dama kin San bakya kaunata Kika aureni,kin San wani kike so Kika zalunceni na aureki, Nabeela tace waye ya fada maka? Wayo ya Mata yace Wanda Kika je ya zubar Miki cikin,tunani tayi Kawai da gaske an fada masa tace Ni bana son haihuwar, gau kake ji ya kifa Mata Mari hagu da Dama yace amma ke azzaluma ce Ina son yaran Kika zubar min da ciki, ya zari zai Fara zaneta ta gudu Daya dakin ta saka key tana Cewa Allah ya Isa,idan ya zageta haka ta rama Kawai takarda ya dakko ya saketa Saki daya ya bata takardarta ya sallameta,ita duk Affan take so akansa take kashe aurenta har da murna zata je ta nemi Affan dama taji labarin inda yake Zaune can zata tafi ko Idda baza ta bari tayi ba. Nusaiba Kuwa soyayya suke bugawa da Sufyan abinda take so yake Mata komai ya samo a gindin Nusaiba da uwarta yake karewa,duk ta rabashi da danginsa Wanda da shi Suka dogara shike Basu ci da Sha amma Nusaiba tasa yanzu ok gaida iyayensa sai yaga dama yake zuwa,Basu da cin yau bare na gobe amma yaki ya taimake su,Ummansa ce ta gaji ta shirya ta tafi gidansa,Lokacin ya tafi Office tana zuwa ta shiga palon Wanda ta iske yar aiki tana ta gyare gyare,Yar aiki ta gaisheta Umma ta shiga ta zauna tace me aikin ta Kira Mata Nusaiba,Nusaiba tana sama taci gayu ta kishingida a saman gado tana latsa Wayarta ac na ratsata,Me aikin ce ta shiga da sallama ta durkusa a gaban Nusaiba tace Kinyi bakuwa Hajiya,Nusaiba da aka Kira da Hajiya tana yatsina tace wace? umman Alhaji ce,uwarsa ce Maimuna Wai?Me aiki tayi mamaki uwar miji guda ake Kira da sunanta gatsal haka,me aikin tace ae itace,tsaki Nusaiba ta ja tare da furta je kice Ina zuwa,tunda me aiki tace gata nan Nusaiba tafi hour guda bata fito sannan sai gata tana sakkowa daga bene tikasai tikasai tana taku dai dai tazo ta zauna tare da furta gani naji ance kina nemana,Uwar miji tace dama Sufyan nazo gani ko Yana gida?kin San Yana wajen aiki bai dawowa sai dare in kuma Zaki jirashi to ta mike tana kunkuni tana cewa miji ma sabo da Masifa baza a barka ka zauna lafiya ba uwar mutum tabi ta isheka ta Shige kitchen,tana zuwa kitchen ta samu me aiki tace idan Kika sake Kika Bata ko ruwa sai na koreki yau,Umman Sufyan tana ji a kunnenta mikewa tayi ma kawai ta bar gidan ta koma gida inda ta bawa Baban Sufyan labarin irin wulakancin da aka Mata,Baban Sufyan yace kyale shi ai Allah shike ciyar da mutum Kuma shi ke raya bawa kyale shi zaizo ya same mu watarana tunda shi mace tafi iyayensa. Bangaren ango Kuwa Nafila yayi shi daya da adduoi Siyama tana zaune a gefen bed tayi Shuru tana tunani da farin ciki yau itace a gidan nan tangameme haka,gida na gagara,mijinta hadadde ga kudi duk natane Allah take godiya har ya idar Yana sallamewa ya juyo Yana kallonta cike da farin ciki Yana Murmushi ya mike tare da haurawa saman bed din ya jawota jikinsa AsmaBaffa [4/1, 5:47 AM]

Table of Contents

Chapters

71 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71