Chapter 68
Chapter 68
aikin maza kenan ni kaina yanzu da kyar nake bacci Sabo da ba harka yo na Saba da wanga lamari,dariya sukayi sai tafawa suke suna iya shege wani abin Aunty tana jinsu,Kawu ne ya shigo Suka Yi mukus,ya dauki jariri yace Siyama ashe asibiti aka kaiki? tace wallahi Kuwa kawu na haihu,Kawu yace to rasa kunya ai na gani,Shuru tayi,Makwafta da Yan uwa ana ta zuwa barka,Aslam ya Kira yaji ya matarsa tana dagawa yajita da murna tace Ina gidanmu fa kazo sai ka daukeni mu koma gida,yace lafiya? Kuma shine baki fada min ba ai na gama meeting dinma Ina hanyar gida tace gidanmu zaka taho bani da lafiya,da sauri ya juya Kan motarsa sai gidan su Siyama Yana zuwa yaga Nusaiba ta fito daga gidan ta Shige gidansu wasu matan suna ta shiga wasu na Fitowa harda Maman Nusaiba,Fitowa yayi zai shiga gidan Yar uwar Aunty harda ce Masa an samu karuwa Allah ya raya,Aslam yace ta haihu ne? Au baka sani ba ai tun safe Muka kaita asibiti tana nan lafiya kalau da jariri,Aslam ai ko gama ji baiyi ba ya kutsa Kai cikin gidan,Yana shiga Yan barka duk sun Gama sun fita Kawu ya shigar da shi tsohon dakin Siyama Wanda yanzu ya Sha kujeru da tiles,Zama yayi sannan Aunty taje Suka gaisa,Siyama ta mike da yaronta har da pillow din da take zama a kai,ta Shiga inda Aslam yake,Murmushi ya sakar Mata itama haka jaririn ya karba Yana kallonta yace Kamar bake ba Anya ma kin Sha wahala Kuwa Na ganki Kamar wannan ba daga cikinki ya fito ba,dariya tayi tace Allah ne ya amsa Adduar da kake min kullum Allah ya sauki matarka lafiya to Allah ya amsa Nafeelar da kake yi akan cikin nan Allah ya amsa, yace ah naga zahiri yace baki ji yanda hankali na yake kanki ba akan haihuwar nan sai gashi ko waya sai dawowa nayi Naga jariri,Siyama tace ai kana fita daga gida ko Office baka Kai ba na Fara ciwo Kai nakuda masifa ce na zaci wucewa zanyi har nace da Aunty a Kira min kai,Aslam harda abin tausayi wai Allah sarki Sannu, kai haka ake nakudar dama bazan sake haihuwa da wuri ba,Aslam yayi dariya yace baki Isa Yara nake so,Siyama kamar zata Yi kuka Kamar yace yanzu zai Mata wani cikin tace dan Allah kayi hakuri kayi min rai wallahi nasha wahala daurewa Kawai nayi amma mutuwa ce Kawai banyi ba harda hawaye,Aslam ta bashi dariya yace to Mene na kukan Kuma kin manta da dadin da ake ji kafin ayi cikin,dadin banza mene amfaninsa kaci Dadi ko kaci wahala,dariya ta Kama Aslam,yace kece fa Watarana kike cewa ayi Miki, to yanzu na gane gaskiya bani ba wannan lamari, tace kazanta haihuwa Ina haihuwa sai amai na dinga amai,haba ya ake cewa abarnan mabiya ta taho da komatsai da tarkace tayo shara Suka shirkito kasa daga cikina na zaci kayan cikina ne duka ai sai amai wayyo kazanta daga yau sai na tsinewa me girman Kai ya taho a cikin wannan kazantar za ayiwa mutane iyayi,Aslam ya dinga dariyar labarin Siyama an Haihu harda cewa daina fada min kazantar nan Kar na kasa cin abinci dake,tace dama ni yanzu na Isa na maka girki kaci ai nayi kazanta da yawa bai ma dace ba wlh Me danyen jego da girki haba kana da gaskiya karka kaci abincina Allah wannan kazanta haka. Yaronsa yayiwa Addua a kunne sosai Yana ta kallonsa idonsa tar yace wannan idon naki ne ba nawa bane,Siyama tace kalli da kyau idonka ne gashi nan a soye,Siyama ta Mika Hannaye tace bani shi ya gaji uwarsa yake so,yace eh lallai shike nan daga na dauke shi ko minti Sha biyar baiyi ba Wai na baki danki ya gaji a Ina Kika gane ya gaji,Siyama tace to shikenan rike shi magana ta kare,Aslam wayarsa ya zaro ya Kira Mum ya fada Mata ya hadata da Siyama ta Mata barka Mum ana ta murna anyi jika,Aunty ce ta roki arziki ya bar Siyama tayi sati biyu a gida sai ta koma ba a sonsa ba da kyar dai ya yarda yaje ya kawo Mata kayanta na sawa da Dan yawa sai na jariri da Suka siyo daga kasar waje komai dai ya kawo,ya jibge Mata kayan shayi da su maltina,juice,ruwan roba,sai kullum Kuma Yana Hanya da su Fruits da nama da sauransu. Nusaiba kullum sai tazo ganin jariri safe da Yamma kamar danta,har zuwa take ta goya shi,Yau ma tun rana tazo ta goya jariri tana gidan har Yamma,Siyama tace Nusaiba bari nayi wanka sai na karbe shi ki huta,tace to Aunty tace wanka ma za ai masa shima Siyama ta shiga wanka Aunty tayiwa jariri wanka ta shiryashi a kayansa wasu milk color yaron ya Kara wayo,Nusaiba ta dauke shi tana zaune yana hannunta Aslam yayi sallama tare da shigowa,Aunty ya gaisar Nusaiba ta gaida shi da kyar ma ya dan iya motsa bakinsa ya amsa shima albarkacin Yaronsa ne da kullum take daukanshi iyaye da dansu,Yana dakin da aka bawa Siyama kwance akan katifarta katuwa dakin ya Sha gyara Yana ta kamshi, shigowa tayi daure da zani a kirji tayi wanka,ya kalleta jikinta duk ruwa zanin ma ya jike a jikinta ya manne Mata a jiki surarta ta bayyana sosai,duk inda ta motsa sai ko Ina na jikinta ya motsa,Aslam yasan ba samu zaiyi ba yace Wai ni idan an Haihu kyau akeyi ne? Kinga kyau fa Kika Kara kin ganki Kuwa kullum nazo sai Naga kinfi jiya kyau har bana so na daina kallonki, Murmushi Siyama tayi tana tsaye tana goge kunnenta da cotton,tace ae ance tana sawa har zuwa arba'in wasu haka take sasu kyau in suka Haihu zuwa 40 days zaka ga mutum ya dawo dai dai,yace yanzu naji zance kinje saloon din? tace ae mana naje jiya na kusa da gidan nan gashi nan an gyara gashin sosai yace okay, yace karbo min dana daga hannun waccen sauri nake yi bacci nake so naje gida nayi,tace to saurin mene Kuma kayi baccin a nan Mana Murmushi yayi yace yan barka fa,Siyama tace Kai rabu dasu sai na koma palon Aunty,Yanzu Zaki suna? ta mike tana cewa Kawu yace babu me zuwa ya bata Masa paint din gida,yace yayi daidai ai, fita tayi ta karbo Jaririn a hannun Nusaiba,jaririn ta bata ta wuce gida abinta. Ranar Suna yaro yaci suna Muhammad raguna manyan gaske uku ya yanka Mata,albarkacin Landlady sai ga Raudah tazo barka da cikinta tsoho itama harda cewa Allah ya bamu ita ku Nima aga nawa haka Siyama tace Allah yasa. Satin Siyama uku a wajen Aunty,me aiki ce ke gyara gidan Aslam kafin ta koma ma sai da aka Masa gyara na musamman,Aslam ya canja furniture na gidan,da Kansa ya dakko matarsa da jaririnsa Muhammad,Allah yasa me aikin nasu babbar macece ita taci gaba da kula da Siyama da jaririn nata tana daukan darasi,tun kafin arba'in jini ya dauke taki fadawa Aslam sai tayi Sallah a boye,Aslam ya gaji yace ban yarda dake ba Baby har arba'in ta wuce ace har yanzu bai dauke ba,Siyama tace bai dauke ba harda mazewa,yace wallahi sai na duba na gani da kaina ya jawota tana tirjewa karka gani kazanta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71