Chapter 31
Chapter 31
tana ji tayi gatsal tace yata shi take so kuma shi zata aura,Shehu yace ba matsala Kai Sufyan gaka ga Nusaiba duk abinda tayi maka karka soma kawo min kara ba ruwana ya tashi ya fice abinsa,Nusaiba ce tazo tace karka damu dashi Indai Mama tana sonka an gama,Sufyan Yana murna sosai ya tafi,Bayan kwana uku ya turo da kudin aure cikin sati biyu Mama ta yanke aure za a daura,Shehu ba ruwansa a ciki sai da daurin aure yazo sannan ya shige gaba Sabo da yarsa ce ba yanda zaiyi aka daura auren Sufyan da Nusaiba Nusaiba takanas ta tafi gidan Aslam ta kwankwasa ya zaci wani ne ya bude sai kuwa ta shiga ciki tana yiwa gidan kallon banza harda cewa to Ina Aslam Dan karya gashi na riga ka aure Kuma na sake samun wani me kudin Allah ba Azzalumin bawansa bane bazai barni cikin wahala ba na sake tafiya gida me ac sai naga ta tsiya Kai Kuwa gaka nan tsiya tsiya kalli wannan dirty smelling House din naka nafi karfinka tana Jan tsaki ta juya ta bude kofa ta fice tace aci gaba da Shan talauci lafiya,Aslam baki ya tabe ko a jikinsa yace Wanda ya kulaki shine banza baki da ajin da Zan saurareki,Nusaiba tana jinsa ita Kam tayi gaba abinta. Masu sharhi Ina Matukar godiya AsmaBaffa [4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️ 46-50 Official By AsmaBaffa Page naku ne MRS SAS YAR AUTA Sufyan Isa,Dane ga Isa Yan garin Ajingi ne Kano amma a cikin Kano suke danginsu ne a Kauye amma uwarsa da ubansa da kannensa guda bakwai suna Kano kofar Ruwa,Sufyan shine Babba a gidansu talakawane, Allah yasa Sufyan yayi degree ya samu babban aiki na gomnati yayi aiki da shekara hudu haka Kawai ya ajiye aikinsa ya fito takarar Chairman ya koma siyasa,bayan anyi zabe ya Sha kasa ko kansilan nadi ba a bashi ba,karshe talauci ya sake baibaye su ya Shiga Neman aikin kamfani bai samu ba sai da ya kwashe shekara biyar sannan ya samu aiki a wani kamfanin shahararren me kudi ya bashi C.E.O ga Albashi me tsoka yana aikinsa sosai bai da wani aibu sai dai dan Adam kowa Yana da Hali me kyau Kuma ba a rasashi da hali na banza ko ya yake,ana haka ya ginawa iyayensa gida me kyau shima ya gina nasa gidan me kyau sosai amma bai Kama kafar gidan Aslam da bank Suka kwace ba Babu hadi ma, ya mallaki motarsa me kyau har ya hadu da Nusaiba ya aureta Kuma. Kwana uku da daura aure Nusaiba ta Sha gyara ta ko Ina tayi kyau sai kamshi take yi,ranar Kuma aka Kai amarya gidan mijinta me kyau kana gani kasan ba gidan talaka bane,zaune take a saman gadonta dake dama Kawai daga ita sai lefenta da kayan sawarta Amma komai na furniture ya zuba abinsa. Sari ne a jikinta Riga da skert maroon ta yafa mayafinsa kyau Kam tayi,9pm angon ya shigo da Sallama hannunsa dauke da ledar kaji da kayan makulashe,Zama yayi a gefenta yace Alhmdllh Ni Kam nafi ko wanne Namiji dace a duniya,yau na mallakeki burina ya cika,Nusaiba tayi Murmushi tare da bude mayafin data rufa a kanta,yace tashi kiyi Alwala,mikewa tayi ta sheka wanka da Alwala ta fito shima ya shiga,shiryawa tayi cikin kayan baccinta masu daukan hankali sannan ta daura zani tasa hijab har kasa bayan ya fito shima ya shirya ya sa jallabiyarsa sannan Suka gabatar da duk abinda akeyi na addini da na al'ada,ledar ya jawo ya bude musu kaji ne da su Yogourt da sauran kayan makulashe da fruits Plates ya dakko ya zuba musu ta kalli Naman tace Wai brolas ne ko Maja? Sufyan yace Ina Zan sani ni da na gansu a gashe na siyo,tace maza dai har abada baza kuci gaba ba,tunda aka halicci iyaye da kakanni kowa kaza kaza dai ankonta kuke Yi ko wanne ango ankon kawo kaza,Sufyan Yana Murmushi yace to me kike so? tace Ina laifin ma tattabara tana magana Yana bata naman a baki tana lamushewa amma tana kushewa,sai da suka koshi suka gama komai sannan ya dauketa suka haura saman bed abinka da bazawara tsagera zagewa tayi Suka farantawa juna rai Suka jiyar da juna dadi sosai Sufyan sai yabonta yake yace Yan unguwarku sunyi sakaki na daukeki shike nan,Rungume shi tayi tana I love you a haka har bacci ya kwashe su. Siyama ce ta zubo shinkafa da wake da Mai da yaji sai salat ta toza wani katon plate kamar mutun uku ne zasu ci tasa a gabanta zaune a tsakar gida saman Sallaya da yamma sanye take daga ita sai vest fara da English skert wani me kyau brown Mai adon fulawowi fari,jikin nan nata sumul sumul komai Masha Allah,ta sa Hannu tana ci baza ma tasa cokali ba,Kawu ne yayi sallama ya shigo sai ga Aslam ma a bayansa sun shigo yasha farin wani yadi me kyan gaske yayi kyau Kamar baza a mutu ba,ya shigo Yana takunsa na Izza,Aunty ce ta amsa sallamarsa,Siyama kunya ta kamata sabo da irin abincin data zuba tana ci ya kamata,Aunty ce ta dakko tabarma tare da shimfida Masa ya zauna Suka gaisa Siyama tace Ina yini amsawa yayi Yana murmushi,ta mike ta kawo Masa ruwa pure water Yana faman binta da kallo,Kitchen ta Shiga ta zubo Masa abinci a plate ta rufe ta kawo plate din salat da Maggi star ta ajiye komai sannan ta koma ta zauna a gaban abincinta,sabo da kunya Siyama tace Aunty kin siyo min maganin tsutsar cikin nawa Kuwa? Aunty tace wanne tsutsar ciki sai dai ki boyewa Aslam amma kowa yasan irin mugun cinki,Siyama baki ta turo tace to ba tsutsar ciki ce ba suke tashi suna neman abinci,Indai suka farka daga bacci to sai na Fara Jin yunwa shike nan ba zaman lafiya idan ban ci ba Kuma fa,Aslam Murmushi yayi ya kalleta ya kalli abincin Siyama tana cin abinta,da Ido tace kaci mana,juyawa yayi ya kalli Aunty da Kawu yaga ai hirarsu suke Yi hankalinsu baya wajensa ya kalli Siyama da Ido ya fada Mata bazai ci ba harda makale kafada,Murmushi tayi tana leka su Kawu sabo da Kar su Kama ta,tashi Aunty tayi da Kawu Suka Shige daki suka basu waje,Siyama ce ta leka palon taga sun shige bedroom da sauri ta jawo abincinsa gabanta ta tona gefa tasa salat da su tumatir ta ebo a Spoon ta Mika masa a Baki ya tsaya Yana kallonta bai bude bakin ba,cikin muryar rada tace kayi sauri kafin su fito fa bazan iya baka a gabansu ba,Baki ya dan bude ta zuba Masa Yana ci ta sake lekawa dakin su Kawu taga dai basu da niyyar fitowa taci gaba da bashi a baki yana ci,sai da ya koshi Yana Shirin cewa ya koshi Kawu da Aunty Suka fito ai da sauri Siyama ta tura plate din Gaban Aslam tana basarwa taci gaba da cin abinta,Aunty ta fito sanye da hijab tace Aslam har ka koshi dan Allah ka cinye ta nan fa ba wajen Kara bane,Kawu yace ke Siyama ku tashi ku koma dakin zaure ko yafi sakewa a.....kafin ya karasa Siyama ta mike tsaye ta kwashi abincinsa da ruwa,Shima mikewa yayi ya zaro
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71